Labarai

Mahajjatan Nijeriya 30 ne su ka rasu a 2024 – NAHCON

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar jigilar Alhazan Nijeriya, NAHCON ta ce aƙalla mutane 30 ne su ka rasa rayukansu a yayin aikin hajjin bana. Shugaban hukumar, Malam Jalal Arabi ya faɗi haka a yayin ganawa da ƴan jarida inda ya ce mutane huɗu ne su ka mutu sakamakon zafin rana da ya haifar da ɗumamar yanayi. Ya ce, duk da a cewa an sanar da su batun sauyin yanayin, zafin rana a shekarar 2024 ya zama daban saboda tsananinsa. Ganin haka ya sa hukumar ta samar da kayayyakin kariya da su ka haɗa da lemomi da wasu ababan garkuwa daga…
Read More

Zanga-zanga: Gwamnati ta fara sayar da buhun shinkafa N40,000

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta fara raba manyan motocin shinkafa goma-goma ga kowace jiha, domin sayar da kowane buhu mai nauyin kilo giram 50 a kan farashin N40,000. Majalisar Zartarwar, FEC ta ce babu buƙatar zanga-zangar tsadar rayuwa, ta na mai cewa ana ƙoƙarin magance mafi yawancin matsalolin da masu shirya ta su ka zayyano. Yayin da ake kusantar lokacin zanga-zangar, Shugaba Tinubu ya ce, ya na ƙoƙarin magance matsalolin matasan. Ministan labaru, Mohammed Idris ya ce raba shinkafar wani ɓangare ne na ƙoƙarin magance matsalolin talauci da tsadar rayuwa.…
Read More

Zanga-zanga: NYSC ta dakatar da tantancewar alawus ga ƴan hidimar ƙasa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da yi wa Ƙasa hidima, NYSC ta dakatar da tantancewar biyan alawus da ' zaman mako-mako da ma'aikatanta da aka fi sani da ƴan bautar Ƙasa ke yi na wucin-gadi sakamakon zanga-zangar gama-gari da ake shirin gudanarwa a sassan Nijeriya. An samu sanarwar hakan ne daga ofishin hukumar inda ta ke umurtar wakilanta na jihohi, ƙananan hukumomi da yankuna da su dakatar da ayyuka. Hukumar ta haramta wa ƴan hidimar ƙasar shiga cikin zanga-zangar, tana mai ƙarawa da cewa za ta sanar da lokacin da za a cigaba da ayyukan tantancewar da sauransu. Kazalika,…
Read More

Sufeto Janar ya umarci Rundunar ‘Yan Sanda ta bai wa ƴan zanga-zanga kariya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sufeto Janar na 'Yan sanda, Kayode Egbetokun ya umarci manyan jami'an hukumar da su bai wa ƴan zanga-zanga kariya wacce za a fara daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta. Kayode ya faɗi hakan cikin wani saƙo da ya fitar bayan da wani babban lauyan kare ƴancin Ɗan Adam, Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) ya nemi Sufeton ya ɗauki matakin bai wa ƴan zanga-zangar kariya. Haka nan, Kayode ya buƙaci haɗuwa da lauyan don tattauna muhimman abubuwa kan batun inda za su gana a ranar Talata, 30 ga watan Yuli. Zanga-zangar, wacce ta ɗauki hankalin al'umma musamman…
Read More

