Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Jami’an tsaro a jami’ar Bayero dake Kano sun kama wasu mutane guda biyu da suke kiran kansu a matsayin malaman jami’ar.
An kama mutanen biyu suna siyar da litattafan karatu na bogi ga sabbin ɗaliban ajin farko.
A cewar sanarwar da sakataren yaɗa labarai na jami’ar, Bala Abdullahi ya fitar ya ce waɗanda ake zargin sune: Daɓid Iluebe daga jihar Edo da Chike E. Eke daga jihar Delta.
Sanarwar ta bayyana cewa mutanen guda biyu sun shiga ɗakin bada karatu a tsangayar ƙere-ƙere inda suka gabatar da kansu ga ɗaliban ajin farko na sashin kan cewa su malamai ne.
Sanarwar ta ce mutanen sun bayyanawa ɗaliban cewa siyan litattafan ya zama dole ga duk wanda yake son tsallake darasin.
Sai dai jami’an tsaron jami’ar sun samu nasarar kama mutanen waɗanda suka amsa laifinsu.
Jami’ar ta ce za a miƙa waɗanda ake zargin ga ‘yan sanda domin ɗaukar matakan da suka dace inda ta ƙara da cewa “za mu ƙara wayar da kan ɗaliban mu kan wannan abu mara daɗi da ya faru”.
