Labarai

Akasarin masu riƙe da muƙamai ya kamata a kai su kurkuku – Obasanjo

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo ya ce mafi yawancin jagororin Nijeriya kamata a ce an an garƙame ko rataye su a madadin raba mu su muƙamai. Obasanjo ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da ƴan majalisar wakilai shida da ke jagorantar ƙudirin neman shekara shida ga kowane wa'adi. Ya ce, a yayin zaɓar shugabanni na gari sai an yi la'akari da halayyarsu, ya na mai cewa Nijeriya ta na tsaka mai wuya da sai ta ɗauki matakan da su ka dace wajen ƙalubale da yawa da ke fuskantar ta. Tsohon shugaban ƙasar…
Read More

Ba zan sake tsayawa takara ba, shekaruna sun ja – Shugaban kwamitin Olympics

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban kwamitin Olympics na ƙasa-da-ƙasa (OIC), Thomas Bach ya ce zai sauka daga muƙaminsa yayin da wa'adinsa na biyu ya ƙare a shekarar 2025. Bach wanda ɗan ƙasar Jamus ne ya faɗi hakan ne kwana ɗaya kafin ƙarƙare gasar Olympics da ke gudana a Farisa babban bankin ƙasar Faransa a wani zama na kwamitin. Ya ce akwai buƙatar a samu sauyi a shugabancin kwamitin tare da bayar da haƙuri ga waɗanda ba su ji daɗin hukuncin nasa ba musanman cikin mambobin kwamitin da suka ɓukaci ya tsawaita zamansa a kujerar. Bach wanda ya taɓa zama zakara…
Read More
Gwamna Abba ya jaddada aniyarsa ta yaƙar cin hanci a Jihar Kano

Gwamna Abba ya jaddada aniyarsa ta yaƙar cin hanci a Jihar Kano

Gwamnan Kano, Abba kabir Kabir Yusuf ya jaddada aniyarsa ta yaƙar cin hanci a faɗin Jihar Kano. Gwamnan ya bayyana haka ne a taron ƙarawa juna sani a kan cin hancin da aka yi a Dawakin Kudu ga dukkan Daraktocin jihar. Gwamnan, wanda mataimakin shi, Com Aminu Abdulsalam Gwarzo ya wakilta ya jaddada cewa gwamnatin su ta nan tana kawo tsare-tsare da shirye-shirye da za su ci da jihar gaba. Ya cigaba da cewa, waɗannan tsare-tsare da ake yi, zasu kawo cigaba mai ɗorewa a faɗin jihar Kano musamman ganin jami'iyyar su ta NNPP ba za ta lamunci wani nau'in…
Read More

Poland ta musanta batun ɗaga tutar Rasha ga ƴaƴanta da DSS ta kama a Kano

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙasar Poland da ke Nahiyar Turai ta musanta batun cewa ƴaƴanta da jami'an hukuma suka kama a Kano an same su da laifin ɗaga tutar ƙasar Rasha. A ranar 6 ga watan Agusta ne aka kama ƴan ƙasar kan zargin ɗaga tutar Rasha a Kano a lokacin zanga-zangar tsadar rayuwa da ƴan Nijeriya suka gabatar. Sannan, an kama wasu mutum shida ƴan ƙasar Sifaniya. A wani zama na ƴan difulomasiyya a Abuja, mai magana da yawun hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS), Peter Afunaya ya ce, an kama ƴan Poland ɗin ne a lokacin zanga-zangar da…
Read More

Shugabar ma’aikata mai barin gado ta gabatar da magajiyarta ga Shugaba Tinubu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Juma'a ne shugabar ma'aikatar ma'aikatu, Misis Folashade Esan ta gabatar da wacce za ta gaje ta a kujerarta, Misis Esther Wilson-Jack ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Esan ta ce Shugaba Tinubu ya yi sauyin yadda ya dace ganin yadda Wilson-Jack ta zauna da ita na tsawon makonni domin ɗaukar hannu daga gare ta, ta na mai bayar da tabbacin Esther za ta iya riƙe muƙamin yadda ake buƙata. Ta kuma ce, sabuwar shugabar ta kasance mai ƙwazo, zaƙaƙura da kuma ƙwarewa ta salo daban-daban na gudanarwa. Kazalika,…
Read More

