15
Aug
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Bankin 'Guarantee Trust' da aka fi sani da GTBank ya tabbatar da cewa an samu kai hari ta adireshinsa na sadarwa a ranar Laraba. Sakamakon haka ne jami'an gudanarwa na bankin su ka kasance a ankare inda harin bai yi nasara ba kamar yadda bankin ya tabbatar wa abokan hulɗa da kuma al'umma. Wata sanarwa da bankin ya fitar a ranar Alhamis, ta ce babu ko ɗaya daga cikin tashoshin sadarwar bankin da aka kutsa wa yayin da ofishin gudanarwarsu ya daƙile harin inda ba a samu buɗewar bayanai na ko da ɗaya ne daga cikin…
