Labarai

Harbin masu zanga-zanga: Atiku ya kai Tinubu gaban Majalisar Ɗinkin Duniya da Kotun Duniya

Harbin masu zanga-zanga: Atiku ya kai Tinubu gaban Majalisar Ɗinkin Duniya da Kotun Duniya

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya kuma jagoran jami'iyyar adawa ta PDP yayi Allah wadai da buɗe ma masu zanga-zangar lumana da jami'an tsaro su ka yi a garuruwan Abuja da kano. Atikun yace, dole jami'an tsaro su ba ƴan ƙasa kariya a lokacin da suke gudanar da zanga-zanga domin tsarin doka ya basu dama. Amma abin kunya ne yadda waɗanda ya kamata su ba da tsaro, sune suke buɗe ma mutane wuta yayin da suke aiwatar da abin da doka ta basu dama. Atikun yayi kira da Majalisar Ɗinkin Duniya da kotun manyan laifuka na duniya ta sanya idanu a…
Read More
Muhimman batutuwan tattalin arziki da jawabin Shugaba Tinubu ya ƙunsa

Muhimman batutuwan tattalin arziki da jawabin Shugaba Tinubu ya ƙunsa

Muhimman batutuwan tattalin arziki da jawabin Shugaba Tinubu ya ƙunsa Jawabin Shugaban Ƙasa Tinubu ya ƙunshi wasu muhimman batutuwa a kan tattalin arziki Nijeriya. Waɗannan batutuwa su ne: Cire tallafin man fetur da dala domin liƙe hanyoyin fitar kuɗi. Samun ƙari a kan harajin da gwamnati ke amsa wanda ya haura tiriliyan 9.1 a watanni ukun farkon 2024 Raguwar biyan bashi da haraji daga kasa 97% zuwa kaso 67 a cikin watanni 13 Biyan bashin dala ga mutane da kamfanoni wanda aƙalla ya kai dala biliyan biyar Manyan ayyukan gina ƙasa kamar titin Lagos-Calabar da kuma Sokoto- Badagry Sauyi a…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya yi magana kan cire tallafin man fetur

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya ce gwamnatinsa ta cire tallafin man fetur da rushe tsarin cinikayyar ƙasashen waje ne sakamakon koma baya da hakan ke haifar wa cigaban tattalin arziƙin Nijeriya. Tinubu ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke gabatar da jawabin kai-tsaye game da zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya, ya na mai cewa tattalin arziƙin ƙasa na fuskantar matsalolin durƙushewa tsawon shekaru saboda rashin tsare-tsare da ɓangaren ya fuskanta. Tinubu ya ce, "sama da shekara ɗaya, Nijeriya ta kai wani mataki da ba za ta iya amfani da tsare-tsare na wucin-gadi wajen…
Read More
Cikakken jawabin Shugaba Tinubu kan zanga-zanga

Cikakken jawabin Shugaba Tinubu kan zanga-zanga

FASSARAR JAWABIN MAI GIRMA BOLA AHMED TINUBU SHUGABAN KASA KUMA BABBAN KWAMANDAN ASKARAWAN NAJERIYA. A KAN ZANGA-ZANGAR GAMA-GARI RANAR LAHADI 4 GA GASKIYA 2024 Yan uwanayan Nigeria! Ina magana ne da ku a yau cikin alhini, tare da kokarin sauke nauyin da ke wuyana cikin gaggawa, hakan na faruwa ne saboda sanin irin tashe-tashen hankula da zanga-zangar da aka yi a wasu jihohin mu ta haifar. Wani abin takaici shine yadda aka sami tarin hazikan matasan Najeriya cikin zanga-zangar wadan da basu da wani buri ko mafarki sai na ganin an samu ci gaba mai kyau da dorewa a kasar…
Read More
‘Yan sanda sun musanta kashe masu zanga-zanga a Katsina

‘Yan sanda sun musanta kashe masu zanga-zanga a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta ce ba a samu asarar rayuka ba a jihar yayin zanga-zangar tsadar rayuwa wadda ta rikiɗe zuwa tarzoma a wasu jihohin ƙasar nan. Kakakin rundunar ASP Abubakar Sadiq Aliyu, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar. Kafin fitar da wannan sanarwa rahotanni daban daban sun bayyana cewar jami'an tsaro sun kashe masu zanga zanga biyu tare da jikkata wasu a ƙokarin jami'an tsaron na tarwatsa matasan da suka yi yunƙurin shiga gidan gwamnatin jihar. Rundunar ta yi kira ga al'uma akan su yi watsi…
Read More
An yi zanga-zangar goyon bayan Tinubu a Kano

