Masu jin zafin faɗuwa zaɓen 2023 suka ɗauki nauyin shirya zanga-zanga – Akpabio

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa waɗanda suka faɗi zaɓen 2023 ne suke ɗaukar nauyin shirya zanga-zangar da ake shirin yi daga ranar Alhamis, 1 zuwa 10 ga Agusta.

“Haushin sun faɗi zaɓe ne ya sa suke ɗaukar nauyin shirya zanga-zanga, saboda a tunanin su za su iya tsallakowa ta katanga domin su hargitsa gwamnati,” inji Akpabio.

Akpabio ya zargi ‘yan takarar da suka faɗi zaɓen shugaban ƙasa na 2023 cewa su ne ke ɗaukar nauyin shirya zanga-zanga a faɗin ƙasar nan.

Ya bayyana haka ranar Litinin a Fadar Shugaban Ƙasa, bayan ya halarci zaman da Shugaba Bola Tinubu ya yi, inda ya sa hannu kan amincewa da mafi ƙanƙantar albashi ya kasance Naira 70,000.

Waɗanda suka yi takara tare da Tinubu a zaɓen 2023, sun haɗa har da Atiku Abubakar na PDP, Peter Obi na LP, Omoyele na AAC da sauransu.

Akpabio ya ja kunnen masu zanga-zanga su guji sata, kwasa, jida ko lalata kayan jama’a.

“Duk kayan da aka lalata to sai Nijeriya ta kashe maƙudan kuɗaɗe wajen maida kamar su. To kuma ba mu da kuɗaɗen. Ya kamata mu yi amfani da kuɗaɗen domin bunƙasa tattalin arziki da inganta rayuwar jama’a.”

Ya yi zargin cewa wasu ɓatagari na shirin yin amfani da zanga-zanga domin su saci kayan jama’a, kuma su aikata manyan laifuka yayin zanga-zanga.

Manhaja ta buga labarin cewa hasalallun matasa sun ɓarke da zanga-zanga tun a ranar Litinin, inda suka datse babban titin da ya tashi daga Abuja zuwa Kaduna.

By ukarofi