Labarai

Kiristoci sun ba Musulmai kariya wajen zanga-zanga yayin da suke sallar Azahar

Kiristoci sun ba Musulmai kariya wajen zanga-zanga yayin da suke sallar Azahar

A wani abun farin ciki da ya faru yayin zanga-zanga a Jos, shine kiristoci sun ba Musulmai kariya yayin da suke sallar Azahar a filin zanga-zanga. Wannan na zuwa ne a lokacin da rikicin addini yayi ƙamari a jihar amma da irin wannan haɗin kan, za a iya cewa lallai matasa sun fara gane abunda ke masu ciwo kuma za su kawo cigaba nan gaba mai ɗorewa. Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa, wannan abun da ya faru ya nuna cewa, kiristoci da Musulmai kan su haɗe yake, wasu ɓatagari ne ko a can baya ke son raba…
Read More
Gwamnatin Jihar Borno ta sanya dokar hana zirga-zirga

Gwamnatin Jihar Borno ta sanya dokar hana zirga-zirga

Gwamnatin Jihar Borno ta sanya dokar hana zirga-zirga a faɗin Jihar. Wannan ya biyon tashin wani bom a ranar Laraba a kasuwar Kawori, wanda ake zargin ƴan ƙungiyar boko haram ne suka saka. Bom ɗin yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama da kuma jikkata wasu su ma. Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Borno, Nahum Kenneth Daso, shi ya sanar da sanya wannan dokar, inda yace gwamnan Jihar Babagaba Zulum bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki ya ga ya dace a sanya wannan dokar domin dawo da zaman lafiya da lumana a jihar. Ya na mai roƙon mutanen jihar za…
Read More
An fara ƙone-ƙone a wasu wuraren zanga-zanga a Kano

An fara ƙone-ƙone a wasu wuraren zanga-zanga a Kano

Zanga-zangar matsin rayuwa da ake gudanarwa a kano ta rikiɗe a wani sashin da ya janyo an fara ƙone-ƙone. Rahoton da Blueprint Manhaja ke samu shine, wasu masu zanga-zangar sub fasa ofishin hukumar da ke kula da harkokin sadarwa in da suka ɗauke abubuwa da dama kamar su kujeru, kwamfuta da sauransu wanda daga ƙarshe suka cinna ma ofishin wuta. Masu zanga-zangar sun kasance matasa ne wanda suka je kofar gidan gwamnatin jihar suna kiran "bamayi", "canji muke so" Masu zanga-zangar an hangesu suna tahowa daga sassa daban daban na jihar. A wani ɓangare kuma, wasu sun fito suna zanga-zangar…
Read More
Gwamnan Zamfara ya biya giratuti na aƙalla 7.3 biliyan ga ma’aikatan da su kai ritaya

Gwamnan Zamfara ya biya giratuti na aƙalla 7.3 biliyan ga ma’aikatan da su kai ritaya

Gwamna Dauda Lawal ya biya Giratuti na aƙalla naira biliyan 7.3 ga ma'aikatan Zamfara da su kai ritaya. Idan bamu manta ba, gwamnatin Zamfara ta kafa wani kwamiti a watan Janairu da zai tantance waɗanda a ke bi bashi tsakanin shekarar 2015 zuwa 2024 da kuma ma'aikatan ƙananan hukumomi daga 2012 zuwa 2019. Wannan ya fito ne daga bakin mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris inda ya bayyana cewa gwamnati ta biya ₦7,345,674,918.42 na giratuti da ba a biya ba tsawon shekaru. Ya cigaba da bayyana cewa, an yi wannan biyan ne sau bakwai kuma yanzu haka yana…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: Zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan ta samu rashin fitar matasa a Gusau

Da Ɗumi-Ɗumi: Zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar nan ta samu rashin fitar matasa a Gusau

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar a yau ta fara gudana a Gusau babban birnin Jihar Zamfara wanda galibin matasa basu fita ba. Wakilinmu ya ruwaito cewa, masu zanga-zangar sun yi cincirindo ne a kusa da asibitin ƙwararru na Yariman Bakura ɗauke da wasu kwalayen da suka ƙunshi bayanai kamar haka, a mayar da tallafin man fetur, rashin kyakkyawan shugabanci na gari, a cire harajin wutar lantarki, a buɗe kan iyakokinmu da dai sauransu. Wakilinmu ya lura cewa matasa da yara ‘yan ƙasa da shekaru goma ne suka fito a zanga-zangar wadda aka fara…
Read More
Ministan Labarai ya umarci ‘yan Nijeriya su haƙura da zanga-zanga