Zanga-zanga: Amurka, Birtaniya da Canada sun gargaɗi al’umma kan tsaro

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙasashen Amurka, Birtaniya da Canada sun ankarar da al'ummar Nijeriya game yiwuwar aukuwar tashin-tashina yayin zanga-zangar tsadar rayuwa da za a fara a ranar Alhamis. Ƙasashen sun aika sakonnin ne ta mabanbanta hanyoyi inda su ka gargaɗi mutanensu da su ƙaurace wa artabu da ka iya aukuwa tsakanin jami'an tsaro da ƴan zanga-zanga, su na masu bada misali da ire-iren yadda su ka faru a baya. Sannan, saƙonnin sun iso ne bayan da manyan ƴan kasuwa a jihohin Abuja, Sakkwato, Kano, Katsina, Ogun, Osun, Zamfara, Gombe da wasu yankunan Nijeriya su ka buƙaci a tsaurara tsaro…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Majalisa ta kira taron gaggawa kan zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio ya kira taron gaggawa na ƴan Majalisar. Sanarwar kiran ta fito daga ofishin akawonsa, Chinedu Akubueze a ranar Litinin inda ya ce za a yi taron ne musamman kan ababan da ke damun ƙasa a halin yanzu. Za a gudanar da taron ne a ranar Laraba, 31 ga watan Yuli, 2024 da misalin ƙarfe 12 na rana, kwana ɗaya kafin fara zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya. Sanarwar ta ƙara da cewa, ana buƙatar sanatoci su yi duk shirye-shiryen da su ka dace don tattauna batutuwa masu muhimmanci ga ƙasa, majalisar…
Read More
NCC ta bada umarnin buɗe duk layukan da aka rufe

NCC ta bada umarnin buɗe duk layukan da aka rufe

Hukumar sadarwa ta Nijeriya ta bada umarnin buɗe duk wani layin waya da aka rufe a dalilin rashin haɗa shi da NIN. 'Yan Nijeriya da yawa sun wayi gari a rufe masu layukan waya a dalilin rashin haɗa shi da NIN ɗinsu. Sai dai a wata sanarwa da hukumar ta NCC ta fitar a ranar litinin, wanda Rueben Mauka ya sanya wa hannu ta bada umarnin duk wanda aka rufe masa layi a buɗe saboda ba a ba 'yan Nijeriya wadataccen lokacin da za su haɗa layin nasu da lambar NIN ta su. Sannan hukumar ta ba mutane shawara da…
Read More

Zanga-zanga: Ku tabbatar da tsaro a makarantu, Gwamnatin Tarayya ga shugabannin jami’o’i

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake cigaba da kusantar kwanakin zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya, Ministan Ilimi, Tahir Mamman, ya umarci shugabannin jami'o'i su shirya matakan kariya don bai wa makarantunsu da malamai da ɗalibai tsaro a lokacin zanga-zangar. Sakataren hukumar kula da jami'o'i ta Ƙasa (NUC), Chris Maiyaki ya fitar da wata sanarwa a ranar Litinin, ya na mai umartar shugabannin jami'o'i su fitar da jawabai na tabbatar da tsaro ga malamai da ɗaliban makarantunsu. Maiyaki, ya kuma shawarci ɗalibai da su kasance a cikin makarantu tare da mayar da hankali kan karatunsu domin kauce wa haɗuran…
Read More

Sojoji sun karɓe ragamar kula da manyan titinan Abuja kwana uku kafin zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI An samu matsewar ababan hawa a babbar hanyar Keffi-Abuja yayin da jami'an soji su ka datse wani yanki domin gudanar da bincike kafin shiga Birnin Tarayyar Abuja. Sojojin sun tare daidai barikin sojoji na Abacha da ke kusa da shataletalen AYA. Kasancewar hukumomin tsaro ba su bada sanarwar hakan ba, an samu cinkoson ababan hawa wanda ya kai har gadar Nyanya, kilomita 12 kafin wajen da aka datse. Da dama daga cikin ma'aikata da ƙananan ƴan kasuwa na Abuja da ke zama a Nyanya, Maraba, Karu da Masaka, an tilasta mu su komawa gida bayan tsawon…
Read More

‘Yan bindiga sun kai hari sansanin hukumar Kwastom, sun kashe jami’i da garkuwa da wani

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƴan bindiga sun kashe jami'in Kwastom tare da yin garkuwa da wani a harin da su ka kai sansanin hukumar a yankin Koko/Besse da ke Jihar Kebbi. Jami'in hulɗa da jama'a na hukumar a Jihar, Tajuddeen Salisu ya ce al'amarin ya faru ne a ranar Alhamis. Ya bayyana cewa, bayan garkuwa da ɗaya jami'in, ƴan bindigar sun kuma buƙaci maƙudan kuɗaɗe domin sako shi. Ya ƙara da cewa, an karɓi gawar jami'in da aka kashe shi ta hanyar yanka tare da kai shi Jihar Kaduna domin yi masa jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Kazalika,…
Read More