Labarai

Boko Haram da ISWAP sun kashe mutane 109 cikin wata shida – Rahoto

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wani sabon rahoto da 'Nextier' ta fitar, ya ce aƙalla mutane 109 ne ayyukan ta'addanci ya yi sanadiyyar mutuwarsu a hare-hare 19 da mayaƙan Boko Haram da na ISWAP su ka kai a wurare mabanbanta a rabin farko na shekarar 2024. Rahoton ya ce, cibiyar kula da lamurran ta'addanci da ƙalubalen sansanin ƴan gudun hijira na Arewa-maso-Gabas ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta haɗe kai da maƙoftan ƙasashe domin inganta tsaro a kan iyakokin ƙasashen. Dakta Chukwuma Okoli na jami'ar Azikwa da ke Akwa a Nijeriya ya wallafa rahoton tare da haɗin-gwiwar Dakta Ndu Nwokolo…
Read More
Kushe ba zai hana ni goyon bayan Tinubu ba —Rarara

Kushe ba zai hana ni goyon bayan Tinubu ba —Rarara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shahararren mawaƙin siyasa, Dauda Kahutu Rarara, ya ce sukar da ake yi masa ba zai tilasta masa janye goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu ba. Rarara ya bayyana cewa ba zai juya wa shugaban ƙasar baya ba ne a yayin wata hira da aka yi da shi a kafar DLC Hausa. A kwanakin baya Facebook ya rufe shafin mawakin bayan masu goyon bayan zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Nijeriya sun kai ƙarar shafin nasa. Sai dai a yayin tattaunawar, Rarara ya ce goyon bayansa ga Tinubu ya samo asali ne daga irin ƙoƙarin…
Read More
Bagudu ya bayyana abinda Tinubu ya ke yi yayin da ake zanga-zanga

Bagudu ya bayyana abinda Tinubu ya ke yi yayin da ake zanga-zanga

Ministan kasafin kuɗi, Atiku Bagudu ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu yana bibiyar zanga-zangar da ke wakana a faɗin ƙasar yayin da shiga rana ta uku. 'Yan Nijeriya da dama ne ke nuna fushin su sabida tsada da kuma ƙuncin rayuwa da ake fama dashi wanda ya fara ne sanadiyar cire tallafin man fetur da shugaban yayi shekara ɗaya da ta wuce. Bagudu ya ce, Shugaba Tinubu na bibiyar al'amarin kuma zai ɗauki mataki na gaggawa domin ganin a samar da sauƙi ga 'yan Nijeriya. Zanga-zangar ta tafi lafiya a jihohi da dama a ranar farko, kafin kuma…
Read More

‘Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga da borkonon tsohuwa a Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Jami'an 'Yan sanda sun tarwatsa taron masu zanga-zanga a filin MKO Abiola da ke Abuja, bayan da su ka watsa mu su hayaƙi mai sanya ƙwalla. An samu raguwar adadin waɗanda su ka halarci zanga-zangar idan an kwatanta da ranakun Alhamis da Juma'a inda bayan da su ka taru a filin da su ka saba yi ne, sai jami'an su ka nemi tarwatsa su ta hanyar amfani da borkonon. Haka kuma, a ranar Juma'a ma an yi mu su irin haka a lokacin da su ka taru a Shataletalen Berger da ke cikin garin Abuja. Yayin…
Read More

Kaso 95 na masu zanga-zanga a Borno ƙananan yara ne – Gwamna Zulum

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya zargi cewa kashi 95 na waɗanda su ka yi zanga-zanga a ranar Alhamis a jihar ƴan ƙasa da shekaru 14 ne. Gwamnan ya faɗi haka ne a lokacin da ya ke gabatar wani jawabi na kai-tsaye a ranar Asabar a inda ya ɗage batun dokar hana fita. Ya ce, "abin mamaki ne ganin ɗan shekara shida ɗauke da allo wanda tabbas wani ne ya umarce shi. Mafi yawancin irin waɗannan yaran, ba ƴan Borno ba ne." Zulum ya ce akwai buƙatar duba lamarin dubban yaran da ke zama a…
Read More

