Labarai

Shugaban rundunar soji ta takwas, GOC ya buɗe makarantar firamare a Gusau

Shugaban rundunar soji ta takwas, GOC ya buɗe makarantar firamare a Gusau

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Shugaban Rundunar Sojojin Nijeriya, runduna ta 8 (GOC), Birgediya Janar Ibikule  Ajose, ya ƙaddamar da Makarantar Ƙananan Yara ta Kwamanda da ke Rundunar Sojojin Nijeriya a Gusau.  Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama'a na Sojoji, 1 Brigade Nigerian Army Laftanar Sulaiman Omale ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau ranar Talata. A yayin ƙaddamar da makarantar, Birgediya Janar Ajose ya yaba da kafa makarantar, inda ya bayyana ta a matsayin abin yabawa, inda ya ce shirin wani ci gaba ne ga al’umma.  “Ilimi na da matuƙar muhimmanci ga…
Read More
An kama malaman bogi a Jami’ar Bayero ta Kano

An kama malaman bogi a Jami’ar Bayero ta Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jami’an tsaro a jami’ar Bayero dake Kano sun kama wasu mutane guda biyu da suke kiran kansu a matsayin malaman jami’ar. An kama mutanen biyu suna siyar da litattafan karatu na bogi ga sabbin ɗaliban ajin farko. A cewar sanarwar da sakataren yaɗa labarai na jami’ar, Bala Abdullahi ya fitar ya ce waɗanda ake zargin sune: Daɓid Iluebe daga jihar Edo da Chike E. Eke daga jihar Delta. Sanarwar ta bayyana cewa mutanen guda biyu sun shiga ɗakin bada karatu a tsangayar ƙere-ƙere inda suka gabatar da kansu ga ɗaliban ajin farko na sashin kan…
Read More
Masu jin zafin faɗuwa zaɓen 2023 suka ɗauki nauyin shirya zanga-zanga – Akpabio

Masu jin zafin faɗuwa zaɓen 2023 suka ɗauki nauyin shirya zanga-zanga – Akpabio

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa waɗanda suka faɗi zaɓen 2023 ne suke ɗaukar nauyin shirya zanga-zangar da ake shirin yi daga ranar Alhamis, 1 zuwa 10 ga Agusta. “Haushin sun faɗi zaɓe ne ya sa suke ɗaukar nauyin shirya zanga-zanga, saboda a tunanin su za su iya tsallakowa ta katanga domin su hargitsa gwamnati,” inji Akpabio. Akpabio ya zargi ‘yan takarar da suka faɗi zaɓen shugaban ƙasa na 2023 cewa su ne ke ɗaukar nauyin shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar nan. Ya bayyana haka ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan…
Read More
Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti kan sabon mafi ƙarancin albashi

Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti kan sabon mafi ƙarancin albashi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kafa kwamitin bayar da shawara kan sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, wanda Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu. Gwamnatin ta kafa kwamitin ne sa’o’i 48 bayan amincewar shugaban ƙasa kan mafi ƙarancin albashin. Kano ita ce jiha ta farko a Nijeriya da ta kafa irin wannan kwamiti. A ranar Talata ne gwamnan ya ƙaddamar da kwamitin a fadar gwamnatin jihar ta hannun mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo. Cikin wata sanarwa da ya fitar, Ibrahim Garba Shuaibu, mai magana da yawun mataimakin gwamnan, ya bayyana…
Read More
Yadda ‘yan bindiga suka sace Sarkin Gobir, ɗansa da ƙaninsa

Yadda ‘yan bindiga suka sace Sarkin Gobir, ɗansa da ƙaninsa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gungun ‘yan bindiga sun arce da Sarkin Gobir, Isa Muhammad Bawa, wato Hakimin Gatawa da ke cikin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a Jihar Sakkwato. An yi garkuwa da shi tare da ɗan sa da kuma ƙaninsa, kamar yadda Kantoman Ƙaramar Hukumar Sabon Birni, Garba Umar Kaba ya shaida wa Daily Trust cewa an yi garkuwa da su a ranar Asabar kusa da Kwanar Maharba, daidai lokacin da suke komawa gida daga Sokoto. Kada ya ce, “Ban san daidai lokacin da abin ya faru ba, amma dai bayanan da jami’an tsaro suka yi mana na…
Read More
Yakamata al’ummar Arewa su haɗa kai don samun mafita daga halin da ƙasar ke ciki – Ɗanpass

