Labarai

An maka CBN a kotu kan ɓatar tsabar kuɗi biliyan N100

An maka CBN a kotu kan ɓatar tsabar kuɗi biliyan N100

Daga MAHDI M. MUHAMMAD ƙungiyar SERAP ta maka Babban Bankin Nijeriya (CBN) ƙara a bisa zargin gaza yin bayanin inda sama da biliyan N100 na yagaggun kuɗi suka shige. SERAP ta ce, tana kuma ɗaukar matakin shari’a a kan CBN saboda biliyan N12 da aka ware wa ofisoshin babban bankin a Abeokuta, jihar Ogun, da kuma Dutse a jihar Jigawa. Mataimakin Darakta na ƙungiyar, Kolawole Oluwadare ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 28 ga Yuli, 2024. Idan dai ba a manta ba, SERAP a ranar Lahadi, 30 ga watan Yuni, ta bayar da…
Read More
’Yan sanda sun kashe shugaban ƙungiyar asiri da ya kashe DPO a Ribas

’Yan sanda sun kashe shugaban ƙungiyar asiri da ya kashe DPO a Ribas

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta ce gwamnan jihar, Siminalayi Fubara, ya cika alƙawarinsa na biyan la'adar Naira Miliyan 100 kan wani fitaccen shugaban ƙungiyar asiri, Gift Okpara, wanda ake kira 2Baba, wanda tare da 'yan ƙungiyarsa suka kashe wani jami’in 'yan sanda, Sufeto Bako Angbashin, a yankin Oduemude na jihar. Kwamishinan 'yan sandan jihar, Olatunji Disu, ya tabbatar da faruwar lamarin a yayin wani fareti da aka gudanar don karrama jami'in da aka kashe a hedikwatar ‘yan sandan jihar a ranar Asabar, inda ya ƙara da cewa an sako gawar ɗan sandan da aka kashe…
Read More
Matasa 11,000 aka ba takardar aiki a gwamnatin Abba – Sunusi Kwankwaso  

Matasa 11,000 aka ba takardar aiki a gwamnatin Abba – Sunusi Kwankwaso  

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano Hon. Sunusi Surajo Kwankwaso, Mai Ba Wa Gwamnan Jihar Kano Shawara Kan Harkokin Siyasa, ya bayana cewa, ko yanzu gwamnatin Abba ta biya bashin alƙawura da dama da ta ɗauka a lokacin gangamin yawon neman ƙuri'ar jama'ar Kano a jam'iyyar NNPP a wani jawabi da ya gabatar a birnin Kano a makon da ya gabata. Sunusi Kwankwaso, ya ƙara da cewa matasan da suka samu aiki suna da yawa a Kano waɗanda aƙalla matasa maza sama da 11,000 suka samu takardar aiki haka abin yake wajen bai wa mata da dama suka sun samu takardar…
Read More
Buhari ya cire tallafin fetur ba Tinubu ba – Gwamna Inuwa

Buhari ya cire tallafin fetur ba Tinubu ba – Gwamna Inuwa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Inuwa Yahaya na Jihar Gombe ya bayyana cewa babu wani laifi ko haƙ ƙ i da ke kan wuyan Shugaban ƙasa Bola Tinubu, saboda ya cire tallafin fetur. Da yake wa shugabannin ƙ ungiyoyin Jihar Gombe jawabi a ranar Talata a Gidan Gwamnati, Yahaya ya ce tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ne ya cire tallafin fetur, saboda babu kuɗin tallafin fetur a cikin kasafin Buhari na ƙarshe na 2023, wanda Tinubu ya taras a ranar 29 ga Mayu. Ya ce Tinubu ba shi da yadda zai yi sai dai ya cire tallafin kawai,…
Read More
Ɗa ya kashe mahaifinsa, ya binne gawar a Minna

Ɗa ya kashe mahaifinsa, ya binne gawar a Minna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani matashi ɗan shekara 29, Mizanmil Abubakar, ya kashe mahaifinsa, Abubakar Adawa, mai shekaru 65, bisa zargin masu kawo masa matsala a harkokinsa a unguwar Kpakungu da ke Minna, Jihar Neja. Wanda ake zargin, kamar yadda rahotanni suka bayyana, ya kuma daddatsa gawar mahaifin nasa gunduwa-gunduwa, ya tattara su a cikin buhun siminti sannan ya binne shi a wani rami mara zurfi a cikin gidan su. An gano cewa Abubakar Adawa mai shekaru 65 'yan uwansa ne suka kai rahoton ɓacewarsa a ofishin 'yan sanda na Kpakungu a ranar 30 ga Yuli, 2024. Jami’in hulɗa da…
Read More
Yunwa ce ta saka ni satar doya, inji wani mutum a kotu

