Labarai

NIS ta dakatar da ɗaukar hutu ga ma’aikata kan zanga-zangar tsadar rayuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI La'akari da zanga-zangar tsadar rayuwa da ke tafe a watan Agusta, hukumar shige da fice, NIS ta sanar da dakatar da neman zuwa hutu ga ma'aikatanta na wucin-gadi. Kwamturola Janar ta hukumar, Misis Kemi Nandap ta bada umarni ga shugabannin shiyyoyi da na jihohi da kuma na yankuna, inda ta ce akwai buƙatar aiki na musamman a kan iyakokin ƙasa domin tabbatar da tsaro a lokacin zanga-zangar. Cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Kenneth Udo ya fitar, hukumar ta ce tana shirye-shirye domin tsare duk wani kutse da ka iya tunkaro ƙasar…
Read More

Majalisar Wakilai ta shirya neman a tsige Kyari daga shugabancin NNPC

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Majalisar Wakilai ta yi barazanar kiran a tsige shugaban kamfanin man fetur na Ƙasa (NNPC), Mele Kyari idan ya cigaba da takurawa ayyukan matatar Ɗangote. Mataimakin kakakin majalisar, Philip Agbese ya faɗi hakan a yayin hira da manema labaru a Abuja. Haka nan, Agbese ya ce Majalisar ta bayyana goyon bayanta game da tsige shugaban hukumar tace man fetur ta Ƙasa (NMDPRA), Umar Farouk, yana mai cewa NNPCL da NMDPRA sun nuna kushewarsu da ƙiyayya ga matatar Ɗangote wanda hakan ya haifar da matsaloli wa ƙasa Nijeriya. Ya ƙara da cewa, tuni dai Majalisa ta umarci…
Read More

Ki bayyana yadda za a magance matsaloli madadin takura wa zanga-zanga, CISLAC ga Gwamnatin Tarayya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Cibiyar tabbatar da dokoki wa al'umma, CISLAC ta yi kira ga gwamnatin Nijeriya ta tsara jadawalin magance koken ƴan ƙasa a madadin sanya takunkumi ga zanga-zanga. Daraktan CISLAC, Kwamared Auwal Musa Rafsanjani ya nuna buƙatar gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa game da matsalolin hauhawar farashi, rashin aikin yi, rashawa, rashin tsaro da kuma rarrabewar cibiyoyi. Rafsanjani ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakin bada kariya ga masu zanga-zanga, yana mai cewa dokar ƙasa ta amince da zanga-zangar lumana. Haka nan, ya bukaci ƙananan hukumomi da jihohi su bi hanyoyin da suka dace wajen fuskantar matsalolin…
Read More
Mu guji zanga-zanga a faɗin ƙasar nan – APC reshen Jihar Zamfara

Mu guji zanga-zanga a faɗin ƙasar nan – APC reshen Jihar Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Jam’iyyar All Progressives Congress(APC) reshen Jihar Zamfara ta gargaɗi ‘yan jihar da su guji shiga zanga-zangar da a ke shirin yi a faɗin ƙasar saboda akwai yiwuwar haifar da hargitsi. Shugaban jam'iyyar na jihar Hon. Tukur Umar Danfulani ya yi wannan gargaɗin a Gusau ranar Asabar. Hon Danfulani ya bayyana cewa kiran ya zama wajibi saboda matsalar tsaro da ta addabi Zamfara da sauran jihohin da ke maƙwabtaka da ita kamar, Katsina, Kaduna, Sokoto da kuma Kebbi a Arewa maso Yamma, inda ya jaddada cewa akwai buƙatar zaman lafiyar Nijeriya a matsayin ƙasa ɗaya dunƙulalliya.…
Read More
Sanata Ifeanyi Ubah ya yi mutuwar fuju’a a Landon

Sanata Ifeanyi Ubah ya yi mutuwar fuju’a a Landon

Sanannen ɗan kasuwan nan, kuma Sanata Ifeanyi Ubah ya gamu da mutuwar fuju'a a wani otel da ke Landon Ubah ya gamu da ajali ne bayan ta bayyana cewa yana da ciwon zuciya kuma ya mutu jiya a Landan. Ya kasance mai shekaru 52. Wasu ‘yan uwa da suka haɗa da matar shi, sun fara zaman makoki bayan da aka samu labarin cewa ɗan uwan nasu ya mutu a wani otel da ke babban birnin kasar Birtaniya, jaridar The Gazette ta ruwaito jim kaɗan bayan da Sahara Reporters ta fara yaɗa labarin a safiyar ranar Asabar. Mista Ubah ya kasance…
Read More

