Labarai

Zanga-zanga: Gwamnatin Tinubu na buƙatar taimakon ƴan Nijeriya don tabbatar da ayyukanta, inji Shettima

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mai girma Mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya aika saƙon neman taimakon ƴan Nijeriya kan ƙaddamar da shirye-shirye da ayyukan Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya na mai cewa shugaban ƙasar na nufin al'umma da alkhairi. Ya ce, jita-jita a wasu wurare na cewa Shugaba Tinubu na adawa da cigaban Arewa ko Musulunci ba haka ba ne, ya mai buga misali da cewa hakan da zai nuna yayin raba manyan muƙamai da Tinubu ya yi na ma'aikatu, hukumomi da ofisoshin wasu ɓangarori. Shettima ya faɗi hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin tawagar ƴan jarida…
Read More

DA ƊUMI-ƊUMI: Masu shirya zanga-zanga sun sanar da wuraren haɗuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Talata, 30 ga watan Yuli, masu zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya su ka fitar da wuraren da za a haɗu wanda za a fara daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta. An samu bayanin ne cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun wani lauya mai suna Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) wanda shi ne Antoni Janar na masu shirya zanga-zangar inda a ciki ta ke cewa, saƙo ne zuwa ga Sufeto Janar na 'Yan sanda, Kayode Egbetokun. Takardar, ta zayyano wuraren da za a yi zanga-zangar da kuma nuni ga muhimmancin hakan…
Read More

Hukumar ‘Yan sanda ta sanar da fara horar da sabbin jami’ai bayan rikici da rundunar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da ƴan sanda, PSC ta sanar da lokacin fara horar da sabbin jami'ai bayan sa'insa tsakanin ta da rundunar kan jadawalin waɗanda aka ɗiba. Yayin da PSC ta fitar da sanarwar ɗaukar sabbin jami'ai 10,000, a ranar 4 ga watan Yuni, rundunar 'Yan sanda ta ƙi amincewa da hakan, ta na mai cewa akwai rashawa da ƙin bin hanyoyin da su ka dace wajen ɗaukar ma'aikatan a cikin hakan. Duk da matsayar rundunar, PSC ta ƙi sauya jadawalin wanda hakan ya sa Ministan harkokin Ƴan sanda, Ibrahim Gaidam ya shiga cikin lamarin tare da…
Read More
ƙungiyar Sawaba ta janye shiga zanga-zangar da ake shirin yi a Nijeriya

ƙungiyar Sawaba ta janye shiga zanga-zangar da ake shirin yi a Nijeriya

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Ƙungiyar Sawaba reshen Jihar Jigawa ƙarƙashin jagorancin shugaban ta na Jihar ta Jigawa kwamared Bashir Kashim Bash ta nuna damuwar ta kan yanayin rayuwa da 'yan Nijeriya suke ciki na tsadar rayuwa da hauhawar kayan masarufi da matsalar rashin tsaro a wasu sassa na arewacin Nijeriya . Shugaban yaci gaba da cewa, faɗuwar darajar Naira a kasuwar duniya da ciyo bashin bankin duniya da IMF wanda gwamnatin tarayya ta keyi babu ƙaƙƙautawa yana daga cikin abubuwan da suka ƙara durƙusar da Nijeriya su ka tsunduma 'yan ƙasar cikin ƙuncin rayuwa Haka zalika ya soki…
Read More
Gwamnan Kano ya turawa majalisar dokoki sunan wanda zai naɗa a matsayin kwamishina

Gwamnan Kano ya turawa majalisar dokoki sunan wanda zai naɗa a matsayin kwamishina

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamna Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf ya tura sunan wani tsohon soja ga majalisar dokokin Jihar kano domin tantace shi a matsayin kwamishina. Wanda a ka tura ɗin shi ne Manjo Janar Muhammad Inuwa Idris mai ritaya. Shugaban majalisar Isma’il Falgore ne ya karanta wasiƙar da gwamnan ya tura musu, yayin zaman majalisar na wannan rana ta Talata. Majalisar ta buƙaci wanda aka tura sunan na shi da ya gurfana gaban majalisar gobe Laraba domin tantancewa.
Read More
Daloli da yawa ake fita da su Nijeriya duk sa’a ɗaya –  INTERPOL

