Labarai

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya sanya hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashi

Da Ɗumi-Ɗumi: Tinubu ya sanya hannu kan dokar sabon mafi ƙarancin albashi

Shugaba Tinubu ya sanya hannu ga dokar sabon mafi ƙarancin albashi a yau. Hakan ya biyo bayan dogon tattaunawa tsakanin ƙungiyoyin Ƙwadago, gwamnati da ƙungiyoyi masu zaman kansu. Rahoton da Manhaja ta samu ya tabbatar Shugaba Tinubu ya sanya hannu ranar litinin a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio tare da wasu 'yan majalisun sun halarci sanya hannun domin shaida wannan gagarumin nasara.
Read More

Da ƊUMI-ƊUMI: Zanga-zangar yunwa ta ɓarke a Neja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wasu matasa a Jihar Neja sun fito cikin gari domin zanga-zangar tsadar rayuwa da ake fama da shi a Nijeriya. Matasan sun fito da alluna da ke ɗauke da batutuwa kamar haka; 'Enough is Enough', Stop 'Anti-Masses Policies', 'We Are Not Slaves In Our Country', 'Hardship Is Unbearable', 'Fuel Subsidy Must Be Back' da sauransu. A lokacin zagayen, matasan na rera wakokin da ke nuna adawa da gwamnati. Gwamnatin Tarayya da na jihohi sun yi ta ƙoƙarin dakatar da zanga-zangar saboda kar ɓata-gari su yi amfani da shi wajen haddasa fitina a ƙasa daga waɗanda ke…
Read More

Yadda farashin man fetur ya kai N1,300 a jihohi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sakamakon bushewa da rijiyoyin man fetur da dama su ka yi, an samu layuka a gidajen mai a jihohin Kano, Legas, Kaduna, Ribas, wasu yankuna na Abuja, Nija da wasu jihohi a faɗin Nijeriya. Rahotanni sun bayyana cewa, hakan ya sa ƴan bunburutu su ke amfani da damarsu wajen sayar da duk lita ɗaya a farashin N1,300 da N1,500 a jihohin Legas da Ogun. An fara samun yawaitar layin man ne tun ranar Asabar a jihohin inda kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya ce hakan na faruwa ne sakamakon tseko da ake samu wajen ɗakko…
Read More
An cafke ɗan majalisa, tsohon ciyaman da hakimi bisa zargin garkuwa da mutane a Zamfara

An cafke ɗan majalisa, tsohon ciyaman da hakimi bisa zargin garkuwa da mutane a Zamfara

Wani ɗan majalisa da ke wakiltar ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara ya faɗa hannun 'yan sandan Jihar Zamfara bisa zargin hannu da ya ke dashi a garkuwa da mutane. Kwamishinan 'yan sanda na Zamfara, CP Muhammad Shehu Dalijan ne ya bayyan haka a wata tattaunawa da yayi. Ya bayyana cewa akwai Hakimin Kaura Namoda, Alhaji Jafaru Abdullahi da kuma tsohon ciyaman na Kaura Namoda, Nasiru Muhammad bisa zargin garkuwa da mutanen. Hakiman Bukuyum, Danjibga da Unguwar Gyauro waɗanda ke ƙananan hukumomin Tsafe da Bukuyum suma ana zargin su a laifin da aikata. Bincike ya fara nuna Hakimin Kaura…
Read More

Ba yaudara a rarrashin da Tinubu ke yi kan zanga-zanga – Sanata Barau

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Sanata Barau I. Jibrin ya roƙi masu shirya zanga-zangar gama-gari su sake yin nazari kan hukuncinsu tare da janye wa daga batun, don kar a yamutsa sauran zaman lafiyar da ya rage wa Nijeriya. Barau, wanda shi ne Mataimankin Kakakin Majalisar ECOWAS na farko, ya ce Tinubu na muhimmin ƙoƙari wajen ganin an magance matsalolin Nijeriya. Wata takarda da ta fito daga ofishin mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ta ce Barau ya yi kira ga masu hura wutar zanga-zangar kan cewa su bai wa Shugaba Tinubu ƙarin…
Read More
An tsige sarautar matashi saboda goyon bayan zanga-zanga a Minna

