Labarai

Turji ya sake jaddada ministan Tinubu cikin masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda

Turji ya sake jaddada ministan Tinubu cikin masu ɗaukar nauyin ‘yan ta’adda

Fitaccen ɗan bindigan nan Kachalla Bello Turji ya jaddada maganarsa da yayi na cewa, Ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar zamfara ya na bada gudunmuwa sosai wajen ta'addanci a Arewacin Nijeriya. A wani faifan bidiyo, Turji ya jaddada Matawalle ya kasance yana bada taimakon kuɗi da sauran taimako ga 'yan ta'adda a yankin Arewacin ƙasar. Wannan na zuwa ne bayan da Matawallen ya ƙaryata wannan zargin da Turji yayi masa. Ya ce wannan zargin, so a ke a zubar ma Matawalle da mutunci da kuma ɓata mashi suna. Sai dai wannan na zuwa ne a lokacin da Arewacin Nijeriya ke…
Read More
Ƙungiyar iyaye mata ta roƙi masu shirin zanga-zanga su yi haƙuri

Ƙungiyar iyaye mata ta roƙi masu shirin zanga-zanga su yi haƙuri

Wata ƙungiyar iyaye mata masu addu'a, sun yi kira da 'yan Nijeriya da kar suyi zanga-zanga domin wanzar da zaman lafiya da cigaban ƙasa. Shugabar ƙungiyar ta ƙasa Rev. Dr Lois Angula ce ta faɗi haka a Abuja yayin ganawa da 'yan jarida. Ta ce, tabbas 'yan Nijeriya na cikin matsin rayuwa, amma zanga-zanga ba ita ba ce za ta kawo sauƙi ba. A cewar ta, zanga-zangar ka iya rikiɗewa ta zama tashin hankali sosai. A na ta faɗin, addu'a ya dace yanzu ba zanga-zanga ba. Ta cigaba da cewa, shugaba Tinubu addu'a ya ke buƙata yanzu ba zanga-zanga ba.…
Read More

Yaran Nijeriya sun roƙi Tinubu ya dakatar da zanga-zangar tsadar rayuwa

Daga KAHLID IDRIS DOYA a Bauchi Ƙungiyar yaran Nijeriya, NCCF sun koka wa Shugaba Tinubu kan cewa ya ɗauki matakan da demokradiyya ta bada dama wajen dakatar da zanga-zangar gama-gari da ke tafe a watan Agusta. Jagorar ƙungiyar, A'isha Hassan Saraki wacce ɗaliba ce makarantar 'Sunshine International', ta gana da manema labarai a ranar Asabar inda ta ce a matsayinsu na jikokin Tinubu, su na kira gare shi da ya bi hanyoyin da doka ta amince da su wajen magance matsalolin Nijeriya. A'isha mai shekaru 8, ta ce a madadin iyayensu da ma ƙasa baki ɗaya su na roƙo da…
Read More
Tinubu ya cigaba da aikin titin Abuja zuwa Kano da Buhari bai kammala ba – Ministan Ayyuka

Tinubu ya cigaba da aikin titin Abuja zuwa Kano da Buhari bai kammala ba – Ministan Ayyuka

Gwamnatin Tarayya ta koma aikin tItin Abuja-Kaduna-Zaria-Kano mai tsawon kilomita 375.9. Ministan ayyuka, Engr. David Umahi, ya bayyana hakan ne a jiya a yayin ƙaddamar da aikin aikin titin mai tsawon kilomita 38 ga rukunin kamfanin Dangote. Umahi a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Barista Orji Uchenna ya fitar, ya buƙaci kamfanoni uku da ke kula da sassan uku da su nuna cikakkiyar sadaukarwa ga kammala aikin. Ya yi nuni da cewa ma’aikatar za ta duba buƙatar sake duba kuɗi domin daƙile illolin hauhawar farashin kayayyaki. Ya ce, “Kashi na farko…
Read More

Ƴar Tinubu ta soki zanga-zangar tsadar rayuwa, ta ce yin hakan kan mahaifinta ya yi wuri

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƴar Shugaba Tinubu, Folshade Tinubu-Ojo ta caccaki zanga-zangar tsadar rayuwa da aka shirya yi a Nijeriya, tana mai cewa hakan wa ƙoƙarin da mahaifinta ke yi wa ƙasar ya yi wuri. Folshade wacce ita ce babbar 'Iyaloja' ta Jihar Legas ta faɗi hakan ne a lokacin da take ganawa da taron ƴan kasuwa cikin wata ɗaukar bidiyo a ranar Lahadi a Jihar Legas. A lokacin da ta ke magana da mata ƴan kasuwa ta harshen Yarbanci, Folshade ta yi kira gare su da su gargaɗi ƴaƴansu game da haɗurran zanga-zanga, ta na mai bada misali da…
Read More

Dalilan da su ka dawo da layukan man fetur a Abuja da Legas – NNPCL

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Kamfanin man fetur na Ƙasa, NNPC ya ce tseko da ake samu daga wuraren jido man fetur su suka haifar da wahalarsa a Abuja da Legas. Wata sanarwa da Jami'in yaɗa labara NNPL, Olufemi Soneye ya fitar a ranar Asabar, ta ce kamfanin na ƙoƙari wajen shawo kan matsalar, kamar yadda 'Blueprint' ta ruwaito. Ya ce, suna cigaba da aiki tuƙuru da masu-ruwa-da-tsaki domin ganin an warware matsalolin da ke haifar da layukan. Soneye, ya ƙara da cewa su na fatan nan ba da jimawa ba za a dawo sayen man yadda aka saba a wuraren…
Read More

An dakatar da Cynthia ta Nijeriya daga gasar Olympics bisa gwajin ƙwayoyi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI An dakatar da ƴar wasan 'boxing' ta Nijeriya, Cynthia Ogunsemilore daga shiga gasar Olympics sakamakon gwajin ƙwayoyi da aka yi mata a ranar Asabar a yayin da ake cigaba da shirin wasanta na farko. Hukumar gwajin ƙwayoyi ta ƙasa-da-ƙasa, ta ce bayan gwajin Cynthia an tabbatar cewa ta na shan maganin 'furosemide wanda yana daga cikin ababan da hukumar ta haramta wa ƴan wasa. Shafin ATI ya wallafa cewa, a halin yanzu an dakatar da ita har sai an warwara matsalar kamar yadda ya ke a cikin dokokin kwamitin gasar. Sannan, hakan ya nuna cewa Cynthia…
Read More
Nijeriya ta tsaurara tsaro a iyakokin ƙasa gudun shigowar ɓatagari lokacin zanga-zanga

Nijeriya ta tsaurara tsaro a iyakokin ƙasa gudun shigowar ɓatagari lokacin zanga-zanga

Gwamnatin tarayya ta tsaurara tsaro kan iyakokinta domin hana shigowar ɓatagari a yayin zanga-zangar matsin rayuwa da aka shirya yi 1 ga watan Agusta 2024 Shugaban hukumar shige da fice Kemi Nandap ta bada umarnin duk ma'aikatan su da su ƙara sanya ido domin gujewa shigowar ɓata gari. Kuma ta dakatar da ma'aikatan hukumar daga tafiya hutu har sai an gama zanga-zangar. Ta yi kira kuma da su zama yan ƙasa nagari masu kishin ci gaban Nijeriya.
Read More
Facebook sun goge shafin Mawaƙi Rarara biyo bayan rubdugun ƙorafi

Facebook sun goge shafin Mawaƙi Rarara biyo bayan rubdugun ƙorafi

Facebook sun goge shafin sanannen mawaƙin siyasan nan Dauda Kahutu Rarara biyo bayan ƙorafe-ƙorafe da mutane su ka shigar dalilin yin wa Shugaba Bola Tinubu waƙa. Hakan ya biyo bayan wata waƙa da ya saki a shafin na shi, wanda a cikin ta yake yabon shugaban Tinubu da cewa yayi maganin yunwa, talauci da kuma tsaro. Wannan waƙar ya saketa a lokacin da 'yan Nijeriya ke fama da matsalolin hauhawar farashin kayan abinci, rashin tsaro da matsanancin talauci. Wannan shi ya tunzura mutane su kai ta kai ƙarar shafin nasa ga Facebook. Mawaƙin in ba mu manta ba, satin da…
Read More

Gwamnati ta ƙaryata jawabin ‘Tinubu Speaks’ da ke yawo

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A wani yunƙurin gaggawa game da wani jawabi da aka yi wa laƙabi da 'Tinubu Speaks' da ake danganta shi da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya ta ƙaryata abin da ke ciki tare da nesanta Shugaban da shi. A ranar Asabar ne Mai magana da yawun Shugaban ƙasa, Ajuri Ngelale ya yi watsi da saƙon, yana mai cewa ba gaskiya ne abin da ake jingina wa Shugaba Tinubu. Ana yaɗa ƙirƙirarren labarin ne a kafafen sada zumunta kan cewa wani jawabi ne da Tinubu ya yi inda ya ke magana game da ƙalubalen da…
Read More