Labarai

Ku kare martabar dimokraɗiyya – Janar Musa ga takwarorinsa na ECOWAS

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban Ma'aikatan Tsaro na Nijeriya, Janar Christopher Musa ya yi kira ga takwarorinsa na ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS da su kare martabar dimokraɗiyya gwargwadon yadda dokokin ƙasashensu su ka shar'anta. Ya ce, faruwar juyin mulkin soji a ƙasashen yammacin Afirka sun haifar da barazana ga martabobi da darajojin demokraɗiyya. Blueprint ta ruwaito cewa, sojoji sun yi wa farin hula juyin mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso da Nijar cikin shekaru uku da su ka gabata. Janar Musa ya faɗi hakan ne a yayin ganawa da shugabannin tsaro na ƙasashen ECOWAS a Abuja…
Read More

Shugaba Tinubu ya naɗa shugabannin gudanarwa na Jami’o’in gwamnati

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin shugabannin gudanarwa na jami'o'i da manyan makarantun gwamnatin tarayya kamar haka: Jami'ar Nigerian Maritime, Okerenkoko, Jihar Delta: Temi Harriman -- Shugaba; Adeola Adeogun -- Memba; Benedict Aguele -- Memba; Freeman Kasa -- Memba; Babangida Alhassan Abdullahi -- Memba. Jami'ar kimiyya da fasaha, 'Nigerian University Of Science And Technology, Abuja': Rabe Mudi Bala -- Shugaba; Mr. Akinola Fagbemi -- Memba; Rakiatou Bagnou -- Memba; Alwel Egwurugu -- Memba; Femi Osabinu -- Memba. Jami'ar aikin gona ta gwamnatin tarayya da ke Bassam-Biri, Bayelsa, Federal University of Agriculture, Bassam-Biri: Bram…
Read More
Gyaran kurakuran baya ake, ba jawo wahala ba – Ministan Yaɗa Labarai

Gyaran kurakuran baya ake, ba jawo wahala ba – Ministan Yaɗa Labarai

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce babban abin da gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali a kai ba shi ne ta ɗora wa ‘yan Nijeriya wahala ba, sai dai ta gyara munanan tsare-tsare da matakan da ba su dace ba waɗanda a tarihi suka kawo cikas ga cigaban Nijeriya. A wata sanarwa da Mataimakin Ministan na Musamman kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabi'u Ibrahim, ya fitar, Idris ya bayyana haka ne a Abuja a ranar Laraba yayin da yake ganawa da jami’an diflomasiyya a Ma’aikatar Harkokin Wajen Ƙasar dangane da zanga-zangar da aka yi…
Read More
Rundunar soja ta cafke sojan da ya kashe wani ɗan zanga-zanga a Kaduna

Rundunar soja ta cafke sojan da ya kashe wani ɗan zanga-zanga a Kaduna

Sojojin Najeriya sun kama sojan da ya kashe wani matashi mai shekara 16, mai suna Isma’il Mohammed, yayin da yake kokarin dakatar da wasu matasa ƙokarin fasa shagunan mutane a unguwar Samaru da ke Zaria da sunan zanga-zanga. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Daraktan hulɗa da jama’a na sojojin, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya bayar a ranar Laraba a Abuja. Nwachukwu ya ce sojojin sun samu kiran gaggawa cewa wasu matasa sun taru a yankin Samaru na Zaria masu yawan gaske, suna ƙona tayoyi a kan titi suna jefa duwatsu ga jami’an tsaro. “Da isar su wurin, matasan…
Read More
Ba mu cikin masu zangon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasa – NNPC

Ba mu cikin masu zangon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasa – NNPC

Shugaban kamfanin NNPC Mele kyari yace kamfani bai karya doka ba wajen mu'amalar su da abokan kasuwanci, don haka a daina zargin kamfanin da kokarin kawo cikas ga harkar mai a ƙasar Kyari, yayi wannan jawabi ne a yayin da gurfana a gaban kwamitin majalisa domin amsa tambayoyi a kan wasu batutuwa da suka taso. Inda ya bayyana kasuwanci tatar mai, kasuwanci ne da kowa zai iya shigar sa saboda babu shubuha a cikin sa. Ya cigaba da cewa, dokar a bayyane take a kan harkokin ɗanyen mai da kuma sayarwa matatun mai na gida. Sannan yace dokar, ta bayyana…
Read More

