Tallafin biliyan N570: Ku binciki gwamnoninku – Shinkafi ga ‘yan Nijeriya

Spread the love


Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Zamfara Dr. Sani Abdullahi Shinkafi ya mayar da martani da kakkausar murya ga gwamnonin Ƙasar nan kan kalaman da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a yau, cewa gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancinsa tun daga farko har zuwa yau an baiwa kowannen su biliyan 570 ga kowanne daga cikin Gwamnonin jihohin kasar 36, yana mai kira ga ‘yan Nijeriya da su ɗora wa gwamnoninsu alhakin halin ƙuncin tattalin arzikin da suke ciki a halin yanzu.

Shinkafi wanda shi ne Babban Daraktan ƙungiyar Patriots for Advancement of Peace and Social Development kuma tsohon sakataren jam’iyyar APGA ta ƙasa ya bayyana haka a yau Lahadi yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labarai a Gusau ta wayar tarho.

A cewarsa, gwamnonin jihohi 36 ne manyan matsalolin Ƙasar nan ba gwamnatin tarayya ba.

Ya ƙalubalanci gwamnonin da yin amfani da kuɗin da aka ba su don biyan bukatun kansu maimakon yi wa al’ummarsu abin da suke buƙata.

“Waɗannan gwamnonin su ne manyan matsalolinmu a Ƙasar nan, kuma abin takaici ne yadda kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta baiwa kowannen su biliyan dari biyar da saba’in akasari sun karkatar da su ne don biyan buƙatan kansu, ta hanyar naɗe-naɗen mukaman siyasa, cin hanci da rashawa, ba tare da amfani da kuɗaɗen don ci gaban al’ummarsu ba”.

“Ina kira ga ‘yan Nijeriya musamman matasa da marasa galihu dasu ɗora alhakin duk wata matsalar rayuwar da suke ciki ga gwamnonin jihohinsu tare da bincikar su yadda suka yi da kuɗaɗen da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba su a cikin shekara ɗaya,ba su ɗora laifin gareshi ba.” Yace

Ya buƙaci gwamnatin tarayya da ta riƙa duba hanyoyin da gwamnonin suka bi wajen salwantar da kuɗaɗen da aka basu da waɗanda za a basu nan gaba a kowane mataki domin ci gaban ƙasa.

Dangane da batun manufofin samar da abinci na gwamnatin tarayya, Shinkafi ya buƙaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ruɓanya jajircewa wajen magance matsalar rashin tsaro domin samun nasarar aiwatar da shirin na samar da abinci a Ƙasar.

A cewarsa, rashin tsaro ne ya addabi yankin arewacin ƙasar musamman arewa maso gabas da arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya.

“A jihar Zamfara, Katsina, Sokoto, Kebbi, Kaduna, da sauran jihohin Arewa ta tsakiya sama da kashi 80 na gonakin da ake nomawa ba za a iya nomawa ba, kuma manoma ba sa iya samun damar yin noma, don haka akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta ɗauki ƙwararan matakai don magance ‘yan bindiga. Ya ƙara da cewa

“A game da zanga-zangar da ake yi a kasar baki daya, idan ka lura, masu zanga-zangar, ba wai suna tada hankali ba ne don neman dawo da tallafin man fetur, amma sun bayar da muhimmanci sosai kan rashin tsaro da ya addabi yankin, don haka akwai buƙatar shugaban ƙasa ya taka muhimmiyar rawa wajen yaƙi da ‘yan bindiga a yankin. domin a samu zaman lafiya”.

Shinkafi ya ba da shawarar cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta samar da shirin farfaɗo da tattalin arziki cikin sauri da wasu Ƙarin hanyoyin bunƙasar tattalin arzikin domin gwamnatin tarayya ta farfaɗo da tattalin arzikin ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi