Labarai

Zaɓen Amurka: An sanya ranar muhawara tsakanin Trump da Harris

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da zaɓen shugaban ƙasar Amurka ke cigaba da ƙaratowa, an sanar da sanya lokacin tafka muhawara na farko tsakanin Donald Trump da takwararsa Kamala Harris. Tashar ABC ta ruwaito cewa cewa za ta haska muhawarar wacce za ayi tsakanin ƴan takaran biyu a ranar 10 ga watan Satumba kamar yadda ta wallafa a shafinta na X. Hakan na zuwa ne bayan da Trump ya yi wasu kalumai a ranar Alhamis inda ya ce a shirye ya ke ya fafata da abokiyar karawar tasa a lokuta da dama kafin lokacin zaɓen wanda za a yi acikin…
Read More

HOTUNA: Sarkin Kano Sanusi ya ziyarci cibiyar sadarwa da masu zanga-zanga suka ɓata a Kano

Daga NASIR S. GWANGWAZO Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yi ziyarar gani da ido cibiyar sadarwa ta zamani da Gwamnatin Tarayya ta gina a Kano ƙarƙashin Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC), wacce wasu masu zanga-zanga suka ɓarnata ta. A ranar 7 ga Agusta, 2024, ne Mai Martaba Sarkin ya kai ziyara cibiyar ta 'Nigerian Communication Commission Digital Indstrial Park', wacce Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gina da nufin bunƙasa harkokin sadarwa ta zamani, wacce aka tsara dubunnan matasa a Kano da maƙotan jihohi za su samu aikin yi a ƙarƙashin shirin. Sarki Sanusi ya jajenta…
Read More
Ambaliya ta yi awon gaba da titin Kano zuwa Maiduguri

Ambaliya ta yi awon gaba da titin Kano zuwa Maiduguri

Wani mamakon ruwan sama da aka yi, yayi awom gaba da titin Maiduguri zuwa Kano tsakanin ƙauyen Malori da Guskuri a ƙaramar hukumar Katagum a Jihar Bauchi. Ruwan ya haddasa dole masu bin hanyar neman mafita dalilin wannan hanyar ba zata biyu ba yanzu. A wata ziyarar gani da ido da gwamnan ya kai wurin, gwamnan ya jaddada irin muhimmancin da titin yake dashi musamman in an yi la’akari da shine ya haɗa Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas a Nijeriya. Yayin ganawa da manema labarai, gwamnan yayi kira da gwamnatin tarayya da ta yi gaggawar gyara wannan titin…
Read More

Olympics: Dalilan da suka sanya ƴar Nijeriya karawa da keken aro – Ministan Wasanni

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ministan wasanni, John Enoh ya yi bayanin dalilan da su ka sanya ƴar wasan gudu a ɓangaren keke, Ese Ukpeseraye ke amfani da keken aro wajen karawa da takwarorinta a cigaba da gasar Olympics da ke gudana a Farisa, babban birnin ƙasar Faransa. Ƴar wasan wacce ta wallafa a shafinta na X cewa, la'akari da sanar da ita da aka yi batun lokacin karawar cikin ƙurarren lokaci wanda hakan ka iya sa ta rasa damar shiga sahun masu fafatawar, ya sanya ta karɓar aron na takwararta na ƙasar Jamus. A lokacin da ya ke magana game…
Read More

Olympics: Nijeriya ta shiga yanayi mafi muni yayin da Amusan ta gaza kai wa wasan ƙarshe

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƴar wasan tsere Tobi Amusan wacce ɗaya ce daga cikin zakarun duniya ta gaza kai wa wasan ƙarshe a ɓangaren tseren mita 100 a cigaba da fafatawa a gasar Olympics da ake yi a Farisa na ƙasar Faransa. Amusan ta zo ta uku ne a cikin daƙiƙu 12.55, wanda haka na nufin ba ta cikin fitattu biyun farko, amma ana sa ran ta zama mafi kyau cikin waɗanda aka kere su. Haka nan, ƙoƙarin ƴar Nijeriyar bai wadatar ba na shiga zango na takwas ɗin ƙarshe. Ganin haka ya sa ake hasashen ciyo tagulla ga Nijeriya…
Read More
Zaɓen shugaban ƙasar Amurka: Trump ya amince da muhawarantar Kamala Harris

