Labarai

An tsaurara tsaro a Majalisar Dokokin Nijeriya yayin da mambobi ke zaman gaggawa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A yayin da ake shirye-shiryen fara zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya, ƴan majalisar dokoki suna gudanar da zama na gaggawa zauren Majalisar. Sakamakon haka ne aka tsaurara matakan tsaro a kewayen Majalisar, biyo bayan zargin zanga-zanga ka iya ɓarkewa da za ka iya haifar da dakatar da zaman. A ranar Lahadi ne ƴan Majalisar Dokokin su ka sanar da batun wanda hakan ya shafi kwanaki hutunsu na shekara da su ka fara a makonnin da su ka gabata. Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan majalisar wakilai, Rotimi Akin ya fitar ta ce, zaman…
Read More

Zanga-zanga: Gwamnatin Katsina ta umarci a gaggauta rufe makarantu a jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci a rufe dukkan makarantu a faɗin jihar. Sanarwar ta fito daga mai magana da yawun ma'aikatar ilimin ƙananan makarantu, Ɗanjuma Sulaiman inda ya ce gwamnatin ta ce a sanar da mutane musamman iyayen yara cewa hutun zai fara ne daga ranar Laraba. Ya ƙara da cewa, hutun shi ne mafarin hutun zango na uku, ɗaya daga cikin zango-zango da makarantun ke yi a shekarar. Ya yi kira ga iyayen da su ɗakko ƴaƴansu da ke karatu a makarantun kwana zuwa gidajensu, ya na mai cewa dokar ta shafi makarantun kuɗi da…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa ‘yan ta’adda na iya fakewa da zanga-zanga

Gwamnatin Tarayya ta yi gargaɗin cewa ‘yan ta’adda na iya fakewa da zanga-zanga

Gwamnatin Tarayya na jan kunne a kan cewa ƴan ta'adda na iya fakewa da zanga-zangar da ake shirin yi domin kawo tashin hankali ko aikata ɓanna kamar yadda sakataren Gwamnatin Tarayya George Akume ya faɗa. Ya cigaba da cewa, zanga-zanga ba ita ce amsar halin da ake ciki ba na matsin rayuwa wanda ya tabbata shugaban ƙasa yana iya bakin ƙoƙarin shi ya shawo kai. A wannam gaɓa ne, na ke kira da 'yan Nijeriya da cewa su ƙara hakuri, komai zai wuce nan bada jimawa ba. Yayi kira da ƴan Nijeriya masu shirya zanga-zanga da su zo ai zauna…
Read More

Gwamnan Kano ya gayyaci ƴan zanga-zanga gidan gwamnati, ya yi gargaɗin tashin-tashina

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani nau'in tashin-tashina ba yayin da ake gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya. Gwamnan ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da shugabannin ƴan kasuwa, sarakunan gargajiya da malaman addini a Fadar gwamnatin jihar da ke Kano a ranar Laraba. Abba Kabir ya ce, "zanga-zanga babu inda za ta kai mu. Ina kira ga waɗanda su ke ƙoƙarin aiki da ƴancinsu na yin zanga-zanga da su kaucewa nuna kowace irin halayya da gurɓatattu zasu yi amfani da…
Read More
An kashe ɗiyar Alƙali Ajumogobia a Legas

An kashe ɗiyar Alƙali Ajumogobia a Legas

Daga USMAN KAROFI a Abuja An kashe ɗiyar mai sharia Rita Ajumogbia Aribemchukwu a Legas da safiyar Laraba. Mamaciyar wadda aka fi sani da Chuchu an kashe ta a gidanta da ke rukunin gidajen da ake kira Parkview Estate da ke unguwar Ikoyi a birnin Legas. Wani ɗan uwanta da ya buƙaci a ɓoye sunan shi ya bayyana cewa an kashe ta ne a gidanta, inda a ka tsinci gawar ta a kusa da rukunin gidajen. An fara zargi sabbin masu aiki da ta ɗauka aiki da basu jima ba. Domin alamu sun nuni cikin gidan kamar an so a…
Read More
Mu na zaune mu na cin abinci ku na zanga-zanga – Akpabio

Mu na zaune mu na cin abinci ku na zanga-zanga – Akpabio

Shugaba Majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya cewa 'yan Nijeriya da za su yi zanga-zanga su yi zanga-zanga amma fa su, su na gida su na cin abinci. Akpabio yayi wannan zancen ne a wani taro da hukumar NDDC ta shirya a Jihar Ribas. 'Yan Nijeriya sun shirya yin zanga-zangar nuna halin matsin rayuwa da ake ciki. Amma wasu jigo a jam'iyyar APC sun ce wannan wani shiri ne kawai na kifar da gwamnatin Bola Tinubu. Akpabio ya ce, muma muna jin wannan matsin rayuwar amma dole muyi hakuri saboda abu ne na ɗan karamin lokaci.
Read More

‘Yan zanga-zanga sun ƙi amincewa da buƙatar Sufeton ‘Yan sanda ta yi a keɓaɓɓun wurare saɓanin kan titina

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Talata ne waɗanda su ka shirya zanga-zangar 'EndBadGovernance' da za a yi a watan Agusta su ka ƙi amincewa da buƙatar Sufeton 'Yan sanda, Kayode Egbetokun, ta neman su gudanar da ita a keɓaɓɓun wurare madadin fitowa kan tituna. Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da tsare-tsaren yadda zanga-zangar za ta gudana, a wani zama da aka yi da jagororin tafiyar da rundunar ƴan sandan. Egbetokun ya ce "ba dai-dai ba ne a yi gangami a kan titi da nufin yin zanga-zanga. Wasu kuma na shirya yin tashin-tashina". Lauya Ebun-Olu Adegboruwa (SAN)…
Read More
Kotu ta bada umarnin yin zanga-zanga a Freedom da Peace park kaɗai a Legas

Kotu ta bada umarnin yin zanga-zanga a Freedom da Peace park kaɗai a Legas

Wata babbar kotu a Legas ta bada umarnin yin zanga-zanga a Peace Park da Freedom Park kaɗai ba faɗin Jihar Legas ba. Mai shari'a Emmanuel Ogundare shi ya bayar da wannan hukunci. In ba mu manta ba, 'yan Nijeriya a faɗin ƙasar na shirin gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa a ranar ɗaya ga watan Agusta 2024. Wani babban Lauya Lawal Pedro shine ya shigar da ƙarar, yana mai faɗin cewa, ƴan ƙasa na da ƴancin yin zanga-zanga amma bai kamata su mamaye ko ina ba domin gudun shiga haƙƙin waɗanda ba za su shiga zanga-zangar ba. Pedro ya cigaba da…
Read More
UNDP ta buƙaci inganta haɗin kan sojoji da fararen hula a yankunan da ake fama da rikici

UNDP ta buƙaci inganta haɗin kan sojoji da fararen hula a yankunan da ake fama da rikici

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Hukumar UNDP ta jaddada buƙatar samar da ingantaccen haɗin gwiwa tsakanin sojoji da farar hula don inganta ayyukan jin ƙai da tallafa wa zaman lafiyar da farar hula ke jagoranta a yankunan da ake fama da rikici. Wakiliyar UNDP a Nijeriya Elise Attafuah, ranar Litinin a Abuja, ta jagoranci bikin bude taron bita na kwanaki biyar ga jami’an hadin gwiwa na jami’an tsaro, da ma’aikatan sa ido da tantancewa kan yadda ake shawo kan rikice-rikice da kuma samar da tsaro bakidaya. Taron wanda UNDP ta shirya domin nuna kwarewar aikin soja a cikin shirye-shiryen…
Read More