Ministan Labarai ya umarci ‘yan Nijeriya su haƙura da zanga-zanga

Ministan ƴaɗa Labarai Mohammed Idris ya shawarci ƴan Nijeriya da su sa himma wajen amfani da irin abubuwan alheri shugaba Tinubu ya kawo maimakon bada himma ga zanga-zanga. Ministan yayi wannan kiran ne a taron manema labarai na duniya a Abuja.Ya jaddada cewa, shekara guda na Shugaba Tinubu ya zo da abubuwan alheri da ƴan Nijeriya za su mora sosai. Ya cigaba da cewa, a shekara ɗaya ya ɗora ginshiƙin cigaban tattalin arziki, tsaro da sauran ayyukan more rayuwa. Yace kar su manta shugaban kwanan nan ya sanya hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashi, ya bada umarnin bada motocin…
Read More

Bom ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama a Borno

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Aƙalla mutane 19 ne su ka rasa rayukansu a yayin fashewar wani bom da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne su ka dasa a wajen cin abinci a ƙauyen Kawuri da ke ƙaramar hukumar Konduga a jihar Borno. Lamarin, ya auku ne a ranar Laraba, kwanaki bayan da mayaƙan su ka kai hari ofishin ƴan sandan Jakana da ke ƙaramar hukumar inda aka kashe ɗan sanda da wata mata tare da ƙona motocin sintiri guda biyu. Wani jami'in gwamnati daga ƙauyen, ya ce lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 8:50 na dare inda mutane ke…
Read More
Zanga-zanga: Ofishin jakadancin Amurka ya umarci ma’aikatansa su zauna a gida

Zanga-zanga: Ofishin jakadancin Amurka ya umarci ma’aikatansa su zauna a gida

Ofishin Jakadancin Amurka, ya umarci ma'aikatansa da su zauna a gida tsawon kwana biyu saboda zanga-zangar matsi na rayuwa da za a gudanar a Nijeriya. A wani saƙo da ofishin ya aika wa ma'aikatan na sa, ya umarci ma'aikatan su zauna a gida har sai an ce su dawo. Yayin da wanda ayyukansu ba sa yankewa, a ka buƙaci su yi aiki yau Alhamis da Juma’a. Jami'an tsaro a ƙasar sun nuna damuwa sosai matuƙa, domin ba su son irin abinda ke faruwa a Kenya, ya maimaita kansa a ƙasar.
Read More
Muna tare da matasanmu – Dattawan Arewa

Muna tare da matasanmu – Dattawan Arewa

Wasu dattawan Arewa da masu ruwa da tsaki, sun goyi bayan matasa a kan shirin zanga-zangar ƙuncin rayuwa da za a gudanar. A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Yusuf Usman, Naja’atu Muhammad, Umar Ardo da Salihu Usman a ranar Laraba, inda su ka ce hujjar yin zanga-zangar gaskiya ne. Sun ƙara da cewa, shugabanni da dama a ƙasar sun kasa magance matsalolin da ke addabar 'yan ƙasar da dama. Don haka ya zama wajibi a ƙyale mutane su nuna rashin jin daɗinsu a kan yadda a ke tafiyar da al’amuransu. Sun yi kira da a guji amfani da…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Kotu ta taƙaice filin wasan MKO Abiola a matsayin wajen zanga-zanga a Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake shirin fara zanga-zangar tsadar rayuwa a gobe Alhamis, babbar kotun birnin tarayya Abuja, ta taƙaice wa ƴan zanga-zanga yin gangaminsu a filin wasa na MKO Abiola a cikin birnin. Mai Shari'a Sylvanus Oriji ya bayar da umarnin hakan a lokacin da ya ke yin hukunci kan wani saƙon neman maslaha da Ministan Abuja, Nyesom Wike ya shigar. A cikin takardar, Wike ya buƙaci kotun ta dakatar da shugabannin zanga-zangar biyar daga yin zagaye a kan titina, unguwanni, ofisoshi da wasu wuraren da al'umma ke wasu harkoki a Abuja. Daga ranar 1 zuwa 10…
Read More