02
Aug
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Dawowar harkoki yadda aka saba na cigaba da wakana a jihohin Sakkwato, Taraba, Adamawa da Kebbi yayin da ake cigaba da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya. Sai dai, a jihohin Legas da Fatakwal a Ribas da Benin a Edo, ana cigaba da gudanar da zanga-zangar kamar yadda aka faro ta a jiya. A jihar Legas, ƴan zanga-zangar sun taru a Ojota inda jami'an tsaro su ka tsaya wajen basu kariya yayin da Kwamishinan Labarai, Gbenga Omotosho ya gabatar mu su da jawabi tare da yi mu su alkawarin cewa gwamnati za ta ɗauki matakin gyara…