Dawo da tallafin man fetur zai sa talauci ya tsananta a Nijeriya, inji Daraktan NOA

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Darakta Janar na hukumar Haɗin-kan Ƙasa, NOA, Issa-Onilu ya yi kira ga ƴan Nijeriya da su tsara hanyoyin gudanar da rayuwa a yanayin matsin tattali da ake fama da shi a sakamakon cire tallafin man fetur a ƙasar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ta yi. A wata hira da gidan talabijin na 'channels', Issa-Onilu wanda tsohon mai magana da yawun jam'iyyar APC ne, ya ce talauci zai yi tsanani matuƙar aka dawo da tallafin mai kamar yadda masu zanga-zangar tsadar rayuwa su ka buƙaci a yi a makon da ya gabata. Ya ce, duk mai…
Read More

Yanzu-yanzu: Shugabannin tsaro na ECOWAS na ganawa a Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugabannin tsaro na ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen yammacin Afirka, ECOWAS na ganawa a helkwatarta tsaro da ke Abuja. Shugaban Hukumar Ma'aikatan Tsaro ta Nijeriya, Janar Christopher Musa wanda shi ne kuma shugaban kwamitin shugabannin tsaro na ECOWAS shi ke jagorantar zaman. Mahlarta taron sun haɗa da; Ministan Tsaro, Muhammed Badaru, Ministan harkokin ƙasashen waje, Yusuf Tuggar da kuma shugaban kwamitin Majalisar Dattijai kan harkokin tsaro, Ahmed Lawan. Sauran sune; shugaban kwamitin Majalisa kan tsaro, wakilin Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro, shugabannin ma'aikatu, shugabannin hukumomin tsaro na ƙasashe face na Mali, Burkina…
Read More
Hukumar DSS ta kama ƴan ƙasar Poland bakwai a Kano bisa hannu a zanga-zanga

Hukumar DSS ta kama ƴan ƙasar Poland bakwai a Kano bisa hannu a zanga-zanga

Aƙalla ƴan ƙasar Poland bakwai hukumar ƴan sandar farin kaya na DSS ta kama bisa zargin hannu a cikin zanga-zangar yunwa da ke gudana. Wakilin DSS ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da ministan harkokin ƙasar waje Yusuf Tuggar. Wakilin yayin zantawa da manema labarai ya bayyana cewa an cafke su ne da bayyana tutocin wasu ƙasashe a yankin Arewa maso Yamma. Waɗanda suka halarci taron sun haɗa da ministan ƴaɗa labarai, Sufeton janar na ƴan sanda da ciyaman kwamitin majalisa harkokin ƙasashen waje.
Read More

Gwamnatin Zamfara ta musanta ware biliyan N19.3 don kayan kicin

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin jihar Zamfara ta ƙaryata batun cewa ta ware Naira biliyan 19.3 don sayan kayan kicin a kasafin shekarar 2024 wanda ta ce an yin haka ne domin a karkatar da tunanin mutane. Wani shafin yanar gizo ya ruwaito cewa, kwaskwarimar da aka yi wa takardar aikin kasafin kuɗin jihar ya nuna cewa ta ware biliyan N19.3 don sayan kayan ɗakin dafa abinci na shekarar 2024. A lokacin da ya ke magana kan lamarin, Kwamishinan Kasafi da Shiryawa na Jihar, Mallam Abdulmalik Gajam ya bayyana takaicinsa game da rahoton, ya na mai cewa an ware kuɗin…
Read More

Shugabannin tsaro sun haɗe hannu don fuskantar matsalolin tsaro

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A wani yunƙuri na nuna haɗin gwiwa don amfanin Nijeriya da al'ummarta, manyan hukumomin tsaro sun taru a hedikwatar tsaro da ke Abuja don samar da hanyoyin warware matsalolin zanga-zanga, tashin-tashina da kuma munanan shirye-shirye da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar ƙasa. Zaman wanda Shugaban Ma'aikatan Tsaron, Janar Christopher Musa ya jagoranta, ya ƙunshi Shugabannin rundunonin sojojin ruwa da na sama, Sufeto Janar na 'Yan sanda, shugabannin hukumomin shige da fice da na Kwastom, Darakta Janar na DSS da sauran manyan hukumomin tsaro. A lokacin zaman, duka jami'an sun bayar da bayanan shirye-shiryen da…
Read More