Labarai

Majalisar Dattijai za ta binciki gwamnatin Buhari bisa kashe Dala biliyan 1.5 a gyaran matatar Fatakwal

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI a Abuja Majalisar Dattijai ta nuna damuwarta kan yadda aka kashe Dala biliyan 1.5 wajen gyaran matatar mai ta Fatakwal lokacin gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a shekarar 2021 ba tare ganin abin a-zo-a-gani ba. Sanata Opeyemi Bamidele, wanda shi ne shugaban kwamitin musamman kan yin zargin zagon ƙasa ga tattalin arziki a fannin man fetur na Nijeriya, ya koka game da hakan ne a lokacin tattaunawa da masu-ruwa-da-tsaki a ranar Laraba a Abuja. Mista Bamidele, wanda kuma shi ne Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Dattawa, ya ce, ba daidai ba ne a riƙa wasarairai…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da shirin sayar da shinkafa ga ma’aikata

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da shirin sayar da shinkafa kan farashi mai rahusa ga ma'aikata wanda haka na nufin janye batun bayar da umarni ga waɗanda ke buƙata. Sanarwar ta fito ne daga wani sabon saƙo daga ma'aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnati a ranar Alhamis. Saƙon wanda ke ɗauke da sanya hannun Daraktan albarkatun al'umma, Aderonke Jaiyesimi, bai bayyana dalilan da su ka sanya aka janye batun ba. Haka nan, babu gamsashshen bayani game da dakatarwa ce ta din-din-din ko kuma ta wucin-gadi, ta na mai kira ga sauran ɓangarori da su…
Read More
Gwamnatin Neja ta tallafa wa iyalan waɗanda ƙasa ta rufta da su

Gwamnatin Neja ta tallafa wa iyalan waɗanda ƙasa ta rufta da su

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Iyalan mutanen da ƙasa ta rufta da su a wajen wani haƙar ma'adanan ƙarƙashin ƙasa a jihar Neja sun samu tallafin Naira miliyan 50 daga gwamnatin jihar. Tun kimanin watanni 2 da suka gabata kenan dai da ƙasa ta rufe waɗansu masu haƙar ma'adanai a yankin na Galadiman Ogo ta ƙaramar hukumar Rafi, da kawo yanzu aak lalubo gawarwakin mutane 10 sannan aka samu 8 da ransu inda har ya zuwa yanzu ake ci gaba da ƙoƙarin zaƙulu gawarwakin wasu mutane 4. Sakataren gwamnatin jihar Nejan Alhaji Abubakar Usman ya  ce duk da yake…
Read More
Wazirin Hausawan Abuja ya buƙaci Tinubu ya rage farashin kayan abinci

Wazirin Hausawan Abuja ya buƙaci Tinubu ya rage farashin kayan abinci

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wazirin Hausawan Babban Birnin Tarayya Abuja, Alhaji Ibrahim Mohammed Kamba, ya yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya rage farashin kayan abinci domin rage raɗaɗin da talakawa ke ciki. Kamba wanda ya yi wannan kiran a wata hira da manema labarai a Abuja kan halin da ƙasar ke ciki, ya kuma roƙi shugaba Tinubu da ya rage farashin man fetur. Ya kuma buƙaci Tinubu da ya samar wa jama’a taransfomomi masu kyau a matakin farko domin bunƙasa wutar lantarki, ya ƙara da cewa jama’a daga lunguna da saƙo na ƙasa ba su da ingatattun…
Read More

Gwamnati za ta bada tallafin Naira biliyan 110 ga sana’o’in matasa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ce ta sauya shirin zuba hannun jari na matasan Nijeriya (NYIF) zuwa ware Naira biliyan 110 da bayar da jari ga masu ƙananan sana'o'i. Ministar matasa, Dakata Jamila Bio Ibrahim ta faɗi hakan a Akure, babban birnin jihar Ondo a lokacin da ta ke ganawa da matasan Kudu-maso-Yammacin Nijeriya. Ta ce, an samu sama da matasa 200,000 cikin sati biyu da ke neman amfana da tallafin tun da aka sake kaddamar da shirin NYIF. Ministar ta kuma ce munafar shirin ita ce samar da sauƙi wajen samun aron kuɗi ga matasan don inganta…
Read More
Jigawa ta bai wa yara miliyan 1.4 rigakafin zazzaɓin cizon sauro

