Labarai

Ɗangote da BUA za su gurfana a majalisa kan badaƙalar haraji

Ɗangote da BUA za su gurfana a majalisa kan badaƙalar haraji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Majalisar Wakilai ta umarci kamfanonin BUA da Dangote su bayyana a gabanta don amsa tambayoyi kan zirarewar kudaden harajin Gwamnatin Tarayya. Kamfanonin simintin BUA da Dangote na cikin jerin kamfanoni masu zaman kansu da cibiyoyin Gwamnatin Tarayya 113 da za su amsa tambayoyi kan wannan lamari. Shugaban kwamitin binciken kudaden jama’a na majalisar, Bamidele Salam, ya sanar cewa shugabannin kamfanonin ko manyan akantocinsu ne za su hallara domin amsa tambayoyin. Bamidele Salam ya ce binciken zai mayar da hankali ne kan rashin biyan kudaden haraji ga gwamnati, rashin bin ka’idojin da doka ta shimfida…
Read More
‘Yan bindiga sun harbe manomi, sun yi awon gaba da iyalansa a Kaduna

‘Yan bindiga sun harbe manomi, sun yi awon gaba da iyalansa a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu ’yan bindiga sun harbe wani manomi tare da yin awon gaba da matansa biyu lokacin da suke dawowa daga gona a unguwar Maraban Jibo a ƙaramar hukumar Kachia a Jihar Kaduna. Wani mazaunin garin, Magaji Ibrahim, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin ƙarfe 6 na yamma. Wani shugaban jama’a a yankin ya tabbatar da faruwa harin. Ya ce ’yan bindigar sun kusa kashe mutumin amma sai suka gano cewa jini na fita daga ƙafarsa, sai suka ƙyale shi suka tafi da matansa. Ya ce an tattara ’yan banga…
Read More
Zanga-zanga ka iya haifar da yunwar da ba a taɓa fuskanta ba Nijeriya – MURIC

Zanga-zanga ka iya haifar da yunwar da ba a taɓa fuskanta ba Nijeriya – MURIC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Kare Muradun Musulman Nijeriya (MURIC), ta gargaɗi masu shirya zanga-zanga cewa zanga-zangar fushin fama da yunwar da suke shirin tsunduma za ta iya haifar da gagarimar yunwar da ba a taɓa fuskanta ba. Ƙungiyar ta ja hankalin matasa cewa su bi a hankali, su yi haƙuri, sannan kuma su amince a zauna teburin sulhu. Wannan matsayi da MURIC ta ɗauka ta fitar da shi ne a ranar Talata, daga bakin Babban Daraktan Ishaƙ Akintola. “Matasan Nijeriya waɗanda manyan ‘yan adawa ke ɗaukar nauyi sun shirya fita zanga-zangar nuna fushin tsadar abinci da yunwa,…
Read More
Shettima ya wakilci Tinubu a buɗe taron tattaunawa kan Afrika

Shettima ya wakilci Tinubu a buɗe taron tattaunawa kan Afrika

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima a yau ya buɗe taron tattaunawa na shekarar 2024 a tsakanin masu ruwa da tsaki kan Nahiyar Afrika dangane da tattalin arziƙi. Taron wanda aka buɗe shi yau a Otel ɗin (Transcorp Hilton), Abuja, cikin jawabin da ya gabatar ya bayyana tsare-tsare da matakan da gwamnati take ɗauka wajen hana karyewar tattalin arziƙin ƙasar a duniya. Ya kuma yi kira kan samar da haɗin kai a duniya a tsakanin ƙasashen Afrika domin magance dukkan wani ƙalubalen tattalin arziƙi da kowace ƙasa take fuskanta tare da ribatar damammaki na…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Sarki Sanusi ya magantu bayan dawowar zanga-zanga a Kano

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga al'umma da kar su bari a yi amfani da su wajen kawo hargitsi a Kano da Arewa da ma a Nijeriya baki ɗaya. Sarki Sanusi ya yi jawabin ne bayan da aka sake dawo da gudanar da zanga-zangar duk da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya saboda tashin-tashina da aka samu a ranar Alhamis. Ƴan zanga-zangar sun sake taruwa a Tudun-Wada da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa tare da cigaba da yin zanga-zangar duk da dokar kulle na sa'o'i 24 da gwamnan jihar,…
Read More

