Labarai

Haraji: Kamfanin lantarki na Kaduna ya yanke wutar gidan gwamna a matsayin martani

Haraji: Kamfanin lantarki na Kaduna ya yanke wutar gidan gwamna a matsayin martani

Kamfanin lantarki na Kaduna ya yanke wutar gidan gwamnatin Jihar Kaduna. Hakan ya faru ne bayan rufe ofishin Lantarkin da hukumar haraji ta yi a safiyar Juma’a saboda bashin miliyan 600. Domin mayar da martani, kamfanin ya yanke wutar lantarkin gidan gwamnatin suma saboda bashin biliyan 2.9. Mai magana da yawun kamfanin, Abdulazeez Salisu ya bayyana kamfanin yayi iya bakin ƙoƙarin shi domin ganin gwamnatin ta yi abunda ya dace kafin a basu gargaɗin yanke wutar tun 21 ga watan Yuli sai sai abun yaci tura.
Read More
Tsohon minista Dalung ya jagoranci zanga-zanga a Jos

Tsohon minista Dalung ya jagoranci zanga-zanga a Jos

Tsohon minista a gwamnatin da ta shuɗe, Solomon Dalung ya jagoranci zanga-zanga a birnin Jos. Masu zanga-zangar wanda mafi yawan su matasa ne, sun yi tattaki inda suke waƙoki suna daga abun rubutu da ke nuni da buƙatar su. Yayin da yake magana, Dalung yace wannan zanga-zanga ba don komai ake yin ta ba sai don a samu shugabanci nagari da kuma neman gwamnati ta sassauta matsin rayuwa da ake fama dashi. Bayan shi, wasu da dama daga ƙungiyoyin sa kai sun yi magana inda su ma suka buƙaci shugaba Tinubu da ya dage ya yi wani abu a kan…
Read More
Sanata Kingibe ta musanta zargin ɗaukar nauyin zanga-zanga

Sanata Kingibe ta musanta zargin ɗaukar nauyin zanga-zanga

Sanatar da ke wakiltar birnin tarayya ta musanta zargin da ake mata na ɗaukar nauyin zanga-zanga. Idan ba mu manta ba, Blueprint ta rawaito ministan babban birnin tarayya ya na zargin cewa sanatar ta na ɗaukar nauyin zanga-zanga duk da bai fito fili ya kama suna ba. Sai dai a wani martani da Sanata Kingibe ta fitar ta faifan bidiyo, ta yi tir da Allah wadai da wannan zargin, inda tace abokan hamayyar ta na siyasa ke yaɗa wannan ƙaryar domin a ɓata mata suna. Kuma tace, ba za ta zauna ta ninke hannu yayin da ake ɓata mata suna…
Read More
DSS sun kama jagoran zanga-zangar tsadar rayuwa a Katsina

DSS sun kama jagoran zanga-zangar tsadar rayuwa a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jami'an DSS a Katsina sun kama ɗan gwagwarmaya Kabir Shehu 'Yanɗaki, wanda shine sakataren gamayyar ƙungiyoyin farar hula ta ƙasa.Shi wannan ɗan gwagwarmaya shi ya jagoranci zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gudanar a Jihar Katsina ranar Alhamis.Babu wani cikakken bayani daga hukumar tsaron game da kamen nashi.Sai dai ba zai rasa nasaba da irin yadda masu zanga-zangar suka lalata kayayyakin gwamnati da ɓalle shagunan mutane suka yi ta wasoso ba.A halin yanzu dai al'amura sun fara dawowa yadda suke, domin 'yan kasuwa sun fara buɗe shagunansu a hankali, ga zirga-zirgar ababen hawa ba fargaba. Faɗin jihar…
Read More

