10
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Borno ta jaddada ƙudirinta na magance kwararowar yaran da ba su da 'yan rakiya a jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai da Tsaro na Cikin Gida, Farfesa Usman Tar, ya bayyana haka bayan taron Majalisar Tsaron Jihar a ranar Litinin. Babagana Umara Zulum, gwamnan jihar Borno ne ya jagoranci taron wanda ya gudana a zauren majalisar na gidan gwamnati. Kwamishinan ya ce, “Majalisar ta yi taro a yau Litinin 5 ga watan Agusta, 2024, domin duba halin tsaro a jihar. Bayan yin nazari sosai kan duk abin da ya faru daga ranar 1 zuwa…