An yi zanga-zangar goyon bayan Tinubu a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Masu zanga-zangar goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu sun fito kan tituna a Jihar Kano. Masu wannan zanga-zanga suna yin ta ne a daidai lokacin da Nijeriya ta ɗauki zafi da zanga-zangar nuna adawa da halin yunwa da tsadar rayuwa a ƙasar. Masu wannan zanga-zanga sun fito ne ta titin Audu Baƙo da kuma Farm Centre suna bayyana adawa ga abin da suka kira zanga-zangar tashin hankali. Sun kuma yi taro a Fadar Sarkin Kano da ke Nasarawa, inda suka saurari jawabai kan hanyoyin da za a magance matsalolin da ke addabar ƙasar. Da…
Read More

Mu na so Tinubu ya taɓo batun haƙƙin waɗanda aka kashe a jawabinsa – AAC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da aka samu sanarwar jawabin da Shugaba Tinubu zai yi a gobe Lahadi, jam'iyyar AAC ta ɓukaci gwamnatin tarayya ta bi haƙƙin waɗanda su ka rasa rayukansu a wajen zanga-zangar tsadar rayuwa a sassan Nijeriya. Sakataren hulɗa da jama'a na Ƙasa a jam'iyyar, Femi Adeyeye ya faɗi hakan cikin wata takarda da ya fitar, inda ya ce sanarwar jawabin raina hankulan ƴan Nijeriya ne da su ka yi kwana uku su na fitowa zanga-zanga, ya na mai cewa ya kamata a gabatar da jawabin tun kafin wannan lokacin. Ya ce sauya taken Ƙasa bai ɗauki…
Read More

Zanga-zanga: An zargi na hannun daman Ganduje da iza wutar tashin-tashina a Kano

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata ƙungiyar kishin al'ummar jihar Kano mai suna 'Civil Liberty Organization', ta zargi ɗaya daga cikin na hannun daman Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, sannan sabon Darakta Janar na Cibiyar Bunƙasa Ƙasa, Baffa Babba Ɗan-Agundi, da ɗaukar nauyin wasu ɓata-gari da su ka haifar da tashin-tashina a jihar a ranar farko ta zanga-zangar tsadar rayuwa. Jaridar 'DAILY NIGERIAN' ta ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanya dokar hana fita a jihar bayan da wasu ɓata-gari su ka shiga sace-sace da salwantar da dukiyar al'umma da ta…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu zai yi jawabi kan zanga-zangar tsadar rayuwa gobe

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A gobe Lahadi ne Mai Girma Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi wa ƴan Nijeriya game da batun zanga-zangar tsadar rayuwa da ake yi a sassa daban-daban na faɗin ƙasar. Mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya faɗi hakan cikin wata takarda da ya fitar a ranar Asabar, ya na mai cewa Tinubu zai yi jawabin ne a ranar 4 ga watan Agusta da misalin ƙarfe 7 na safe. Ya yi kira ga gidajen jaridu kamar su telebijin da rediyo su kasance a shirye don ɗaukar jawabin kai-tsaye. Sannan za a sake maimaita…
Read More
Lamunin karatun gaba da sakandire ya je hannun ɗaliban Jami’o’i 6 a Nijeriya

Lamunin karatun gaba da sakandire ya je hannun ɗaliban Jami’o’i 6 a Nijeriya

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja A yanzu jami’o’in gwamnatin tarayya guda shida da ɗalibansu ne suka ci gajiyar kashin farko na lamuni daga asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya NELFUND. Jami'o'in sun haɗa da; Jami’ar Benin dake Jihar Edo; Jami'ar Ibadan dake Jihar Oyo, Jami'ar Bayero dake Jihar Kano da Jami'ar Ilorin dake Jihar Kwara. Ragowar sun haɗa da Jami’ar Maiduguri ta Jihar Borno da Jami’ar Tarayya da ke Dutsin-ma a Jihar Katsina. A halin yanzu an bada tallafin na kuɗi da ya kai Naira Biliyan Biyu da Miliyan Ashirin da shida da dubu ɗari da sittin…
Read More