Labarai

DSS ta kama telolin da ake zargin su da ɗinkawa masu zanga-zanga tutocin Rasha

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI 'Yan sandan farin kaya ta DSS ta sanar da kama wasu teloli a jihar Kano da ke ɗinka tutocin ƙasar Rasha waɗanda ake zargin masu zanga-zangar tsadar rayuwa ne za su yi amfani da su. Mai magana da yawun hukumar, Peter Afunaya ya faɗi hakan a ranar Litinin cikin wata takarda da ya fitar, ya na mai cewa su na binciken gano waɗanda ke ɗaukar nauyi tare da kama su don a hukunta su. Haka nan, Peter ya ce rahoton da ke yawo cewa sun kama wani mai suna Adaramoye Michael, shugaban ƙungiyar 'youth rights campaign'…
Read More
Gwamnatin Tinubu ta ƙaddamar da shirin cibiyoyin ƙera kayan gine-gine

Gwamnatin Tinubu ta ƙaddamar da shirin cibiyoyin ƙera kayan gine-gine

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaddamar da shirin kafa cibiyoyin ƙera kayayyakin gine-gine da ake amfani da su wajen gine-gine a shiyyoyi shida na Nijeriya. Za a kafa cibiyar shiyyar Kudu maso yamma a jihar Ogun, kudu maso gabas a jihar Abia, kudu maso kudu a Warri ko Asaba dake jihar Delta, Arewa ta Tsakiya a Ajaokuta dake jihar Kogi, Arewa Maso Yamma a Jihar Kano, sai kuma Arewa maso gabas a jihar Gombe. Wannan cibiyoyi zasu samar da ayyukan yi ga dubban matasa a faɗin ƙasar, a lokaci guda kuma zasu rage tsadar kayayyakin…
Read More
Masu zanga-zanga sun yi artabu da sojoji bayan ƙin bin dokar hana fita a Jos

Masu zanga-zanga sun yi artabu da sojoji bayan ƙin bin dokar hana fita a Jos

Matasa a garin Jos sun ƙarya dokar hana zirga-zirga da gwamnatin jihar ta sanya, inda da daman su suka fito yin zanga-zangar. Wani faifan bidiyo ya nuna yadda jami'an tsaro, sojoji da ƴan sanda su kayi ƙokarin shawo kan matasan amma abun ya ci tura, sai dai rabuwa su ka yi da su. In ba mu manta ba, Gwamnan Jihar Jos, a safiyar yai ya sanya dokar hana zirga-zirga a wasu sassa na cikin Jihar saboda gudun tashin hankali ganin yadda zanga-zangar ta fara rikiɗewa saboda shiga ɓatagari.
Read More
Bayan gurfanar da mutane 632, Gwamnan Kano ya magantu kan masu ɗaga tutar Rasha

Bayan gurfanar da mutane 632, Gwamnan Kano ya magantu kan masu ɗaga tutar Rasha

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano An gurfanar da mutane 632 da laifin wawure dukiyar jama’a yayin da masu zanga-zangar ke ci gaba da yin tattaki ɗauke da tutocin ƙasar Rasha a Kano, Gwamnatin jihar Kano ta sanar da gurfanar da wasu mutane 632 da ake zargi da lalata kayayyakin gwamnati da sace kayan jama’a da yayin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar, Manhaja ta ruwaito cewa, an ga matasa masu zanga-zanga suna rera waƙoƙin nuna adawa da gwamnati da kuma riƙe da tutar kasar Rasha, a wurare irin su Mandawari da Dakata da Rimin…
Read More

Kotu ta dakatar da sayar da Nigeria Air ga Ethiopian Airlines

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata babbar kotun tarayya da ke Legas, ta haramta sayar da tashar jirgin sama ta 'Nigeria Air' ga 'Ethiopian Airlines'. Kotun ta yi hakan ne bayan da ta yi la'akari da bayanan da ke cikin ƙarar da aka shigar. Mai Shari'a, Ambrose Lewis-Allagoa ya yi umarnin cewa, za a dakatar da shirin gwamnatin tarayya na samar da tsarin kula na kai ga Nigeria Air. An gabatar da hukuncin ne da cibiyar masu kula gudanar da tashar jirgin da kuma wasu masana'antun jiragen sama guda biyar su ka shigar inda su ka yi nasara a ƙarar. Mai…
Read More

