Labarai

Matar Gwamnan Kebbi za ta buɗe cibiyar sulhun aure 

Matar Gwamnan Kebbi za ta buɗe cibiyar sulhun aure 

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi Uwargidan Gwamnan Jihar Kebbi Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris ta bayyana ƙudurinta na buɗe wata cibiya don sulhun ma'aurata a maimakon zuwa kotu kaitsaye. Ta yi wannan bayani ne a wani taron da ƙungiya mai kula da sha'anin aure da ladubbansa, mai suna Aure Bautar Allah Women Multipurpose Cooperatiɓe Association Kebbi State. Hajiya Zainab Nasare ta ce ba kowace matsala ce ya kamata a ce an je kotu kaitsaye ba ko a cikin gida ko unguwa ana ana iya sulhu. Zuwa kotu tsakanin ma'aurata ba ƙaramar illa ya ke da ita ba musamman idan…
Read More
Sashen sadarwa na Nijeriya yana cikin tasku, inji Shugaban MTN

Sashen sadarwa na Nijeriya yana cikin tasku, inji Shugaban MTN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Karl Toriola, Shugaban Kamfanin Sadarwa na MTN a Nijeriya, ya yi gargaɗin sosai game da mummunan halin da ɓangaren sadarwar Nijeriya ke ciki, yana mai bayyana shi a matsayin "tasku". Ya bayyna haka ne yayin wani jawabi da ya gabatar a wani taron zuba jari na kamfanonin sadarwa na zamani wanda Kamfanin Financial Deriɓatiɓes Company (FDC) ya shirya a ranar Talata a Legas. Toriola ya jaddada buƙatar gaggawa na shiga tsakani don hana sashin rugujewa, yana mai nuni da cewa idan ba a ɗauki matakin gaggawa ba, masana'antar za ta iya fuskantar ƙalubale masu tsanani da…
Read More

Har yanzu a gidan haya na ke zama – Shekarau

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce har yanzu a gidan haya ya ke zama a Abuja wanda nda ya samu haka ne a sanadiyyar tasirin horo daga ƙungiyar ɗalibai musulmai ta Nijeriya, MSSN. Shekarau, wanda tsohon ministan ilimi ne, ya ce bai taɓa tattauna batun samun wani kaso da kowane ɗan kwangila ba a lokacin da ya ke gwamna. A lokacin da ya ke magana game da batun mutuntaka a taron manema labarai gabannin bikin cikar shekara 70 na MSSN da za a fara a ranar 12 ga watan Oktoba, 2024, Shekarau ya…
Read More

Gwamnan Zamfara ya ce makarantun kwaleji na taka muhimmiyar rawa ga ƙoƙarin gwamnatinsa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana makarantar kwalejin tarayya reshen ilimin fasahar koyarwa (FCET) a matsayin zaure da ke samar da ƙwararrun malamai a makarantu a faɗin jihar. A ranar Laraba ne shugabannin majalisar FCET suka kai ziyara wa gwamnan a Fadar gwamnatin jihar da ke Gusau. Wata sanarwa daga mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ta ce ziyarar wani nau'i ne da ke nuna kusanci tsakanin gwamnatin da kuma majalisar tare da ƙarfafa alaƙa a tsakanin su. A lokacin da ya ke magana, gwamna Lawal ya marabci mambobin majalisar tare da nuna…
Read More
‘Yan gida ɗaya sun mutu sakamakon cin guba a Sakkwato

‘Yan gida ɗaya sun mutu sakamakon cin guba a Sakkwato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani iftila'i ya afku a ƙauyen Runjin Barmo da ke gundumar Kajiji a ƙaramar Hukumar Shagari a Jihar Sakkwato, yayin da wasu mutum bakwai 'yan gida ɗaya suka mutu bayan sun ci wani gurɓataccen abinci na rogo. An tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da Nura Bello, jami’in yaɗa labarai na ma’aikatar lafiya ta jihar Sokoto, ya fitar a madadin kwamishinar lafiya ta jihar, Hajiya Asabe Balarabe, a yammacin Lahadi. A cewar sanarwar, hakimin ƙauyen, Malam Muhammadu Modi, ya bayyana wa kwamishinan abubuwan da suka faru a lokacin da ta jagoranci wata tawaga zuwa…
Read More