Zaɓen shugaban ƙasar Amurka: Trump ya amince da muhawarantar Kamala Harris

Ɗan takar kujerar shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump, ya yarda da muhawarantar abokiyar karawarshi, mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris. Trump ya faɗi hakan ne a marecen ranar Juma'a, inda ya ce, ya amince da muhawara tsakanin sa da abokiyar karawarshi ta Jam’iyyar Democrat, mataimakiyar shugaban ƙasa, Kamala Harris, wanda za a yi a tashar FOɗ.  "Na yarda da tsayawa a tashar Foɗ don yin muhawara da kamala Harris a ranar Laraba, 4 ga watan satumber," Trump ya rubuta a shafinsa na TRUTH. Wallafawar Trump ta fito awanni bayan an tabbatar da mataimakiyar shugaban ƙasa a matsayin halastaciyyar 'yar takarar kujerar…
Read More
 A yi hattara da ’yan damfara a intanet!

 A yi hattara da ’yan damfara a intanet!

Babu makawa ga duk mai mu'amala da Intanet ko wayar salula ya san matakan kariya game yadda waɗansu ɓata gari ke baza tarko ta ko wacce irin dama su ka samu don su damfari jama'a. Idan muka ce yanar gizo to anan mu na nufin Ko wanne fanni na yanar gizo. Shin kai ma'abocin burauzin ne don karanta labarai, ko mai binciken ilmi, ko ma'abocin kafofin sada zumunci da dai sauran su. Za mu kawo hanyoyin da su ka fi shahara wajen yin damfara a yanar gizo, kuma sanin su zai taimaka wajen tsallake tarkon su. Haƙiƙa a wannan zamani…
Read More
Cafke sojan da ya harbe matashi a Zariya abin a yaba ne – Atiku

Cafke sojan da ya harbe matashi a Zariya abin a yaba ne – Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban Nijeriya Atiku Abubakar ya yabi rundunar sojin ƙasar da ta bayyana kama sojan da ake zargi da harbe wani matashi mai shekaru 16 a Zariya da ke Jihar Kaduna. Atiku wanda ya yi wannan yabo cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba, ya kuma bayyana alhininsa kan yadda matashin ya rasa ransa. Wazirin Adamawa ya ce akwai buƙatar a gudanar da bincike kan sauran zargin abubuwan da a jami’an tsaron suka yi a sassan ƙasar a lokacin zanga-zangar. “Ina kuma kira da a gudanar da…
Read More

Mafi yawa daga cikin masu zanga-zanga almajirai ne da ba su san manufar hakan ba – Gwamnan Nasarawa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya buƙaci Arewa ta magance matsalolinta, ya na mai cewa mafi yawancin waɗanda ke yin zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar Almajirai ne ba su san komai ba game da gangami. Zanga-zangar wacce aka faro a ranar 1 ga watan Agusta, an fara ta ne cikin lumana wanda daga baya ta sauya salo sakamakon samun bayanan sata da lalata kadarorin gwamnati da na al'umma, saboda haka aka sanya dokar hana fita wasu jihohi. "Mafi yawa daga cikin su ba su ma san ma'anar zanga-zanga ba. A lokacin da na yi magana da…
Read More
Ku samar wa al’umma shugabannin da suke buƙata – Farfesa Sani Malumfashi ga shugabannin jam’iyya

Ku samar wa al’umma shugabannin da suke buƙata – Farfesa Sani Malumfashi ga shugabannin jam’iyya

Daga RABIU SANUSI An buƙaci shugabannin jam'iyyu a Jihar Kano da su samar da 'yan takarar da za su tsaya zaɓe a ƙananan hukumomin da zai gudana nan bada daɗewa ba. Shugaban hukumar zaɓe na jihar Kano Farfesa Sani Lawan Malumfashi ne ya bayyana haka a yayin da yake ganawa da shugabannin jam'iyyu na  jihar Kano a ranar Alhamis ɗin wannan makon. Shugaban hukumar zaɓen ya ce a yanzu ne ya kamata jam'iyya ta samar da shugaban da zai kawo wa al'umma canjin da suke buƙata, waɗanda kuma za su taimaka wajen kawo ayyukan raya ƙasa da za su taimakama…
Read More