Labarai

Har yanzu na kasa gamsuwa cewa mata sun ƙwace harkar rubutu – Mustapha Rijiyar Lemo 

Har yanzu na kasa gamsuwa cewa mata sun ƙwace harkar rubutu – Mustapha Rijiyar Lemo 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  A yayin da ake ganin mata marubuta sun ƙwace harkar rubutun adabi, saboda wasu dalilai masu nasaba da samun isasshen lokaci da kasancewar hatta karatun littafin ma yanzu mata ne suka fi yi. Hakan bai sanyaya gwiwar Mustapha Abbas Rijiyar Lemo ba, matashin marubucin da tauraruwarsa ke haskawa a duniyar adabin Hausa, tsakanin maza marubutan onlayin. Kodayake har yanzu yana ganin bugaggen littafi yana da tasiri a wajen masu karatu, ba lallai sai na waya ba. Ya kasance marubucin zube, marubucin wasan kwaikwayo, kuma gwani a harkar ƙawata gine-gine. Wakilin Blueprint Manhaja, ya tattauna da shi…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da ayyukan titin Sakkwato-Badagry da madatsun ruwa 63

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da gaɓa ta farko ta aikin hanyar Sakkwato-Badagry domin faɗaɗa hanyoyin da zasu sabbaba haɗaka a tsakanin manyan biranen Nijeriya. Ministan yaɗa labarai da haɗin kan ƙasa, Alhaji Mohammed Idris ya faɗi hakan a lokacin ƙaddamar da wani shirin kwana biyu na ma'aikatar da hukumomin da ke ƙarƙashin ta a Abuja. Hanyar zata haɗe jihohi guda tara wanda haka zai sauƙaƙe harkokin sufuri a tsakanin su. Baya ga haka, gwamnatin ta ce ta bayar da damar gina madatsun ruwa guda 63 waɗanda zasu taimaka wajen inganta harkokin wutar lantarki da noma a…
Read More

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji a hanyar Gusau-Funtua

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƴan bindiga a wani karon sun sake tare hanyar Gusau-Funtua tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama a motoci uku a kusa da ƙauyen Margazu a ƙaramar hukumar Tsafe da ke jihar Zamfara. Hallau, ƴan bindigar sun tare hanyar a mabanbanta wurare ciki har da unguwan Chida da makusanta garuruwa inda suka tare motoci biyar da yin garkuwa da fasinjoji. Mazauna yankunan sun ce wasu ƴan bindigar cikin waɗanda aka kashe sun jima su na addabar yankin ta hanyar amfani da lokacin damina wajen kai hare-hare. Wani daga cikin su ya ce, su kan kawo…
Read More
Ƙaruwar cutar ƙyandar biri ya haifar da agajin gaggawa a Afrika da fargabar yaɗuwa

Ƙaruwar cutar ƙyandar biri ya haifar da agajin gaggawa a Afrika da fargabar yaɗuwa

Hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa na Afirka sun bayyana annobar ƙyandar biri da ake fama da shi a Afirka ta tsakiya a mastayin abun fargaba. Hakan na faruwa ne bayan samun wani sabon nau'in ƙwayar cutar wanda ya ke da saurin yaɗuwa. Domin haka ne hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Afirka ta bayar da sanarwa cewa lamarin ya zama annoba mai ɓukatar agajin gaggawa yayin da hukumar lafiya ta duniya ita ma a na sa ran za ta fitar da irin wannan sanarwar ranar 14 ga Agusta. Masana na nuna damuwa kan yadda…
Read More

Buhari, Jonathan da Majalisar Ƙasa sun yi mubayi’a ga Tinubu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Majalisar Ƙasa, NCS ta yi mubayi'a ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu inda ta ce ta na mai tabbatar da goyon bayanta ga shugabancinsa da kuma ƙoƙarinsa wajen daidaita ƙalubalen da ke fuskantar Nijeriya. Majalisar wacce ta ƙunshi tsoffin shugabannin ƙasa da wasu manyan ƙasa, ta yaba wa hoɓɓasa da gwamnatin Tinubu ke yi na samar da hanyoyin rage raɗaɗi wa al'umma acikin matsanancin yanayi da ake ciki a faɗin ƙasar. An gudanar da zaman ne a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja wanda kuma shi ne na farko tunda shugaba Tinubu ya karɓi karagar mulki.…
Read More
Tinubu ya amince da ƙarin albashin ma’aikatan shari’a da kaso 300%