Yunwa ce ta saka ni satar doya, inji wani mutum a kotu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Wani mutum mara aikin yi mai suna Cletus Gandu mai shekaru 40, a ranar Laraba ya bayyana cewa ya saci doya guda biyu ne saboda yana jin yunwa. Hukumar NSCDC, ta tuhumi Gandu da aikata laifuka da kuma sata. Gandu ya shaida wa Kotun Majistare da ke Kafanchan, Jihar Kaduna cewa, “Yunwa ta sa na saci doya sau biyu, inda ya roƙi afuwar kotu." Alƙalin kotun, Michael Bawa, ya ɗage yanke hukunci har zuwa ranar 6 ga watan Agusta, bayan da wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa. Bawa ya bayar da umarnin a tsare shi. Tun…
Read More
Aiwatar da kasafin kuɗi: Gwamnatin Kano ta kashe miliyan N596 wajen sayen kayan ma’aikatu

Aiwatar da kasafin kuɗi: Gwamnatin Kano ta kashe miliyan N596 wajen sayen kayan ma’aikatu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kashe Naira Miliyan 596 wajen samar da kayayyakin ofis da sauran ababen more rayuwa a ma’aikatun gwamnatin jihar a cikin zangon farko da na biyu na kasafin kuɗin shekarar 2024. Baya ga haka, gwamnati ta ba da umarnin sake sabunta kashi na biyu na ayyukan kasafin kuɗin jihar nan take. Da yake mayar da martani ga rahotannin da kafafen yaɗa labarai suka yaɗa kan yadda kasafin kuɗin jihar ke gudana, inda aka tanadi zunzurutun kuɗi Naira biliyan 10 da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kashe kan kayayyakin ofis, mai magana…
Read More
’Yan bindiga sun halaka mutum bakwai a Sakkwato

’Yan bindiga sun halaka mutum bakwai a Sakkwato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A wani ƙazamin hari da wasu ’yan bindiga suka kai ƙauyen Karfen Sarki da ke ƙaramar Hukumar Gudu a Jihar Sakkwato, sun kashe mutane bakwai ciki har da jami’an sabuwar rundunar tsaro da gwamnatin jihar ta kafa su biyar. Shugaban ƙaramar hukumar Gudu, Hon. Umar Maikano Balle, ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Talata. A cewar Balle, ’yan bindigar sun yi wa mutanen kwanton ɓauna, inda suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi. “Kwarai jami’an sabuwar rundunar tsaron yankin suna ƙoƙarin daƙile hare-haren ’yan bindiga na lokaci-lokaci har ya zuwa yanzu, wanda hakan ya…
Read More
Dalilin gwamnati na rashin sanar da cibiyoyin sayar da shinkafa – Minista Idris

Dalilin gwamnati na rashin sanar da cibiyoyin sayar da shinkafa – Minista Idris

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ta hana sanar da cibiyoyin sayar da shinkafar da za ta bayar domin gudun kada wasu masu hannu da shuni su kawo matsala a tsarin. Idris ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan rediyon Abuja a ranar Larabar da ta gabata, inda ya bayyana shirin sayar da buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 50 kan kuɗi Naira 40,000, wanda gwamnati ta keɓance da nufin rage wa 'yan ƙasa matsalar tattalin arziki. A ranar Litinin ɗin da…
Read More
Ya kashe mahaifinsa, ya binne shi a gidansu

Ya kashe mahaifinsa, ya binne shi a gidansu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Rundunar ’yan sandan Jihar Neja, ta kama wani matashi mai shekara 29 mai kan zargin kashe mahaifinsa mai shekara 65 a duniya. Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Waisu Abiodun ne, ya bayyana hakan a Minna a ranar Talata, inda ya ce an kai rahoton faruwar lamarin ofishin ’yan sanda da ke Kpakungu. Ya ce, “A ranar Talata da misalin ƙarfe 10 na safe ne aka samu labari a ofishin da ke Kpakungu cewa ranar Litinin wani Abubakar Adawa ya ɓace a unguwar Barkin-Sale a Minna.” Abiodun ya ce jami’an ’yan sandan da ke…
Read More