Zanga-zanga: APC ta yaba wa Sanata Yari da Matawalle kan sanya baki a Zamfara

Daga Sanusi Muhammad a Gusau Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara, ta yaba wa Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar da Ƙaramin Ministan Tsaro, Hon. Bello Muhammad Matawalle bisa jajircewa da su ka yi wajen ganin babu wani ɗan Jam’iyyar da ya shiga zanga-zangar da aka gudanar a ranar Alhamis a jihar. Sakataren yaɗa Labarai na jihar, Yusuf Idris tare da ɗaukacin shugabannin jam’iyyar na jihar su ka bayyana hakan a wani taron manema labarai da su ka gudanar a babban masauƙin baƙi mallakar rundunar soji (Command Guest Inn) da ke Gusau a ranar Juma’a. Sun bayyana ƙoƙarin da Sanata Yari da Matawalle…
Read More

An tura shugaban mulkin soji zaman shekaru 20 a gidan yari a Guinea

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata kotu a ƙasar Guinea ta yanke wa tsohon shugaban ƙasa na mulkin soji, Moussa Dadis Camara zaman gidan yari na tsawon shekaru 20 kan ta'addanci ga al'umma a ƙasar. An yi masa hukuncin ne sakamakon jagorantar ɗaya daga cikin kashe-kashe mafi muni a tarihin ƙasar wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 156 a lokacin da jami'an soji su ka buɗe wa jama'a wuta a wani gangamin neman kawo ƙarshen mulkin soji a shekarar 2009. Camara ya karɓi ragamar shugabancin ƙasar ne bayan wani juyin mulki a shekarar 2008 a lokacin da shugaba Lansana Conte ya…
Read More

Ƴar aiki ta yi iƙirarin ita ta kashe ƴar alƙali, inji majiyar ƴan sandan Legas

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata ɗaya daga cikin ƴan aikin Aribemchukwu, wacce aka yanka ta har lahira, ta yi iƙirarin ta na hannu waje kisan uwar gidanta, kamar yadda ƴan sanda su ka bayyana a ranar Alhamis. Aribemchukwu, wacce ƴa ce ga Alƙali Rita Ofili-Ajumogobia, an kashe ta ne a gidanta da ke Rukunin gidajen Parkview a yankin Ikoyi na Jihar Legas. Wata majiya ta ce an kashe ta ne a ranar Talata yayin da aka tsinci gawarta a ƙofar gidanta a safiyar ranar Laraba. An kama mutane uku da ke mata aiki da su ka haɗa da; mai aikin…
Read More
Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah wadai da kashe masu zanga-zanga

Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah wadai da kashe masu zanga-zanga

Ƙungiyar Amnesty International tayi Allah wadai da kisan masu zanga-zanga 13 a faɗin Nijeriya. Shugaban ƙungiyar Isa Sanusi ne ya faɗi haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya na mai umartar gwamnatin Nijeriya ta gudanar da bincike domin gurfanar da waɗanda suk aikata wannan laifin. Ƙungiyar ta ce, waɗanda aka kashe sun fito daga sashe daban daban na ƙasar nan, mutum shida a Suleja da ke Jihar Neja, huɗu a Maiduguri da kuma mutum uku a Kaduna. Ƙungiyar ta cigaba da cewa, binciken su, ya nuna cewa jami'an tsaro a wannan wurare sun buɗe ma masu zanga-zanga…
Read More

Atiku ya buƙaci a bai wa ƴan zanga-zanga goyon baya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon Mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, Alhaji Atiku Abubakar ya yaba wa ƴan zanga-zangar da ke ƙalubalantar matsin rayuwa da ake fama da shi a Nijeriya. Yayin da ya ke jinjina wa ƙoƙarin nasu, Atiku ya kuma yi alla-wadai da ɓata-gari da su ka sauya zanga-zangar a wasu jihohin zuwa tarzoma. Ya kuma yi kira ga jami'an tsaro kan irin yadda su ke gudanar da ayyukansu da kuma kaurace wa cin mutuncin ƴan jarida ko kuma hantararsu. Har'ilayau, Atiku ya yi kira ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya…
Read More