Labarai

Kayan abinci za su sauko – Kwastom ga masu zanga-zanga

Kayan abinci za su sauko – Kwastom ga masu zanga-zanga

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta sanar da cewa farashin abinci zai ragu sosai nan ba da jimawa ba. Shugaban hukumar Kwastam na Najeriya, Bashir Adeniyi, ne ya bayyana hakan a hedkwatar tsaro, Abuja, ranar Talata, 6 ga watan Agusta, 2024. Adeniyi na daga cikin shugabannin hukumomi da suka halarci taron sirri na tsare-tsare da shugaban hafsan soji, Janar Christopher Musa, ya kira.Za a iya tunawa cewa, dubban ‘yan Najeriya sun shiga zanga-zanga a faɗin ƙasa ranar 1 ga watan Agusta, inda suka gabatar da buƙatu daban-daban, ciki har da matsalar tsadar abinci da hauhawar farashi. Da yake zantawa da manema…
Read More
Tinubu ya naɗa shugabannin asusun kula da makarantun gaba da sakandire

Tinubu ya naɗa shugabannin asusun kula da makarantun gaba da sakandire

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin shugaba da membobin gudanarwa na asusun kula da manyan makarantu na ƙasa "Tertiary Education Trust Fund (TETFund)". Mutanen da ya naɗa ɗin sun haɗa da: (1) Alhaji Aminu Masari -- Shugaba, (2) Sanata Sani Ɗanladi -- Memba (3) Mista Sunday Adepoju -- Memba (4) Mista Nurudeen Adeyemi -- Memba (5) Madam Esther Onyinyechukwu Ukachukwu -- Memba (6) Malam Turaki Ibrahim -- Memba (7) Mista Aboh Eduyok -- Memba. Shugaba Tinubu ya hore su da su yi aiki cikin himma domin cimma manufofin da aka sanya a gaba na tallafawa ilimin gaba…
Read More
Sanata Ndume ya ba jami’iyyar APC haƙuri a kan sukar gwamnatin Tinubu

Sanata Ndume ya ba jami’iyyar APC haƙuri a kan sukar gwamnatin Tinubu

Tsohon bulaliyan Majalisar Dattijai, Sanata Ali Ndume ya ba shugabancin jam'iyyar APC mai mulki haƙuri saboda rashin tuntuɓar jam'iyyar kafin yayi zargin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da rashin kyakkyawan shugabanci. Ndume wanda ke wakiltar Kudancin Borno a majalisar dattijai, duk da haka ya ce yana nan kan bakarsa, yana jaddada cewa duk abin da ya faɗa ko ya aikata ya fito ne daga kishin ƙasa. "Jiya jam’iyya ta gayyace ni kuma ga ni a nan don mu tattauna abubuwa game da abin da ya faru wanda kowa ya sani, haƙiƙa shugaban jam’iyya ba wai kawai shugaban jam’iyya bane a…
Read More
Farfaɗo da Masana’antar Auduga: Matasa miliyan 1.4 ne za su sami aikin yi

Farfaɗo da Masana’antar Auduga: Matasa miliyan 1.4 ne za su sami aikin yi

Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wani gagarumin shiri na farfaɗo da masana’antar auduga a Najeriya, da nufin samar da ayyukan yi sama da miliyan 1.4 a duk shekara a fannin. A cewar wata sanarwa da ta fito daga ofishin mataimakin shugaban ƙasar Kashim Shettima, shirin na haɗin gwiwa ne tsakanin gwamnati da kwamitin ba da shawara kan auduga (ICAC). Da yake jawabi a wajen wani taro da jami’an ICAC, mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima, ya jaddada buƙatar ganin masu ruwa da tsaki sun haɗa kai don bunƙasa darajar auduga a fannonin da suka haɗa da noma, saka, ciyawa, da murza…
Read More
Shugaba Tinubu ya naɗa shugabannin Ma’aikatar Jinƙai