Jigawa ta bai wa yara miliyan 1.4 rigakafin zazzaɓin cizon sauro

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa ta samu nasarar kammala bai wa yara ƙananan miliyan 1.4 magungunan rigakafin zazzaɓin Maleriya. Kwamishinan Lafiya na Jihar Jigawa, Dakta Abdullahi Kainuwa ne ya bayyana haka, yayin da ya ke cewa an bai wa yara ‘yan ƙasa da shekara biyar maganin rigakafin zazzaɓin Maleriya na SMC, wato ‘Seasonal Maleria Chomopreɓention’ a faɗin jihar. Ya ce an gudanar da wannan gagarimin aiki ne tare da Shirin Kawar da Zazzaɓin Maleriya na ‘Malaria Consortium Programme’. Ya ce ƙananan yara 1,415,438 ne suka samu maganin na SMC a faɗin ƙananan hukumomi…
Read More
Hukumar DSS ta musanta kai farmaki ofishin NLC a Abuja

Hukumar DSS ta musanta kai farmaki ofishin NLC a Abuja

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hukumar Tsaro ta Farin Kaya a Nijeriya, DSS, ta musanta kai samame ofishin hedikwatar ƙungiyar ƙwadago ta NLC. A ranar Laraba da daddare ne dai wasu jami'an tsaro ɗauke da manyan makamai suka kai samame ofishin ƙungiyar, tare da yin waon gaba da wasu takardu. ƙungiyar ta NLC ta zargi jami'an tsaron farin kaya na DSS ta ƙaddamnar da samamen. ƙungiyar ta ce, jami'an sun isa ginin hedikwatar tata ne da ake kira Labour House, tun da daddare da misalin ƙarfe 8:30 To sai dai cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafukanta na sada…
Read More
Gwamnatin Tinubu ba ta biyan tallafin fetur, inji Ministan Kuɗi

Gwamnatin Tinubu ba ta biyan tallafin fetur, inji Ministan Kuɗi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya a ƙarƙashin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ta musanta mayar da tallafin man fetur, inda ta ce babu wani kasafin kuɗin da aka ware mata. Ministan Kuɗi Wale Edun ya bayyana haka a wata hira da ya yi kwanan baya a gidan talabijin na AIT. Edun ya ce ba a saka tallafin man fetur a cikin kasafin kuɗin ƙasar na 2024 kuma ya bayyana ci gaban tattalin arziki a matsayin dalilin kiyaye manufofin da ake ciki. “Babu tallafin mai a kasafin kuɗin. Muna da alamun cewa muna tafiya kan hanyar da ta…
Read More

Atiku ya soki Gwamnatin Tinubu kan yaɗa farfagandar ruɗar al’umma

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tawagar yaɗa labaru na tsohon shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ta soki tsarin isar da saƙo na gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ga ƴan Nijeriya, ta na mai zargin hakan a matsayin farfagandar ruɗar al'umma. Hakan na zuwa ne bayan da aka yaɗa wani tsohon bidiyo na shugaba Tinubu ta kafar X inda ya ke lallashin al'umma domin kare kasawar gwamnatinsa la'akari da zanga-zangar tsadar rayuwa da ake yi a faɗin Nijeriya. Asalin bidiyon an yin shi ne tun kafin wannan lokacin wanda tawagar ta ke ganin hakan a matsayin salo na wasa da hankulan al'ummar ƙasa…
Read More
Zanga-zanga ta kashe ma na kasuwa, inji mabaratan Kano

Zanga-zanga ta kashe ma na kasuwa, inji mabaratan Kano

Daga NASIR S. GWANGWAZO Wasu masu yawon barace-barace a kan titinan birnin Kano sun koka ga masu shirya zanga-zanga a faɗin Nijeriya da cewa, su mayar da wuƙarsu cikin ƙube, don nuna jinƙai a gare su, su na masu cewa, zanga-zangar da ake gudanarwa a faɗin ƙasar ta kashe kasuwarsu bakiɗaya. A cewarsu, akasarin masu bara a ƙasar su na samun abinda za su ci ne kawai, idan sun fito yawon bara kullum, inda yanzu haka zanga-zangar ta hana su sakat. An fara zanga-zanga a Nijeriya ne ranar 1 ga Agusta, 2024, don yin matsin lamba ga gwamnati kan halin…
Read More