Tinubu ya amince da ƙarin albashin ma’aikatan shari’a da kaso 300%

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince ya sanya hannu a kan dokar da zata ƙara wa ma'aikatan shari'a albashi da kusan kaso 300%. Wannan sanarwar ta fito daga bakin Sanata Lado, wanda shine mai ba shugaban ƙasa shawara a kan harkokin majalisa. Idan ba mu manta ba, a watan Yuni, shugaban ƙasa ya aikewa majalisa kundin dokar kan batun ƙarin albashin ga ma'aikatan shari'a a faɗin tarayya da jihohi. A cikin watan majalisar da zartar da doka kuma ta aikewa shugaban domin sanya hannu. Lado ya bayyana cewa, yin haka yana nuni da irin jajircewar da Shugaban ƙasa ya…
Read More

An buƙaci Gwamnan Katsina ya dakatar da shirinsa na rushe kasuwar Funtua

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina. Ƴan kasuwan da ke babbar kasuwar garin Funtua, sun yi kira ga gwamnan jihar Katsina, Mallam Dikko Raɗɗa da ya dakatar da shirinsa na rushe kasuwar. Sakataren yaɗa labarai na kungiyar ƴan hatsi a kasuwar, Shehu Ɗahiru Mai-Wada ya yi wannan kira a garin Funtua inda ya ce wannan mataki na gwamnan zai jefa da dama daga cikin ƴan kasuwa cikin halin ƙunci. Ya kara da cewa, mafi yawancin ƴan kasuwan zasu rasa matsugunin wajen da zasu rinƙa harkokin kasuwancinsu. Mai-Wada ya ƙara da cewa, tun da aka ɗauki tsawon lokaci ana kulle a lokacin…
Read More

Kotu ta ƙara wa’adin keɓance zanga-zanga a filin MKO Abiola na Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Alƙali Sylvanus Oriji na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya ƙara wa'adin umarnin dakatar da taron masu zanga-zanga a filin wasa na MKO Abiola wanda aka fi sani da 'National Stadium'. Mai shari'ar ya bayar da umarnin ne sakamakon shigar ƙara da babban lauya, Dakta Ogwu Onoja (SAN) ya yi a madadin Ministan Abuja, Nyesom Wike. A lokacin yin hukunci game da ƙarar, babu ɗaya daga cikin mutane 12 da aka shigar da sunayen su akan ƙarar da ya bayyana kuma babu halstaccen wakilci daga gare su. Waɗanda aka zayyano su acikin takardar ƙarar sune;…
Read More
Ƴan sanda sun tura waɗanda ake zargi da ɗaga tutar Rasha Abuja

Ƴan sanda sun tura waɗanda ake zargi da ɗaga tutar Rasha Abuja

Rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta sanar a ranar Litinin cewa ta miƙa mutane 76 da aka kama suna ɗauke da tutocin Rasha ciki har da wani da ba ɗan ƙasar ba, zuwa hedkwatarsu da ke Abuja domin gudanar da bincike mai zurfi kan zarginsu da laifin tayar da tarzoma. Kwamishinan 'yan sandan Jihar Kano, Salman Garba, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake bayar da bayanai kan mutanen da aka kama a lokacin zanga-zangar yunwa a faɗin ƙasar wadda ta rikiɗe zuwa tashin hankali a yankin Arewa. Ya bayyana cewa bisa ga umarnin Sufeto Janar na…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya tafi Equatorial Guinea kan ziyarar kwana uku

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Laraba ne shugaba Bola Ahmed Tinubu zai fara ziyarar musamman ta tsawon kwanaki uku a ƙasar Equatorial Guinea. Mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce Tinubu zai bar Abuja ne a ranar Talata zuwa Malabo, babban birnin ƙasar inda zai gana da shugaban ƙasar, Nguema Mbasogo a Fadar shugaban ƙasa da ke birnin. A lokacin ziyarar, Tinubu zai tattauna da takwaran nasa kan inganta ababen da ƙasashen biyu suka haɗu a kai ciki har da matsalolin tsaro, mai da kuma gas. Ƴan rakiyar shugaba…
Read More