Labarai

’Yan sanda sun tabbatar da kashe shahararren ɗan siyasa a Bauchi

’Yan sanda sun tabbatar da kashe shahararren ɗan siyasa a Bauchi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani soja ya bindige wani fitaccen ɗan siyasa mai suna Habibu Aminu Dankasa a ranar Laraba a ƙauyen Lere da ke ƙaramar Hukumar Tafawa Balewa a Jihar Bauchi. Rundunar ’yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da faruwar lamarin ga Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a wata tattaunawa ta wayar tarho. A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Ahmed Wakili, lamarin ya ta’azzara ne bayan wata hatsaniya da ta ɓarke tsakanin ’ya’yan jam’iyyar PDP daga ƙauyen Lere da jami’an tawagar ‘Operation Safe Haɓen’ da ke Tafawa Balewa. Rahotanni sun bayyana cewa wasu 'ya’yan jam’iyyar…
Read More
Har yanzu matatun man gida ba su samun ɗanyen mai a Naira ba – CORAN

Har yanzu matatun man gida ba su samun ɗanyen mai a Naira ba – CORAN

Daga MAHDI M. MUHAMMAD ƙungiyar Masu Mallakin Matatar ɗanyen Mai ta Nijeriya, CORAN, ta bayyana cewa har yanzu mambobinta ba su fara sayen ɗanyen mai a Naira ba, duk da amincewar da Gwamnatin Tarayya ta yi a baya-bayan nan. Sakatariyar hulɗa da jama’a ta CORAN, Echie Idoko, ta bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da ta yi da gidan talabijin na Channels, inda ta bayyana buƙatar samar da ƙa’idoji don aiwatar da umarnin Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC). Majalisar ta amince da sayar da ɗanyen man fetur ga matatun man Nijeriya da suka haɗa da matatar Dangote a naira domin…
Read More
An samu tagomashi a ɓangaren lantarki – Minista Adelabu

An samu tagomashi a ɓangaren lantarki – Minista Adelabu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, ya bayyana cewa ɓangaren wutar lantarkin Nijeriya ya samar da megawatts na wutan lantarki a ranar 27 ga watan Yulin 2024, inda ya bayyana shi a matsayin tsawon shekaru uku. Adelabu ya bayyana hakan ne a wajen taron ƙaddamar da cibiyar samar da wutar lantarki ta ma’aikatu a Abuja ranar Laraba. Yayin da yake bayyana nasarorin da aka cimma da kuma manufofin da za a cimma a nan gaba a fannin wutar lantarki, Ministan ya ce, “A ’yan kwanakin da suka gabata, a ranar 27 ga watan Yuli, mun samu nasarar…
Read More
Ɗan wasan ƙasar Portugal Pepe ya sanar da ritaya daga ƙwallon ƙafa

Ɗan wasan ƙasar Portugal Pepe ya sanar da ritaya daga ƙwallon ƙafa

Shaharren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na ƙasa Portugal Pepe ya sanar da ritayar shi daga wasan ƙwallon ƙafa. Pepe ɗan shekara 41, yayi wannan sanarwar ne ta hanyar wallafa bidiyo daga shafinsa na sada zumunta. Pepe in bamu manta ba, gogaggen ɗan wasan baya ne. Ya fara taka leda a ƙungiyar Maritino inda daga nan ya tafi ƙungiyar kwallon ƙafa da Real Madrid inda ya shafe shekaru 10 yana taka leda. Ya samu damar lashe kofuna kamar kofin zakarun turai na Champions League har guda uku, yayi nasara cin kofin nahiyar Turai a shekarar 2016. Pepe ya kasance ɗan wasa…
Read More
NIRSAL ta tallafi manoma 2000 a jihohi huɗu

NIRSAL ta tallafi manoma 2000 a jihohi huɗu

Hukumar NIRSAL ta kammala wani horo ga manoma a kan harkar rogo da kiwon cikin ruwa a jihohin Sokoto, Imo,Kwara da Oyo. Wannan shirin an yi shi ne domin ƙara wq manoman sani a kan yadda zasu samu bashi da kuma hanyar biya. Shirin ya samu aƙalla manoma 2000 da suka halarta tare da jami’an gwamnati. Ciyaman ɗin kwamitin noma na majalisar Imo, Mr Uche Agabige ya jinjinawa NIRSAL da ta sanya jihar ta Imo a wannan zagayen horon ga manoman. A jihar Imo, akwai aƙalla mutane 500 daga wajen horo biyu da aka tanada, ɗaya a cikin birni sai…
Read More
Kwastom za su buɗe shigo da abinci daga Ƙasashen waje sati mai zuwa