Daloli da yawa ake fita da su Nijeriya duk sa’a ɗaya – INTERPOL

Ƙungiyar 'yan sanda na duniya wadda a ke kira da INTERPOL ta bayyana cewa sa'a ɗaya miliyoyin daloli a fitar wa daga Nijeriya da sauran ƙasashen Afrika. Ƙungiyar ta bayyana harkar halasta kuɗin haram ya ƙaru sosai a wannan shekarar musamman a ƙasashen mu na Afirka wanda dole sai hukumomin tsaro sun tashi tsaye sannan za su yi maganin wannan abun. Garba Baba Umar wanda shine mataikin shugaban na Afirka shi ya bayyana hakan a yayi buɗen wani taron ƙarawa juna sani da aka shiryawa jami'an 'yan sanda da ke Nijeriya. Umar ya cigaba da cewa dole a tashi tsaye…
Read More

Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da aikin titin Magami-Ɗansadau

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sanya hannu kan fara aikin hanyar Magami zuwa Ɗansadau wacce za ta kai tsawon kilo mita 108. Gwamnan ya gabatar da hakan ne a yayin zama da Majalisar Zartarwar Jihar a Fadar gwamnatin Zamfara a ranar Litinin. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, hakan na zuwa ne la'akari da ƙoƙarin da gwamnatin Jihar ke yi kan matsalolin tsaro da ya addabi mutanen yankin. Dauda Lawal, "ya ƙaddamar da ƙwantiragin aikin ga kamfanin Gini na Ɗantata da Sawoe kasancewar sa wanda ya…
Read More

EFCC ta gayyaci Shugaban NAHCON kan aikin Hajjin 2024

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati, EFCC ta gayyaci Shugaban hukumar jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Malam Jalal Arabi zuwa ofishinta da ke Jabi a Abuja. Rahoto daga 'News Point Nigeria' ya ce, EFCC ta gayyaci Arabi ne domin yin bayani game da yadda ya sarrafa Naira biliyan 90 da gwamnati ta bayar na tallafi ga Alhazan Hajjijn 2024. Haka kuma EFCC za ta gabatar da tuhume-tuhume kan Arabi da NAHCON ciki har da zargin rashin karrama Alhazan yadda ya dace a ƙasar Saudiyya yayin aikin hajjin. Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum huɗu a Imo

‘Yan bindiga sun kashe mutum huɗu a Imo

A ranar Litinin ne ‘yan bindiga suka yi wa ‘yan sanda huɗu kwanton ɓauna a unguwar Irete da ke kan titin Onitsha a Owerri, babban birnin Jihar Imo. A cewar majiyoyi, ‘yan bindigar sun kai farmaki kan ‘yan sandan da ke sintiri a lokacin An kuma bayar da rahoton kashe wani mai sana'ar PoS da wani mai wucewa a harin da ‘yan bindigar suka kai wa ƴan sandan. Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Henry Okoye ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce an kashe ‘yan sanda huɗu ba shida ba. Wannan harin dai shi ne na baya bayan nan a…
Read More

Zanga-zanga: Jami’ar Bayero ta ce za ta cigaba da aiki yadda aka saba

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da kwanakin zanga-zangar tsadar rayuwa ke ƙara kusantowa a Nijeriya, Hukumar gudanarwa ta Jami'ar Bayero ta Kano, ta ce za a cigaba da gudanar da harkokin makarantar kamar yadda aka saba. Mataimakin shugaban reshen kula da harkokin al'umma na jami'ar, Lamara Garba ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannunsa inda ya bayyana cewa su na sane da batut fara zanga-zangar a ranar 1 ga watan Agusta. Hukumar gudanarwar ta sanar da al'umma cewa, za a cigaba da harkoki a jami'ar kamar yadda aka saba, ya na mai shawartar ma'aikata da…
Read More