Zanga-zanga: An sanya dokar hana fita a Jigawa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya saka dokar hana fita na tsawon sa'o'i 24 a faɗin jihar sakamakon tashin-tashina da aka samu a rana ta farko na zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya. Gwamnan ya ce, ba a so faruwar hakan ba inda daga baya aka ɗage dokar don al'umma su gabatar da sallar juma'a. Namadi ya ce, "yayin da aka samu zanga-zangar lumana ta sauya zuwa tarzoma ta hanyar lalatawa da satar dukiyar al'umma da ta Ƙasa, ba za mu amince wa hakan ba don baya cikin al'adarmu, saboda haka ba za mu lamunta ba." Ya…
Read More

Soji ba za su bari Nijeriya ta shiga tsaka-mai-wuya ba – gargaɗin Janar Christopher ga ƴan zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban ma'aikatan Tsaro (CDS), Janar Christopher Musa ya gargaɗi masu ƙoƙarin tada tarzoma a zanga-zangar tsadar rayuwa da ake cigaba da yi a Nijeriya, ya na mai cewa ko su janye daga yunƙurinsu ko kuma doka ta yi aiki a kan su. Janar Christopher ya faɗi hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja game da batun zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya. Ya ce, hukumomin tsaro musamman ƴan sanda su na ƙoƙari wajen ji da lamuran tashin-tashina a zanga-zangar, ya na mai kira ga al'ummar Nijeriya da su fahimci halin da…
Read More

Mutane da dama sun raunata yayin da ƴan sanda suka tarwatsa masu zanga-zanga a Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI An samu mutane da dama da su ka samu raunuka a lokacin da jami'an ƴan sanda su ka tarwatsa taron ƴan zanga-zanga a birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a. Hakan na zuwa ne sakamakon watsi da gargaɗin da rundunar ƴan sandan ta yi mu su na hana su gangami da sunan zagayen tsadar rayuwa da ake ciki a birnin Abuja koma bayan inda kotu ta keɓanci mu su. . Wani shaida ya ce, ƴan sanda sun tarfa masu zanga-zangar ne jim kaɗan bayan sun wuce ta yankin asibitin Ƙasa inda jami'an su ka yi amfani da…
Read More

Yanzu-yanzu: Ɗan sanda ya kashe abokin aikinsa bisa kuskure yayin harin ƴan zanga-zanga a Katsina

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wani abin tausayi a jihar Katsina ya auku yayin da jami'an Ƴan sanda su ka harbe abokin aikinsu bisa kuskure a lokacin da su ke ƙoƙarin tarwatsa an zanga-zanga. Lamarin ya auku ne a ranar Juma'a inda shaidu su ka bayyana cewa ana gudanar da zanga-zangar cikin lumana kafin jami'ai su shiga cikin inda bayan haka ne aka samu hargitsi sakamakon harbe-harbe da ƴan sandan su ka fara yi. Sakamakon ƙunci da al'umma a jihar ke ciki sanadiyyar tsadar rayuwa da rashin tsaro, ya sa mutane su ka yi dandazo don nuna damuwarsu game da halin…
Read More

Gwamnan Kano ya ɗora laifin caɓewar zanga-zanga kan magoya bayan Aminu Ado Bayero da APC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, ya ce tashin-tashina da aka samu a zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar, aiki ne na wasu ɓata-gari da ke biyayya ga saukakken Sarki, Aminu Ado Bayero da kuma ƴan daba da jam'iyyar APC ta ɗauki nauyinsu. Wasu matasa ɗauke da makamai sun kutsa Fadar gwamnatin jihar inda su ka yi ta ƙone-ƙone a farfajiyarta. Abba ya ce, dubban ƴan zanga-zangar lumana ne su ka taru a wajen Fadar don su miƙa saƙon kokensu, inda daga baya ta sauya zani zuwa tarzoma. Gwamnan ya ce, a lokacin da jami'ai su…
Read More