Labarai

Farfesa Sa’adatu Liman tana kawo ci gaba a babbar Jami’ar Nasarawa, cewar Farfesa Maikano

Farfesa Sa’adatu Liman tana kawo ci gaba a babbar Jami’ar Nasarawa, cewar Farfesa Maikano

Daga JOHN D WADA a Lafiya  An yaba wa sabuwar shugabar babbar Jami'ar Jihar Jihar Nasarawa dake garin Keffi a jihar Nasarawa, Farfesa Sa’adatu Hassan Liman dangane da ci gaba da ta kawo jami’ar a yanzu cikin lokuta ƙalilan da ta yi a muƙamin sabuwar shugabar babban jami’ar ta gwamnatin jihar. A lokacin wani zantawa na musamman ne da wakilinmu ya yi da Farfesa Maikano Ari wanda a yanzu haka shine shugaban fannin karatu na gaba wato Post Graduate Studies a Turance na babbae jami’ar ne ya bayyana haka a ofishinsa dake jami’ar ranar Laraba 31 ga watan Yulin shekarar…
Read More
Command Science Secondary School Boys, Jega ta karrama gwamnan Kebbi

Command Science Secondary School Boys, Jega ta karrama gwamnan Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Birnin Kebbi  Hukumar makarantar yaran sojoji maza da ke garin Jega a Jihar Kebbi ta karrama maigirma gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris.  An gudanar da bikin karramawar ne ranar asabar a lokacin da makarantar take gudanar da bikin yaye ɗalibai makarantar. Hukumar makarantar ta bayyana cewa ta bai wa Maigirma Gwamna wannan karramawar ne bisa gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban makarantar da kuma ilmi bakiɗaya. Shugaban Ma'aikatan Jihar Kebbi Alhaji Safiyanu Garba Bena ne ya wakilci Maigirma Gwamna Dakta Nasir Idris a wurin taron bikin yaye ɗaliban. Ya bayyana jin daɗinsa bisa ga…
Read More
Yadda aka gudanar da taron ranar ‘Yaumul Ƙur’an’ da Marigayi Khalifa Isyaku Rabiu ya assasa

Yadda aka gudanar da taron ranar ‘Yaumul Ƙur’an’ da Marigayi Khalifa Isyaku Rabiu ya assasa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An gudanar da taron 'Yaumul Ƙur’an' na bana a masallacin Juma’a na gidan Khalifa Isyaka Rabiu wanda ya samu halartar alarammoni da dama daga ciki da wajen jihar Kano. Taron da ake gudanar da shi duk shekara Marigayi Khalifa Sheikh Isyaka Rabiu ne ya assasa shekaru da yawa kamar yadda ɗaya daga cikin masu shirya taron Alhaji Auwalu Isyaka Rabiu ya shaida wa manema labarai.. Ya ce ba zai iya sanin takamaimai lokacin da aka soma gudanar da taron na 'Yaumul Ƙur’an' ba tun suna yara ake tara bayin Allah su karanta Alƙur’ani domin yi…
Read More
Yadda bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 19 a teburin mai shayi a Borno

Yadda bom ɗin Boko Haram ya kashe mutane 19 a teburin mai shayi a Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mutane aƙalla 19 ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin bom ɗin Ƙungiyar Boko Haram a teburin wani mai shayi a Jihar Borno. A daren Laraba ne mayaƙan ƙungiyar suka tayar da bom ɗin a teburin mai shayin da jama’a ke hira a garin Kawuri da ke Ƙaramar Hukumar Konduga. Wani jami’in gwamnatin jihar ya ce mutane da dama sun samu raunuka a sakamakon tashin bom ɗin da misalin ƙarfe 8.05 na dare. Jami’in gwamnatin ya ce, hatta waɗanda abin ya rutsa da su ba za su iya faɗin haƙiƙanin yadda abin ya auku…
Read More