APC ta nemi a binciki jami’an gwamnatin Kano kan zargin karkatar da shinkafar tallafi ta Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Jam'iyyar APC a jihar Kano ta nemi a gudanar da bincike kan zargin sauya akalar shinkafar da Gwamnatin Tarayya ta bai wa gwamnatin jihar a matsayin tallafi ga al'umma. Shugaban Ma'aikata na gwamnan jihar, Shehu Sagagi ne ake zargi da karkatar da shinkafar. Sai dai, Sagagi ya musanta zargin, ya na mai cewa shinkafar da aka samu a makarantar Islamiyyarsa shi ya saya da kuɗinsa yayin da wasu mutane suka bayar da taimakon wani ɓangare na shinkafar don ciyar da ɗalibai. Amma shugaban APC na jihar Kano, Alhaji Abdullahi Abbas ya ce jam'iyyar ta damu da…
Read More
Ba mu karɓi shinkafar gwamnatin ba – Ƙungiyar Izalar Katsina

Ba mu karɓi shinkafar gwamnatin ba – Ƙungiyar Izalar Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban ƙungiyar Izala ta ƙasa reshen Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa ya musanya raɗe-raɗin da ake cewa Gwamnatin Tarayya ta ba ƙungiyar shinkafa buhu 6000. A hira da ya yi da manema labarai a gidansa da ke Katsina Sheikh Yakubu Musa ya ce a saninsa Majalisar ƙoli na tabbatar da shari'a aka wannan shinkafa ta raba. Ya cigaba da cewa, Majalisar sai ta kafa kwamitin mutum uku da ba su alhakin raba ganin ƙungiyoyi irin na ita izala da ɗariƙa da sauransu suna ƙaraashin ita majalisar ce. Sheikh Yakubu Musa ya ƙara da cewa, kamar…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta tuhumi ɗan kwangilar da ya yi aikin titin Kano-Maiduguri lokacin Buhari

Gwamnatin Tarayya ta tuhumi ɗan kwangilar da ya yi aikin titin Kano-Maiduguri lokacin Buhari

Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta hannun Ministan Ayyuka, David Umahi, ta miƙa tuhuma ga ɗan kwangilar da ya yi aikin titin Maiduguri-Kano a lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, titin da ya lalace sakamakon ambaliyar ruwa a kwanan nan. Titin ya kasance sashe na uku na sabon titin Kano-Maiduguri da aka gyara ba da jimawa ba. A cikin wata sanarwa daga mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Orji Uchenna Orji, Umahi ya bayyana cewa, abin takaici ne ganin yadda hanyoyin da aka kammala a ƙasar ba su kai wa tsawon shekara biyar. Umahi…
Read More

Trump ya sake tsallake rijiya da baya yayin da jirginsa ya samu tangarɗa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI An tilasta wa jirgin tsohon shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump sauka a yankin Billings da ke jihar Montana bayan da ya samu tseko akan hanyarsa ta zuwa Bozeman. Jami'an filin jiragen sama suka shaidawa tashar CBS aukuwar lamarin a ranar Juma'a. Trump zai ƙaddamar da wani gangamin siyasa ne a Bozeman da ke jihar wanda hakan bai yiwuwa ba saboda tasgaro da aka samu wanda ya sanya ya sauka a Billings mai nisan mil 150 tsakanin sa da asalin inda aka shirya taron. Baya ga haka ne, Trump ya tafi Bozeman a wani jirginsa mai tashin…
Read More

Yadda dandazon masu zanga-zanga ya banƙara shirin ƴan sanda a rana ta 10 a Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da aka kai rana ta ƙarshe a kwanaki 10 na zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya, dandazon mutane sun hallara acikin sahun da aka yi wa laƙabi da 'one-millon-man-march' a yankunan Apo da Lokogoma da ke Abuja. Masu zanga-zangar sun sauya wajen gangamin ne daga filin MKO Abiola da Eagles square da aka jibge jami'an tsaro zuwa zuwa Apo da Lokogoma inda su ka taru tun ƙarfe 7 na safe. A yayin haka ne suka yi ta ɗaga takardun saƙonni tare da rera waƙoƙin "a kawo ƙarshen yunwa" da kuma "dawo da tallafin man fetur", su…
Read More