Zanga-zanga: Tinubu ya kira zama na gaggawa da shugabannin tsaro

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake cigaba da gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a yau Litinin, Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ganawa da shugabannin harkar tsaro a Fadar shugaban ƙasa. Su na gudanar da zaman ne ƙarƙashin jagorancin Majalisar tsaro ta Ƙasa inda ake tattauna batun zanga-zangar tsadar rayuwa da gazawar shugabanci. Mahlarta taron sun haɗa da; Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima; Shugaban Ma'aikatan tsaro, Janar Christopher Musa; Shugaban Ma'aikatan Fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila; Sufeto Janar na Ƴan sanda, Kayode Egbetokun da sauran manyan ma'aikatan harkar tsaro. A jiya ne shugaba Tinubu yi gabatar da jawabi game da…
Read More

‘Yan sanda sun kama mutane 64, sun ƙwato kayan da ɓata-gari suka wawashe a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar ƴan sanda a jihar Katsina ta ce ta kama matasa 64 da suka sace kayan jama'a da na gwamnati ciki har da buhunan takin zamani 693 bayan da ɓata-garin suka ɓalle ma'ajiyar gwamnati a yayin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa da rashin tsaro da ta rikiɗe zuwa tarzoma a jihar. Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyanawa manema labarai hakan a birnin Katsina. Tun farko, rundunar ta fitar da wata sanarwa inda ta yi kira ga iyaye akan su kula da ƴaƴansu tare da jan kunnensu kan su guji shiga ayyukan da suka…
Read More
Zanga-zanga: Gwamnatin Kaduna ta sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya

Zanga-zanga: Gwamnatin Kaduna ta sa dokar hana fita a Kaduna da Zariya

Daga USMAN NASIR KAROFI Gwamnatin Jihar Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga tsawon awa 24 a biranen Kaduna da Zariya. Hakan ya biyo bayan taron majalisar tsaro ta jihar da ya wakana a yau Litinin. Sanarwa, wacce kwamishina mai kula da Ma’aikatar Tsaro da Gida, Samuel Aruwan, ya fitar ta ce, an samu hujjoji masu ƙarfi da ke nuni da cewa ɓatagari sun shiga cikin zanga-zangar lumana da ake yi. Hakan ya sanya sun kai farmaki da dukiyoyin al'umma da dama a jihar. A dalilin wannan, majalisar tsaro ta jihar ta ga ya dace a sanya dokar hana zirga-zirga a…
Read More

IBB ya musanta zargin neman dawo da mulkin soji a Nijeriya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya musanta zargin cewa ya na son a dawo da mulkin soji a Nijeriya, ya na mai cewa demokraɗiyya ta na nan daram. Wata sanarwa da aka wallafa a shafin X, ta ce IBB ya ce, "Nijeriya ta kasance cikin yanayi mafi kyau a lokacin mulkin soji yayin da mulkin demokraɗiyya ya haifar da sanya ƙasar cikin ƙunci." Sai dai wata sanarwa daga ofishinsa na yaɗa labaru mai ɗauke da sanya hannun Mahmud Abdullahi ta ce, Janar Babangida bashi da shafin X, ya na mai jaddada…
Read More

Gobara ta ƙone rijiyar man NNPCL

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da tace man fetur ta NUPRC, ta ce sun samu rahoton kamawar gobara a rijiyar Akaso mai baki huɗu da kamfanin NNPC ke gudanarwa a ranar Asabar. Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Laide Shonola ya fitar a ranar 3 ga watan Agusta ta ce, lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11:12 na dare a ranar Juma'a inda gobarar ta faɗaɗa zuwa rafin da ke kusa da wajen. Shiyyar gudanarwa ta 18 ta NNPC ta tabbatar da cewa an samu ɗaukin gaggawa domin kashe gobarar da kuma keɓance wajen ta…
Read More