Labarai

Majalisar sarakunan gargajiya ba su amince da yin zanga-zanga ba

Majalisar sarakunan gargajiya ba su amince da yin zanga-zanga ba

Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Nijeriya ta koka kan zanga-zangar wahala da tsadar rayuwa da aka shirya yi. Matsayin Majalisar kan wannan batu yana ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da ta fitar a ƙarshen taron kwamitocin zartaswa na ƙungiyar da ta ke yi duk bayan wata uku. Sanarwar wacce ta samu sa hannun Shugaban Kwamitin gudanarwa na Majalisar, Mai Martaba Sarki Alh. (Dr.) Yahaya Abubakar, CFR, Etsu Nupe, ya bayyana cewa taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin mai martaba Alhaji (Dr.) Muhammad Sa'ad Abubakar, CFR, mni, Sarkin Musulmi, da kuma Mai Martaba (Dr.) Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, CFR, Ojaja Il,…
Read More

Kotu ta yanke wa ƴan Boko Haram 125 hukunci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Aƙalla mayaƙan Boko Haram 125 tare da masu ɗaukar nauyinsu ne aka yanke wa hukunci a bainar jama'a a wani zama na kwana biyu a Kainji da ke jihar Nija. An same su ne laifukan ta'addancin kan iyaka, tallafa wa ta'addanci da wasu lafukan kotun fashin ƙasa-da-ƙasa. Antoni Janar na ƙasa kuma Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi, shi ne wanda ke sanya ido kan lamarin hukuncin tare da haɗin gwiwar ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro. An gudanar da hukuncin ne a ranakun Talata da Laraba wanda masu shari'a biyar daga babbar kotun…
Read More

Zanga-zangar tsadar rayuwa: Rundunar ‘Yan sanda ta baza jami’ai 4,200 a Abuja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar 'Yan sandan Abuja ta ɗauki matakin baza jami'ainta a lunguna da saƙo-saƙo na babban birnin sakamakon zanga-zangar tsadar rayuwa da wasu masu ƙishin al'umma da matasa su ka shirya yi a faɗin Nijeriya. Mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Edeh ta bayyana hakan wa manema labarai a ranar Juma'a, inda ta ce sun ɗauki matakin bada kariya wa al'umma ta hanyar yin bincike ga masu zanga-zangar a wurare daban-daban da haɗin gwiwar wasu hukumomin tsaro. Ta ce, Kwamishinan babban birnin, Benneth Igweh a lokacin da ya ke magana akan damar ƴanci da dokar ƙasa…
Read More
Arewa na kan siraɗi, inji Gwamnan Kaduna

Arewa na kan siraɗi, inji Gwamnan Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana damuwarsa kan yadda ƙananan yara da ba sa zuwa makaranta, talauci da sauran matsalolin tattalin arziki da ake fama da su a Arewa, ya bayyana cewa yankin na daf da wargajewa idan shugabanni ba su haɗu don nemo hanyoyin magance ƙalubalen ba. Uba Sani ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar ban girma da shugaban Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), Mamman Osuman ya kai jihar Kaduna. Ya ce, “Wannan sabon kwamitin zartarwa ya fito ne a lokacin da ake fuskantar ƙalubale. Muna fuskantar ƙalubalen a ɓangaren cigaba da tsaro.…
Read More
Matawalle ya musanta zargin kusanci da ’yan bindiga

Matawalle ya musanta zargin kusanci da ’yan bindiga

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙaramin Ministan Tsaro kuma tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya musanta zargin ta’addancin da wani sarkin 'yan bindiga, Bello Turji ya yi masa, yana mai cewa 'yan adawar sa ne ke yi masa sharri. Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga ofishin Ministan a ranar Lahadi. A cikin wani faifan bidiyo da ya fitar a shafukan sada zumunta, Turji, shugaban ƙungiyar ɓarayin daji da ke gudanar da ayyukanta a arewacin Nijeriya, ya zargi Matawalle da rashin tafiyar da harkokin tsaro yadda ya kamata a lokacin da yake gwamnan jihar Zamfara.…
Read More
CBN na shirin shawo kan hauhawar farashin kayayyaki