Yakamata al’ummar Arewa su haɗa kai don samun mafita daga halin da ƙasar ke ciki – Ɗanpass

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An yi kira ga al'ummar Arewa musamman Hausa/Fulani su haɗa kai a yi aiki tare domin cimma manufofi da za su bunƙasa kima da ci gaba da za a samu kyakkyawan makomar fita daga mawuyacin halin da ƙasar nan take ciki. Ya ce idan aka duba yawanci abokan haɗakarmu na ƙasar nan ƙabilu daban-daban kansu a haɗe yake amma Hausa/Fulani mu ba abinda yake a gabanmu sai biyan buƙatar son rai idan bamu sami haɗin kai ba ba za mu cimma ga ci ba. Alhaji Gambo Muhammad Ɗanpass don haka a sa tsoron Allah a…
Read More
Yadda sojoji da ‘yan banga suka kashe ‘yan bindiga sama da 100 a jihar Neja

Yadda sojoji da ‘yan banga suka kashe ‘yan bindiga sama da 100 a jihar Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Dakarun rundunar sojin Nijeriya tare da hadin gwiwar ‘yan banga sun kashe ‘yan bindiga sama da 100 a kauyen Kundu dake karamar hukumar Wushishi a jihar Neja. Dakarun sun yi arangama da maharan ranar Laraba da safe. Jami’an tsaron sun samu wannan nasara bayan sun yi wa maharan zobe yayin da za su tsallaka zuwa Kontagora ta hanyar Akere dake Kundu. Wani majiya daga Kundu ya bayyana wa Daily Post cewa sun samu labarin zuwa maharan akan baburan amma sai daga baya sun samu labarin maharan sun ajiye baburan su suna takowa a kasa.…
Read More
’Yan bindiga 31 sun shiga hannu a Nasarawa

’Yan bindiga 31 sun shiga hannu a Nasarawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar ’Yan Sandan Jihar Nasarawa ta kama wasu mutum 11 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne da suka addabi mazauna ƙauyen Nunku da ke ƙaramar hukumar Akwanga, Masaƙa da kuma ƙaramar hukumar Karu da sauran ƙananan hukumomin jihar. Rundunar ta kuma kama wasu mutum 13 da laifin aikata fashi da makami a ƙaramar hukumar Karu. Kwamishinan ’yan sandan jihar, Mista Shehu Umar-Nadada, yayin da yake gabatar da waɗanda ake zargin a garin Lafiya, ya ce an kama ɗaya daga cikin waɗanda da ake nema ruwa a jallo a kan satar mutane a…
Read More
Jihar Yobe ta samu nasarar bunƙasa harkokin addini da rayuwar almajirai ƙarƙashin hukumar  AISEB

Jihar Yobe ta samu nasarar bunƙasa harkokin addini da rayuwar almajirai ƙarƙashin hukumar  AISEB

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano  Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Mai Mala Buni ta zo da kyakkyawan tsari na kyautata makomar yara da  ake samu suna  yawace-yawace akan manyan hanyoyi a jihar ta gina su akan neman ilimi da bunƙasa rayuwarsu. Wannan nasara an same tane bisa irin ƙwazo da himma na Babban sakataren Hukumar kula da ilimin Arabiyya da harkokin addini ta jihar Yobe (AISEB), Malam Umar Abubakar. Babban sakataren da ya samu kyakkyawar shaida na cewa tun naɗa shi daga tun 9 -10-2023 ya  gudanar da ayyukan ci gaba da dama da a yanzu ake alfahari da su…
Read More
 Ba a ba mu abincin tallafi ba —Gwamnatin Adamawa

 Ba a ba mu abincin tallafi ba —Gwamnatin Adamawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Adamawa ta musanta karbar tireloli 20 na abincin tallafi daga Gwamnatin Tarayya. Ta bayyana cewa duk da haka, maimako zaman jira, ta ɗauki matakin raba nata kayan tallafin domin rage wa al’ummar jihar halin da suke ciki na matsin rayuwa. Kwamishinan yaɗa labaran jihar, Iliya James, ranar 29 ga watan Yuni, ya sanar cewa, gwamnatin jihar ta karɓi kasonta na takin zamani da Gwamnatin Tarayya ta bayar domin raba wa al’umma. A cewarsa, gwamnatin jihar a shirye take domin inganta walwalar jama’a, duk da ƙalubalen da ake fuskanta ƙasar. Sai dai ya…
Read More