09
Aug
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Aƙalla ƙananan yara biyar ne aka tabbatar sun rasu cikin ƙasa da awa 24 sakamakon wata baƙuwar cuta a ƙaramar Hukumar Obi da ke Jihar Nasarawa. Babbar Jami’ar Binciken Cututtuka ta Jihar Nasarawa, Dokta Grace Tsakpa, ta tabbatar da mutuwar ƙananan yaran, inda ta ce an tura jami’an lafiya zuwa yankin domin gudanar da bincike. ƙauyen Gidinye da ke yankin Jenkwe na daga cikin wuraren da aka samu ɓullar wannan baƙuwar cutar mai kisa. Wakilin Manhaja ya gano cewa yaran shekarunsu 5 ne zuwa 15, kuma sun yi fama da ciwo ciki da ciwon…
