Labarai

‘Yan sanda sun ce ba sakatariyar NLC suka yi nufin kai farmaki ba

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar 'Yan sanda ta ce jami'anta sun gudanar da atsayen ne a gidan ƙwadago (Labour House). Wata sanarwa da hedkwatar Ƴan sandan ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, ACP Olumuyiwa Adejobi ta ce "Ba sakatariyar NLC ba ne aka nufi kai farmakin". Rundunar ta ce an shirya atsayen ne kaɗai domin kama wanda ake zargi - wani ɗan ƙasar waje da aka jingina wa laifukan fashi da makami a Nijeriya da ma wasu ƙasashen Afirka. Rahotanni sun bayyana cewa ƙungiyar ƙwadago (NLC) ta ɗaga murya kan farmaki da jami'an tsaro suka kai sakatariyarta, ta…
Read More

Shugaban tsaro na ECOWAS ya buƙaci dawo da Mali, Nijar da Burkina Faso cikin ƙungiyar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Juma'a ne shugabannin tsaro na ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS suka yi kira ga dawo da ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar cikin ƙungiyar. A lokacin da ya ke jawabi yayin ziyartar cibiyar kula da lamuran ta'addanci ta Ƙasa, shugaban kwamitin shugabannin tsaro na ECOWAS, Janar Christopher Musa, ya ce dawowar ƙasashen na da muhimmanci wajen tunkarar matsalolin tsaro musamman ɓangaren ƴan tada ƙayar baya. Ya ce, su na cigaba da ƙoƙari wajen tabbatar da ƙasashen sun dawo, ya na mai jaddada muhimmancin gudunmawarsu ga magance matsalolin tsaro a yammacin…
Read More
An fara zanga-zangar mutum miliyan ɗaya a Abuja

An fara zanga-zangar mutum miliyan ɗaya a Abuja

Masu zanga-zangar yunwa da matsin rayuwa sun fara taruwa a babban birnin tarayya Abuja domin gudanar da zanga-zangar mutum miliyan ɗaya. An hangi masu zanga-zangar ɗauke da kwalaye a rana ta goma na zanga-zangar matsin rayuwan da aka fara run ɗaya ga watan Agusta 2024. Wakilin Manhaja ya gano cewa, an sami ƙarin jami'an tsaro a tituna na Abuja da filin taro na Eagle Square.
Read More

Abinci: Shettima ya nemi ƙarin tallafi ga ƴan ƙasa yayin da MTN ta bada agaji

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mai Girma Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jinjina wa kamfanin MTN kan bayar da tallafin Naira biliyan ɗaya da kuma kayan fasahar zamani guda 4,600 domin a raba wa makarantu. Shettima ya faɗi hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya karɓi baƙoncin shugaban MTN, Ernest Ndukwe a Fadar shugaban ƙasa. Ya ce, yunƙurin da MTN ɗin ya yi na tallafa wa ƙoƙarin gwamnati wajen magance matsalar tsadar rayuwa abin a yi kwaikwayo ne, domin hakan na nuna ƙoƙarinsa ta fuskar bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya. Ya kuma ce, ma'aikatar masana'antu da zuba hannun jari tare…
Read More
‘Yan sanda a Katsina sun kama mutane 64, sun kuma ƙwato kayan da ɓata-gari suka wawashe 

‘Yan sanda a Katsina sun kama mutane 64, sun kuma ƙwato kayan da ɓata-gari suka wawashe 

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar 'yan sanda a jihar Katsina ta bayyana cewa ta kama matasa 64 da suka sace kayan jama'a da na gwamnati, ciki haɗa buhunan takin zamani 693 bayan da ɓatagarin suka ɓalle ma'ajiyar gwamnati, a yayin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin tsaro da ta rikiɗe zuwa tarzoma a jihar. Kakakin rundunar ASP Abubakar Sadiƙ Aliyu ne ya bayyana wa manema labarai hakan a birnin Katsina. Tun da farko rundunar ta fitar da wata sanarwa inda ta yi kira ga iyaye akan su kula da 'ya'yansu tare da jan kunnensu akan su guji shiga…
Read More

Bayan sanar da raba kuɗi, ƴan TikTok sun bada lambobin bankunansu ga ƴan ta’adda kan yabon Bello Turji