Ku bada ƙarfinku ga zaɓe maimakon zanga-zanga – Kwankwaso

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NNPP a zaɓen 2023, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya zargi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da laifuka shida na siyasa da tattali yayin da ya buƙaci al'ummar Nijeriya su mayar da hankali kan zaɓe ba zanga-zanga ba. Kwankwaso ya faɗi haka a ranar Asabar cikin wata sanarwa da ya fitar game da batun zanga-zangar 'EndBadGovernment', yana mai nuna damuwa kan halin da Nijeriya ta tsinci kanta inda ya danganta hakan da gazawar gwamanti tun daga shekarar 2007. Ya ce, shugabanci mai kyau da adalci na girmama dokar ƙasa, bayyanawa ga kowa,…
Read More
An samu gawar ɗalibar Jami’ar ATBU da ke Bauchi a banɗaki

An samu gawar ɗalibar Jami’ar ATBU da ke Bauchi a banɗaki

Wata ɗalibar Kimiyyar Kwamfuta yar aji 300 a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU) Bauchi, Naja’atu Salisu ta rasu bayan an same ta a sume a wani banɗakin dalibai da safiyar Juma’a. Rahotanni sun bayyana cewa, Naja’atu ta shiga banɗaki ne na ɗakin kwanan dalibai mata da ke harabar jami'ar na Gubi domin yin wanka tare da shiryawa domin tafiya aji kamar yadda ta saba amma sai a ka ji ta shiru bata fito ba. Wata abokiyar Naja’atu tace “ Ta gama duk shirye-shiryen tafiya aji da safe kafin ta shiga banɗakin. Hatta kayan da zaka saka ta fito dasu ta…
Read More
Masu sayar da mai na rufe gidajen mai a yayin da a ke shirin zanga-zanga

Masu sayar da mai na rufe gidajen mai a yayin da a ke shirin zanga-zanga

Masu sayar da mai a garuruwan Abuja, Kogi da Nasarawa sun rufe gidajen mai dalilin shirin zanga-zanga da za gudanar ɗaya ga watan Agusta 2024, wanda ya jawo layin mai na dawowa a sassan garuruwan . A birnin tarayya, gidajen mai da dama har wanda hukumar NNPC ta mallaka sun daina sayar da mai ranar Juma’a. Wanda hakan ya jawo gidajen man da ke sayarwa, layi yayi yawa sosai a anguwannin Dei-Dei, AYA, Zuba da sauransu. Haka lamarin yake a garuruwan Legas, Ogun, Ibadan. Masu aikin tuƙa mota suna koka wa yadda hakan ba ya bari suyi aikin su sosai…
Read More

Ofishin jakadancin Amurka ya yi gargaɗi kan zanga-zangar gama-gari a Nijeriya

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ofishin jakadancin Amurka a Nijeriya ya yi gargaɗi game da zanga-zangar gama-gari da ake shirin yi a Nijeriya wanda ake tsammanin farawar sa daga 29 ga watan Yuli zuwa 5 ga watan Agusta. Sanarwar ta wacce ta fito daga ofishin, ta ce zanga-zangar ka iya haifar da tare hanyoyi, madakatun bincike, cinkoson ababan hawa da artabu na gaba-da-gaba duk da cewa ba a san takamaiman wuraren da hakan za su faru ba. Domin kaucewa faɗawa cikin haɗari, ofishin jakadancin ya bada shawarwari kamar haka; Bibiyar gidajen jaridu na gida domin samun labaru da ɗumi-ɗuminsu, nisantar tarurruka,…
Read More

Lauyoyi sun ja kunnen Sufeto Janar kan kawo cikas ga zanga-zangar lumana

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake cigaba da shirin zanga-zanga a faɗin Nijeriya, lauyan kare ƴancin Ɗan Adam, Inibehe Effiong ya aika da saƙo ga Sufeto Janar na 'Yan sanda, Kayode Egbetokun inda ya buƙaci a bai wa masu zanga-zangar kariya. Effiong ya ce zanga-zangar lumana a dokar Nijeriya ta halatta, dan haka akwai buƙatar hukumomin tsaro su ba su kariya, ya na mai kafa hujja da sakin-layi na 39 da na 40 na kundin dokar ƙasa. Ya ƙara da kira ga Sufetan, ya umarci dukkan kwamishinoni da ɓangarorin da ke da alhakin bayar da tsaro ga al'umma domin…
Read More