Yadda ƴan zanga-zanga su ka mamaye gidan Buhari a Katsina

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da zanga-zangar tsadar rayuwa ke cigaba da cabewa a faɗin Nijeriya, a na zaman ɗar-ɗar sakamakon tururuwa da masu zanga-zangar su ka yi a gidan tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari da ke Daura da jihar Katsina. Hakan na zuwa ne bayan da zanga-zangar ta sauya salo zuwa tashin tashin-tashina a sassa daban-daban na faɗin ƙasar wanda hakan ya sanya jihohi uku su ka sanya dokar hana fita. An ga wata ɗaukar bidiyo dake nuna ƴan zanga-zangar maƙil a gidan Buhari inda wasu ke ƙoƙarin kutsawa cikin gidan yayin da wasu kuma ke ihun "Bama yi!…
Read More
Zanga-zanga: APC a Zamfara ta zargi PDP da ɗaukar nauyin kai hari gidan Matawalle

Zanga-zanga: APC a Zamfara ta zargi PDP da ɗaukar nauyin kai hari gidan Matawalle

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Jam’iyyar All Progressives Congress APC reshen Jihar Zamfara ta zargi jam’iyyar PDP da ɗaukar nauyin ‘yan bangar siyasa da suka kai hari gidan tsohon gwamna kuma ƙaramin ministan tsaro Hon. Bello Muhammed Matawalle da ke Gusau yayin zanga-zangar da aka gudanar a faɗin kasar nan a yau. Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran jam’iyyar na jihar, Yusuf Idris. "Jam'iyyar All Progressives Congress APC reshen Jihar Zamfara ta damu da yadda zanga-zangar lumana taso ta sauya sabon salon kai farmaki ga wasu jigajigan…
Read More

Ɓata-gari sun sauya zanga-zangar Kano zuwa sata a shaguna da ofisoshi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake cigaba da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya, wasu ɓata-gari a jihar Kano sun sauya ta zuwa tarzoma inda su ka fara fasa shaguna da ofisoshi su na kwashe dukiya da wasu kadarorin gwamnati. Waɗanda ke satar an gan su ɗauke da kayayyaki da suka haɗa da; kujeru da na'urorin comfuta da wasu abubuwa. Ganin haka ya sa gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sanya dokar hana fita ta tsawon awanni 24 a faɗin jihar.
Read More

Yobe ta sanya dokar ta ɓaci sakamakon ƙwace jagorancin zanga-zanga da ɓata-gari su ka yi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A cigaba da gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya, aƙalla manyan motoci ƙirar 'Bus' guda bakwai ne aka ƙona a Ƙaramar Hukumar Potiskum da ke jihar Yobe. An ƙona motocin ne a sakatariyar Ƙaramar Hukumar a ranar Alhamis. Wani shaida ya ce wasu mutane da su ka yi dandazo sun yi ƙoƙarin haddasa rikici a wajen yayin da jami'an tsaro su ka gaggauta dakatar da su. Jami'in hulɗa da jama'a na 'Yan sandan jihar, Dungus Abdulkarim ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya na mai cewa za a hukunta waɗanda ke da hannu a ciki.…
Read More
Da ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Jihar Kano ta garƙame gari zuwa awanni 24

Da ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Jihar Kano ta garƙame gari zuwa awanni 24

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta sanya dokar hana fita zuwa awanni 24. Gwamna Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana haka a yanzu lokacin da ya ke ma manema labarai ƙarin bayani. Gwamna ya bayanna cewa ɗaukar wannan doka na da nasaba da yunƙurin da ake yi na cigaba da tashe-tashen hankula dake gudana da sunan zanga-zangar lumana da ake gudanarwa a faɗin Ƙasar nan baki ɗaya. Gwamnan ya kuma buƙaci jami'an tsaro da su ƙara ƙwazo wajen aiwatar da aikin su dan kare al'umma da dukiyoyin su.
Read More

Yanzu-yanzu: Yadda ƴan zanga-zanga su ka rufe mashigar Fadar Gwamnatin Kano

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Jami'an tsaro sun tarwatsa ƴan zanga-zanga bayan da su ka riƙa ƙona tayoyi da wasu abubuwa a wajen Fadar gwamnatin Jihar Kano. Ƴan zanga-zangar sun taru ne daga sassa daban-daban na Jihar a inda su ke jira gwamna Abba Kabir Yusuf ya gabatar mu su da jawabi. Yayin haka ne su ka mayar da taron ya koma hayaniya inda ƴan sanda da sauran jami'an hukumomi su ka ɗauki matakan da su ka dace game da al'amarin.
Read More