Labarai

Ku sanya kayan gidan jaridarku lokacin zanga-zanga – ‘Yan sanda ga manema labarai

Ku sanya kayan gidan jaridarku lokacin zanga-zanga – ‘Yan sanda ga manema labarai

Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja Rundunar ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ta buƙaci ‘yan jarida, waɗanda za su fito filin dagar zanga-zangar matsin rayuwa da ake gudanar da su tabbata sun sanya riguna mai ɗauke da alamar aikinsu a lokacin fitowarsu. Wannan sanarwa ta fito daga bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Abuja, S. Josephine Adeh, a yammacin Lahadi. Sanarwar ta ce, “Kwamishinan ‘Yan Sandan Babban Birnin Tarayya Abuja ya umarci ƴan jarida da za su fito aiki ranar Litinin, domin ɗaukar yadda zanga-zanga za ta wakana, da su sanya kayan gidan jaridarsu, sannan su tabbatar suna da katin…
Read More
Yadda za ku buɗe layukan wayarku ba tare da zuwa kamfani ba

Yadda za ku buɗe layukan wayarku ba tare da zuwa kamfani ba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD ƙungiyar masu kamfanonin wayar ta bayyana yadda mutanen da aka rufe wa layukan za su iya buɗe su. A cikin sanarwar, ta ce mutane na iya amfani da hanyar latsa wasu lambobi domin haɗa layulan su da lambar Shaidar ɗan ƙasa don tantance matsayin layukansu da kuma buɗe su. Sai dai sanarwar ta ce idan har aka kasa buɗe layi ta hanyar amfani da lambobin, mutane za su iya zuwa ofisoshin kamfanonin waya domin kai ƙorafi. An wari gari galibin masu amfani da layukan MTN da 9mobile ba su iya kira tun daren Asabar. Wannan lamarin…
Read More
Zanga-zanga: Soyinka ya soki jawabin Tinubu

Zanga-zanga: Soyinka ya soki jawabin Tinubu

Farfesa Wole Soyinka ya soki jawabin shugaba Tinubu saboda a ciki bai yi Allah wadai da abinda jami'an tsaro suke yi ma masu zanga-zanga ba. Soyinka ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar safiyar Lahadi, in da yace, jawabin ko kaɗan bai yi magana a kan irin hare-hare da jami'an tsaro ke kaiwa masu zanga-zangar lumana ba. Soyinka ya bayyana cewa, yanayin matsi na rayuwa da yunwa a ƙasa shi ya sanya mutane suka fito don nuna fushin su. Amma abun kunya sai a ka samu jami'an tsaro suna harbin masu zanga-zangar nan don kawai sun fito…
Read More

NUJ ta roƙi hukumomi su daina wulaƙanta ƴan jarida

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar ƴan jarida ta Ƙasa, NUJ ta yi alla-wadai da cin mutunci da wulaƙanta ƴan jaridan da ke ɗaukar rahotannin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya da wasu ke yi. Sakataren ƙungiyar, Achike Chude ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi inda ya ce duk da ƙalubalen da ƴan jarida ke fuskanta, hakan bai sanya su kasa sauke nauyinsu na sanar da al'umma, wayar mu su da kai da kuma ilimantar da su ba. Ya ce, ƴan jarida sun yi ta ƙoƙarin ruwaito labarai kan yadda ta ke kasancewa a zanga-zangar tsadar…
Read More

Yanzu-yanzu: Tinubu ya bayyana ribar tattalin arziƙi da aka samu cikin watanni 14

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ribar da aka samu a ɓangarorin tattali da zuba hannun jari a ayyuka su suka sa babu buƙatar yin zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya. A yayin wata ɗauka ta kai-tsaye, Tinubu ya ce gwamnatinsa ta samu jimillar kuɗin shiga da adadinsu ya kai kimanin Dala tiriliyan 9.1 a kashin farko cikin biyu na shekarar 2024. Ya ce gwamnatin tarayya ta rage bashi zuwa kashi 68 daga kashi 97 a shekarar 2023 cikin watanni 13. Sannan kuma ta samar da hanyar warware bashi a cinikayyar ƙasashen waje na Dala…
Read More
Tallafin biliyan N570: Ku binciki gwamnoninku – Shinkafi ga ‘yan Nijeriya

Tallafin biliyan N570: Ku binciki gwamnoninku – Shinkafi ga ‘yan Nijeriya

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Zamfara Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya mayar da martani da kakkausar murya ga gwamnonin Ƙasar nan kan kalaman da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a yau, cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancinsa tun daga farko har zuwa yau an baiwa kowannen su biliyan 570 ga kowanne daga cikin Gwamnonin jihohin kasar 36, yana mai kira ga ‘yan Nijeriya da su ɗora wa gwamnoninsu alhakin halin ƙuncin tattalin arzikin da suke ciki a halin yanzu. Shinkafi wanda shi ne Babban Daraktan ƙungiyar Patriots for Advancement of Peace…
Read More

NYSC ta ƙi karɓar ɗaliban HND da ba su yi IT ba

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da masu yi wa Ƙasa hidima, NYSC ta gargaɗi ɗaliban da su ka kammala karatu a makarantun 'polytechnic' da 'minotechnics' cewa wajibi ne su gabatar da takardar shaidar yin horon IT na shekara ɗaya kafin ta karɓe su. Shugabar hukumar reshen jihar Legas, Misis Yetunde Baderinwa ta faɗi hakan a yayin wani hira da jaridar 'News Agency Nigeria' a ranar Asabar a Legas inda ta ce hukumar ta fitar da takardar umarnin ne ga dukkan ɗaliban da hukuncin ya shafa. Ta ce "sanannen abu ne cewa a kwanakin nan wasu daga cikin ɗaliban makarantun…
Read More
An sassauta dokar fita a Kano da Yobe

An sassauta dokar fita a Kano da Yobe

Gwamnatocin jihohin Yobe da Kano sun sassauta dokar hana fita ta sa’o’i ashirin da huɗu da suka kafa a wasu garuruwa. In bamu mance ba, gwamnatocin sun sanya dokar hana fita bayan zanga-zangar adawa da matsalar tattalin arziki da ta rikiɗe ta koma tashin hankali A wani jawabi da kwamishinan yaɗa labarai na jihar Kano Malam Baba Ɗantiye ya sanar a ranar Lahadi, ya ce dokar hana fita a jihar yanzu ta fara daga ƙarfe 8 na safe zuwa ƙarfe 2 na rana. Ya ce an gyara dokar hana fita ne domin dawo da zaman lafiya a jihar. Dantiye ya…
Read More