Shugaba Tinubu ya naɗa shugabannin Ma’aikatar Jinƙai

A ƙoƙarinsa na ganin shirin tallafawa al'umma ya gudana yadda ya kamata, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa shugabannin ma'aikatar jinƙai, agaji da kyautata rayuwar al'umma ta ƙasa. "Federal Ministry of Humanitarian Affairs, Disaster Management and Social Development". Mutanen da shugaba Tinubu ya naɗa sun haɗa da: Dakta Badamasi Lawal, a matsayin shugaban shirin samarwa al'umma jari "National Social Investment Programme Agency (NSIPA)". Dakta Lawal yana da digirin digirgir a fannin ilimi, kuma tsohon kwamishinan ilimi ne a Jihar Katsina. Funmilola Olotu, a matsayin shugabar shirin kula da al'umma. Tana da digirin digirgir a fannin kasuwanci, sannan kuma, babbar…
Read More

Yadda masu zanga-zanga su ka mamayi gidan Wike a Ribas

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wasu masu zanga-zangar tsadar rayuwa sun taru a wajen gidan Ministan Abuja kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da ke Fatakwal babban birnin jihar, domin su bayyana kokensu. Wata ɗaukar bidiyo da ya karaɗe kafafen sadarwa ya nuna yadda masu zanga-zangar su ka yi dandazo inda da dama daga cikin su ke riƙe da takardun da ke ɗauke da saƙonni masu yawa. Haka nan, an ga sinƙi-sinƙin jami'an tsaro da su ka bazu a wajen cikin shiri don tabbatar da tsaro a yankin. A lokacin zanga-zangar, an samu wasu na rera tsohon taken ƙasa yayin…
Read More
Babban Hafsan Sojoji ya kira taron gaggawa na tsaro

Babban Hafsan Sojoji ya kira taron gaggawa na tsaro

Babban Hafsan Sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa ya kira wani taron tsaro na gaggawa a hedkwatar tsaro da ke babban birnin tarayya Abuja. Taron ya biyo bayan umarnin Shugaban ƙasa Bola Tinubu na cewa a tabbatar an kawo tsaro saboda zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar. Taron ya sami halarcin hukumomin DSS, NIA, DIA da sufeton ƴan sanda. Taron ya sami halartar manyan sojojin ƙasar kamar su, Janar Lagbaja, Air marshall Hassan Abubakar da kuma wakilan hukumar kwastom da hukumar shige da fice ta Immigration. A na sa rai taron zai fara nan ba da jimawa ba.
Read More
Gwamnati ta sanya ido ga jagororin zanga-zangar yunwa

Gwamnati ta sanya ido ga jagororin zanga-zangar yunwa

Gwamnatin Tarayya ta sanya ido kan jerin sunayen masu jagorancin zanga-zangar yunwa da ke gudana a faɗin ƙasar. Hakan ya bayyana ne daga bakin shugaban hukumar shige da fice ta Nijeriya, Kemi Nandap bayan fitowa daga tattaunawar tsaro da shugaban ƙasa. Nandap wadda ba ta bayyana sunayen waɗanda a ka sanya sunayen su a jerin waɗanda a ke dako, tace ta mafi yawansu ba su zaune a Nijeriya, suna zaune a ƙasashen ƙetare. Ta cigaba da bayyana cewa jami'an hukumar sun ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro a iyakokin ƙasa da sama domin gudun shigowar agaji daga wajen ƙasar.
Read More

Kamala Harris ta zaɓi ɗan takarar Mataimakin Shugaban Ƙasa a zaɓen Amurka

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mataimakiyar shugaban ƙasar Amurka kuma ƴar takarar kujerar shugabancin ƙasar, Kamala Harris ta sanar da gwamnan jihar Minnesota, Tim Walz a matsayin abokin tafiyarta a cigaba da shirye-shiryen zaɓen ƙasar. Hakan na zuwa sakamakon karawa da za ta yi da tsohon shugaban ƙasar, Donald Trump a zaɓen da ke tafe a watan Nuwamba, 2024. Walz ya zo da tsarin shiga karkara kamfe a sassan ƙasar ga jam'iyyar Democrat da karɓar tsare-tsaren ɓangarori daban-daban da kuma inganta ɓangaren kula da ma'aikata.
Read More