Kwastom za su buɗe shigo da abinci daga Ƙasashen waje sati mai zuwa

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanar da cewa dokar ɗage haraji kan kayayyakin abinci da magunguna za ta fara aiki a mako mai zuwa. Sanarwar ta fito ne daga bakin shugaban hukumar Kwastam Bashir Adeniyi a wata hirarsa da manema labarai. Hakan na nufin masu shigo da kayayayyakin abinci kamar shinkafa, alkama, masara, dawa da sauran hatsi, ba za su biya haraji ba har tsayin watanni uku. Wannan tsarin ya biyo bayan kudirin gwamnatin shugaban Tinubu na rage farashin kayan abinci don rage wa ‘yan kasa raɗaɗin tattalin arziki.
Read More

Gwamnan Filato ya sassauta dokar hana fita a Jos da Ɓukuru

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin jihar Filato ta sassauta dokar hana fita ta sa'o'i 24 da ta sanya a biranen Jos da Ɓukuru. Don haka, mazauna yankunan daga yanzu zasu ke zirga-zirga daga ƙarfe 2 na rana zuwa 6 na yamma. Sanarwar ta fito ne a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Daraktan harkokin labarai na gwamna Caleb Murfwang. Hakan na zuwa ne bayan da gwamnan ya shawarci hukumomin tsaro da su ka yi tsayin daka wajen ganin an kiyaye dokar hana fitar a yankunan.
Read More
Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana zirga-zirga

Gwamnatin Jihar Kaduna ta sassauta dokar hana zirga-zirga

Gwamnatin Kaduna ta sassauta dokar hana zirga-zirga daga 8 zuwa 6 na yamma. Wannan ya biyo bayan majalisar tsaro ta jihar ta sake zama domin duba yadda abubuwa ke tafiya a cikin jihar. Sanarwar ta fito daga Kwamishinan tsaro na cikin gida Samuel Aruwan a ranar 7 ga watan Agusta 2024. Sanarwar ta bayyana cewa, mutane za su iya fitowa su cigaba da al'amuransu na rayuwa daga 8 zuwa 6 yamma. In bamu manta ba, 4 ga watan Agusta gwamnatin Jihar kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga na tsawon awa 24 a birnin kaduna da Zaria sakamakon zanga-zangar yunwa ta…
Read More

An daina yayin juyin mulki yanzu a duniya – Al-Mustapha

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon shugaban jami'an tsaro na marigayi shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustapha (rtd) ya yi kira da a inganta harkar aikin rundunar soji madadin juyin mulki kamar yadda aka goyi bayan yin hakan a wasu wurare. Tsohon hafsan sojan ya na magana ne la'akari da kiraye-kirayen da wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa ke yi tare da ɗaga tutar ƙasar Rasha da nufin neman agajin ƙasashen waje. Helkwatar Tsaro ta yi gargaɗin cewa rundunar soji ba za ta karɓi duk wani kira da ya shafi juyin mulki ba, ta na mai cewa…
Read More
Mutum 20 sun mutu a kwale-kwale yayin da suke tsere wa ƴan bindiga a Zamfara

Mutum 20 sun mutu a kwale-kwale yayin da suke tsere wa ƴan bindiga a Zamfara

Aƙalla mutane ashirin ne suka rasa rayukansu yayin da suke ƙoƙarin tserewa daga harin ‘yan bindiga a ƙauyen Kali da ke ƙaramar hukumar Gummi a jihar Zamfara bayan kwale-kwalen su ya nutse. Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa ‘yan bindigar sun kewaye ƙauyen da misalin ƙarfe 1:00 na ranar Lahadi da ta gabata. “‘Yan bindigar a ranar Lahadi da ta gabata an ga sun nufi ƙauyen Kalli da babura ɗauke da manyan makamai domin kaiwa yankin hari, wanda hakan ya sa mutanen ƙauyen su ka tsere,” inji shi. Ya…
Read More