Shettima ya nemi a daina kanbama gidan Tinubu, ya ce nasa na Maiduguri ya fi shi ƙawa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ɓukaci ƴan Nijeriya su daina kanbama gidan shugaba Bola Ahmed Tinubu na jihar Legas inda ya ce nasa da ke Maiduguri a jihar Borno ya fi wannan ƙawatuwa. Shettima ya faɗi haka ne a lokacin taron ƙaddamar da wani littafi mai suna 'Navigating the Politics of Universal Education Policies in Nigeria' da Farfesa Modupe Adelabu daga Jami'ar Obafemi Awolowo ya wallafa, wanda aka gudanar a Abuja. Ya kuma tabbatar wa al'umma cewa, nan ba da jimawa ba za su fara ganin amfanin matakan da gwamnatin tarayya ke ɗauka wajen daidaita…
Read More
Yadda matasa suka binne ɗan uwansu da rai a Zariya

Yadda matasa suka binne ɗan uwansu da rai a Zariya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A wani lamari mai ban tsoro da ya faru a garin Zariya na Jihar Kaduna, wasu matasa biyu ’yan uwan juna sun binne ɗan uwansu mai suna Abubakar ɗan shekara 16 da rai sakamakon zarginsa da satar waya. Batun da ya yaɗu a kafafen sada zumunta na yanar gizo da kuma tofin Allah-tsine, ya sa hukumomin jihar suka ɗauki matakin gaggawa, wanda ya sa aka kama matasan. Hajiya Rabi Salisu, Kwamishiniyar Ayyukan Jinƙai da Cigaban Jama’a ta Jihar Kaduna, ta bayyana baƙin cikinta kan lamarin. “Ban taɓa ganin an binne wani da rai ba ko a…
Read More
Atiku ga Akpabio: Ina fatan ba za ku dakatar da Sanata Sumaila ba

Atiku ga Akpabio: Ina fatan ba za ku dakatar da Sanata Sumaila ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Ahugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya mayar da martani kan tonon sililin da Sanata Abdurrahman Sumaila Kawu ya yi game da adadin kuɗaɗen da sanatoci ke karɓa a matsayin alawus-alawus ɗinsu na wata-wata. Rahotanni sun ce Sanata Sumaila ya ce, sanatoci na karɓar alawus-alawus na Naira miliyan 21 duk wata baya ga albashin Naira miliyan ɗaya na wata. Atiku a cikin wata sanarwa a ranar Laraba ya bayyana iƙirarin Kawu a matsayin jajircewa. Ya kuma bayyana fatan cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ba zai dakatar da Kawu kamar Ningi da Ndume…
Read More
An ƙayyade kuɗin fom ɗin tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin Kano

An ƙayyade kuɗin fom ɗin tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) ta ƙayyade kuɗin sayen fom ɗin tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a gudanar a bana. Shugaban hukumar zaɓen, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya sanar da hakan ne a yayin bayyana jadawali da ƙa’idojin shiga zaɓen a wani taron manema labarai da hukumar ta gudanar a Kano a ranar Alhamis. A yayin taron, hukumar zaɓen ta sanar da cewa duk mai son tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukuma a zaɓen to zai sayi fom a kan naira miliyan 10. Yayin da ɗan takarar…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamnatin Tarayya za ta daƙile yunƙurin wasu ƴan China masu ƙoƙarin damfarar ƙasar

Daga NASIR S. GWANGWAZO Fadar shugaban ƙasa ta bankaɗo wani yunƙuri na danne kadarorin Najeriya da kamfanin ƙasar China mai suna Zhongshan Fucheng Industrial Investment Co. Limited ya yi a gaɓar tekun Najeriya ta hanyar zamba cikin a aminci. Kamfanin dai ya so yin amfani da wani hukunci mai cike da ruɗani da wata kotun birnin Paris ta zartas kan jiragen shugaban ƙasar ne da ake kula da su a Faransa inda ya so ƙwace wa Najeriya jiragen nata. Gwamnatin, ta kuma nisanta kanta da yin duk wata hulɗa da kamfanin na Zhongshan, inda ta ce za ta yi aiki…
Read More