Borno ta ɗage dokar hana fita, ta buƙaci al’umma su kiyaye doka

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin jihar Borno ta janye dokar hana fita a faɗi jihar wanda ta sanya sakamakon hargitsi da ake samu a yayin gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya. Hakan na zuwa ne bayan da aka samu sace-sace da ƙone-ƙone a wasu sassan ƙasar inda gwamnan jihar, Umar Babagana Zulum ya sanya dokar kulle na sa'o'i 24 don dakatar da aukuwar fitina a faɗin jihar. Zulum ya yi jawabin ne a wata hirar kai-tsaye da ya gabatar, ya na mai cewa hakan dama ce ga al'umma su fito su cigaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda aka…
Read More

Rundunar sojoji ta magantu game da zargin sata kan jami’anta a Kano lokacin zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar sojin Nijeriya ta ce sojoji ba su yi sata a ɗakin ajiya na Barakat ba, sai dai sun ƙwato ababan da ɓata-gari su ka sace da sunan zanga-zanga. Daraktan hulɗa da jama'a na rundunar, Manjo Janar Onyema Nwachukwu ya faɗi hakan la'akari da wani bidiyo da ke nuna cewa jami'an rundunar sun shiga sahun masu satar kayayyaki a ɗakin ajiyar a ranar Alhamis. Ya ce, akwai kuskuren fahimta game da fahimtar da jama'a su ka yi wa bidiyon, ya na mai cewa jami'an na runduna ta uku, an kira su ne don su kawo ɗauki…
Read More
Yadda ’yan bindiga suka karɓe iko a yankuna 102 na Zamfara

Yadda ’yan bindiga suka karɓe iko a yankuna 102 na Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD ’Yan bindiga sun mamaye yankuna 102 a Jihar Zamfara, inda suka daƙile ayyukan noma a gonaki da dama. Jihar Zamfara da aka santa da noma, sana’ar noma ta durƙushe a jihar sakamakon yawaitar ayyukan 'yan fashin daji da suka fara a shekarar 2009 zuwa 2012. Wannan tashin hankalin ya sa noma ya kusa gagara, musamman a yankunan karkara. Mazauna jihar, waɗanda sama da kashi 90 bisa 100 sun dogara ne kan noma, an tilasta musu yin watsi da gonakinsu. Fiye da kashi 70 na mazauna karkara sun yi gudun hijira zuwa birane domin gujewa hare-haren 'yan…
Read More
Rundunar Sojojin Nijeriya ta kori jami’an da suka tsere daga fagen daga a Borno

Rundunar Sojojin Nijeriya ta kori jami’an da suka tsere daga fagen daga a Borno

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar sojin Nijeriya ta sallami wasu sojoji shida daga aikinta bisa zarginsu da tserewa daga wani harin da ƙungiyar Boko Haram ta kai a garin Damboa na jihar Borno. Sojojin da ke aiki da rundunar Operation Lafiya Dole, an ce sun janye daga fagen daga ne bayan harsasan su sun ƙare a yaƙin da su ke yi da 'yan ta'adda. Sojojin da aka kora sune: PTE OLANIYI EMMANUEL (19NA/78/0690); PTE MASA’UDU ADAMU (20NA/79/3745); PTE ABDUL AZEE SALEH (22NA/82/5192); PTE MOHAMMED MOHAMMED (22NA/82/1721); PTE ADAH TOYE (22NA/82/1191); PTE HASSAN ABUBAKAR (22NA/82/1909). Wata majiyar sojin ta bayyana hukuncin…
Read More
Hukumar ’yan sanda ta sanar da fara horar da sabbin ƙananan jami’ai

Hukumar ’yan sanda ta sanar da fara horar da sabbin ƙananan jami’ai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD  A ƙarshe, Hukumar 'Yan Sanda ta sanar da fara horar da sabbin jami'an 'yan sanda da aka ɗauka aiki. Lamarin dai na zuwa ne biyo bayan wani zazzafar rikicin da ya ɓarke tsakanin hukumar da rundunar 'yan sandan Nijeriya dangane da jerin sunayen jami'an da suka samu gurbi. Taƙaddamar ta taso tsakanin hukumar PSC da rundunar NPF bayan da aka fitar da jerin sunayen mutane 10,000 da suka yi nasarar samun aikin ɗan sanda da kwararrun jami’an 'yan sandan Nijeriya a ranar 4 ga watan Yuni. Rundunar 'yan sandan dai ta yi watsi da jerin sunayen,…
Read More