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wani abin mamaki ya karaɗe shafukan sadarwa bayan da ƴan Nijeriya suka fara tura wa ƴan bindiga lambobin bankunansu sakamakon yabon shahararren ɗan ta'addan nan mai Bello Turji yayin zanga-zangar da ke gudana a Nijeriya. A ranar 1 ga watan Agusta ne aka fara zanga-zangar wanda daga baya ta sauya salo a wasu yankunan inda aka yi ta satar dukiyar al'umma da ta gwamnati. Yayin da zanga-zangar ke raguwa a faɗin ƙasar ne, ƴan bindiga suka sanar da batun raba kuɗaɗe don nuna godiyarsu na yabon shugabansu da wasu ƴan 'TikTok' ke yi inda suka kira…
Read More
Ba mu da hannu ko alaƙa da masu filfila tutar Rasha a zanga-zangar Nijeriya – Jakadan Rasha

Ba mu da hannu ko alaƙa da masu filfila tutar Rasha a zanga-zangar Nijeriya – Jakadan Rasha

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ofishin Jakadancin Rasha na Nijeriya ya nesanta ƙasar sa daga hannu ko alaƙa ta kusa ko ta nesa da waɗanda suka riƙa filfila tutar ƙasar a lokacin zanga-zanga a faɗin Nijeriya. A zanga-zangar ta ranar Litinin, an riƙa filfila tutar Rasha a wasu garuruwan Arewa, yayin da ake ta kiraye kirayen a cire Shugaban ƙasa Bola Tinubu daga kan mulkin Nijeriya. Gwamnatin Nijeriya dai ta ce ba za ta lamunci kiraye-kirayen sojoji su ƙwace mulki ba, kuma duk wanda ya filfila tutar wata ƙasa to ya aikata laifin cin amanar ƙasa. Haka dai Babban…
Read More
Yadda wasu mutum huɗu suka mutu bayan cin amala a Kwara

Yadda wasu mutum huɗu suka mutu bayan cin amala a Kwara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani abin takaici ya faru yayin da wata tsohuwa mai shekaru 70 da ɗanta da wasu ‘yan uwa biyu suka mutu a unguwar Eruda da ke Ilorin a ƙaramar hukumar Ilorin ta yamma bayan sun ci amala da aka ce an sa musu guba. Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dakta Amina El-Imam, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce gwamnati ta sanya tsarin kula da lafiya a kan hanyar magance ɓarkewar cutar. Ta kuma bayyana cewa an samu rahoton mutuwar mutum ɗaya daga cin guba. A cewarta, ɗaukacin tawagar ma’aikatar lafiya ta ma’aikatar sun…
Read More
Mace ta farko Shugabar SUG a Jami’ar Kalaba ta naɗa mataimaka 50

Mace ta farko Shugabar SUG a Jami’ar Kalaba ta naɗa mataimaka 50

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An zaɓi Alims ne a ranar 14 ga Yuni, 2024, a matsayin mace ta farko Shugabar SUG a Jami'ar Kalaba. Alims a halin yanzu tana Nazarin Zaman Lafiya da warware rikice-rikice a Sashen Kimiyyar Siyasa tare da CGPA  4.75 a halin yanzu. Ta fito daga Gakem, a ƙaramar hukumar Bekwarra, jihar Kuros Riba.. A cikin 2022, Blessing Alims ta kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka yi nasara a cikin sama da 'yan takara 150 da aka zana daga ko'ina cikin Afirka don shiga cikin Shirin Matasa na Gidauniyar Mata da ƙarin Tasirin zamantakewa. Ita…
Read More
‘Yan sanda sun zafafa sintiri gabanin zanga-zangar mutum miliya ɗaya a manyan birane

‘Yan sanda sun zafafa sintiri gabanin zanga-zangar mutum miliya ɗaya a manyan birane

Ɗaruruwan ƴan sanda ne ke sintiri a manyan birane da ke Nijeriya sabida zanga-zangar mutum miliyan ɗaya da ake sa rai za a gudanar a yau Asabar. Zanga-zangar yunwar da matsin rayuwa a na sa ran za ta ƙare yau. Masu zanga-zangar na neman gwamnati ta dawo da tallafin mai, ƙara mafi ƙarancin albashi da kuma sauran batutuwa domin kawo sauƙi da ɗan Nijeriya. Duk da dai zanga-zanga ta rage ƙarfi a jihohi da dama, garuruwa irin su Kano,Kaduna,Ribas da Bauchi har yanzu ana gudanar da ita. Kodinetan 'Take It Back Movement ' Sanyaolu Juwon ya ce su na nan…
Read More