06
Aug
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Litinin 5 ga watan Agusta ne Naira ta samu farfaɗowa akan Dala da kaso 0.6 a kasuwar sunku inda a ke sayar da ita a N1,607.15. Wata sanarwa daga FMDQ wanda zaure ne da ke kula da canjin kuɗin Nijeriya a kasuwannin duniya na NAFEM ya ce, Naira ta samu ribar N9.93 wanda ke wakiltar kaso 0.6 idan an kwatanta da darajarta ta ranar 2 ga watan Agusta da ke matakin N1,617.08 kowace Dala ɗaya. Sakamakon haka, an samu raguwar adadin a ke fita a kullum daga Dala miliyan 131.55 zuwa Dala miliyan 77.09…