An tsige sarautar matashi saboda goyon bayan zanga-zanga a Minna

Hakimin ƙaramar hukumar Bosso da ke jihar Neja, Muazu Adamu-Laka, ya tuɓe wa wani matashi mai fafutuka, Abdullahi Isah sarautar gargajiya a matsayin Sarkin Matasan Bosso saboda ya goyi bayan zanga-zangar yunwa da ƙuncin rayuwa da a ke shirin yi a faɗin kasar. Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa yankin yana cikin Masarautar Minna.An tattaro cewa shugaban matasan ya fito fili ya goyi bayan zanga-zangar da aka shirya za a fara ranar 1 ga watan Agusta. Sai dai a wata wasiƙar da a ka aike wa shi matashin, Isah mai ɗauke da kwanan watan 28 ga watan Yuli, sarkin ya…
Read More

Ku nisanci zanga-zanga, inji jagoran CAN ga Kiristoci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙungiyar Kiristocin Nijeriya (CAN) reshen jihar Nija ta yi kira ga mabiyanta cewa kar su shiga zanga-zangar tsadar rayuwa da za a yi a watan Agusta. Shugaban CAN na jihar, 'Bishop Bulus Yohanna ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ne cewa wasu kan iya amfani da zanga-zangar wajen tada fitina da za ta iya shafar waɗanda basu-ji-ba basu-gani-ba. Yohanna ya kuma yi kira ga Shugaba Tinubu da cewa, baya ga rarraba tallafi, akwai buƙatar a yi aiki kan farashin kayayyaki wanda hakan ya haifar da tsadar rayuwa ƙasar da kuma batun da…
Read More

Peter Obi ya yi gargaɗi kan ɓarkewar rikici a zanga-zanga

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana matsayarsa game da zanga-zangar tsadar rayuwa da ke tafe A wata Agusta. A lokacin da ya ke magana bayan wani zama da gwamnan Jihar Abia, Alex Otti a ranar Lahadi, Obi ya ce masu zanga-zangar sai sun tabbatar da kiyaye doka da oda, ya na mai kira ga hukumomin tsaro cewa su bi umarnin doka, domin duk duniya an halatta yin zanga-zanga. Wannan shi ne karo na farko da Obi ya magantu kan zanga-zangar. Mai bai wa Shugaba Tinubu shawara kan harkokin labaru, Bayo…
Read More

Ruftawar gini ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku a Jigawa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Akalla mutane uku ne su ka mutu sakamakon ruftawar wani gini a Jihar Jigawa. Jami'in hulɗa da jama'a na Rundunar Ƴan sandan Jihar, Lawan Salisu Adam ya tabbatar da aukuwar lamarin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya na mai cewa wasu huɗu sun samu raunuka. A wani jawabin, kiwon dabbobi ya haifar da rikici a ƙauyukan Maikambu da Balalashe na Ƙaramar Hukumar Garki inda aka ƙona gidaje biyar tare da raunata mutum shida. Rundunar 'Yan sandan ta ce ta kama mutum biyu da hannu a cikin aukuwar rikicin tare da ƙoƙarin kwantar…
Read More

Tsohon ɗan jarida Lawal Saulawa ya rasu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon ɗan jarida, Alhaji Yusuf Saulawa ya rasu yana da shekaru 80 a ranar Asabar. Saulawa ya rasu ne da dare a gidansa da ke Badikko a Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Kudu a Jihar Kaduna. Alhaji Yusuf ya kasance wakilin gidan BBC kimanin shekaru 50 da su ka gabata yayin da daga baya ya riƙe muƙamin kwamishinan labaru a tsohuwar Jihar Kaduna da kuma kwamishinan labaru na farko a Jihar Katsina. Haka nan shi ne, ya kasance Daraktan shirye-shirye a gidan Muryar Nijeriya (VON) da kuma Babban Daraktan hukumar kula da gidajen rediyo ta Ƙasa, FRCN.…
Read More