CBN na shirin shawo kan hauhawar farashin kayayyaki

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ce zai ɗauki matakan da suka dace domin shawo kan hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar. Gwamnan CBN Olayemi Cardoso wanda ya bayyana hakan a yayin taron manufofin kuɗi (MPC) ya ce yayin da manufofin kuɗi ke daidaita yawan buƙatu, hauhawar farashin abinci da makamashi na ci gaba da yin matsin lamba kan bunƙasa farashin. MPC na Bankin Apeɗ ya ƙaru da Manufofin Kuɗi (MPR), da kashi 50, daga kashi 26.25 zuwa kashi 26.75 cikin ɗari. Babban bankin ya sake jaddada ƙudurinsa na tabbatar da daidaiton farashin Bankin kuma ya ci gaba…
Read More
An farfaɗo da shari’ar mutanen da ake zargi da ta’addanci

An farfaɗo da shari’ar mutanen da ake zargi da ta’addanci

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya ta ce ta ci gaba da shari'ar wasu mutane sama da 300 da ake zargi da hannu a ayyukan ta'addanci da kuma waɗanda ake zargi da aikata munanan laifuka a Nijeriya. Wata sanarwa da shugaban Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa (NCTC), ofishin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) Abu Michael, ya fitar ta bayyana cewa, shari’ar ta biyo bayan ƙudirinta na inganta adalcin zamantakewar al’umma ta hanyar kafa tsarin gudanarwa na gaskiya. Ya ce, shari’ar da ake ci gaba da yi wadda ta yi daidai da tsarin shari’ar manyan laifuffuka…
Read More
Yakamata ’yan Nijeriya su goyi bayan Matatar Dangote, inji Otedola

Yakamata ’yan Nijeriya su goyi bayan Matatar Dangote, inji Otedola

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Hamshaƙin ɗan kasuwar nan, Femi Otedola, ya bayyana dalilin da ya sa ya kamata ’yan Nijeriya, musamman gwamnati su goyi bayan shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote, ta hanyar samar da yanayi mai kyau don ganin kasuwancinsa ya bunƙasa. Ya bayar da hujjar cewa gudunmawar da Dangote ya bayar wanda ya wuce wuraren masana'antu zuwa muhimman ababen more rayuwa, dole ne a gane su kuma a tallafa masa ta kowace hanya. Otedola, wanda ya tashi don kare abokinsa kuma abokin kasuwancinsa a wani rubutu a shafinsa na Ɗ a ranar Talata, ya bayyana Dangote a matsayin "Kyautar…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta kira taron gaggawa don warware batun zanga-zangar matsin rayuwa

Gwamnatin Tarayya ta kira taron gaggawa don warware batun zanga-zangar matsin rayuwa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jami'an Gwamnatin Tarayya sun shirya taron gaggawa don warware batutuwan shirin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar. Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya yi wa manema labarai jawabi a ranar Laraba a Abuja, inda ya jaddada cewa gwamnati ba ta yin sakaci da ayyukanta tare da neman ƙarin lokaci daga 'yan Nujeriya. Idris ya ba da tabbacin cewa za a warware dukkan batutuwan domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar. Ya ƙara da cewa, a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Tinubu ke martaba 'yancin 'yan ƙasa na gudanar da…
Read More
 Zanga-zanga: Ya kamata Shugaban Ƙasa ya tashi tsaye, ‘yan Nijeriya na cikin wani hali — NLC

 Zanga-zanga: Ya kamata Shugaban Ƙasa ya tashi tsaye, ‘yan Nijeriya na cikin wani hali — NLC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa, sun shawarci Shugaban Ƙasa Bola Tinubu da ya daƙile zanga-zangar da ta kunno kai a faɗin ƙasar ta hanyar tattaunawa da waɗanda su ke shirya ta. Daily Trust ta rawaito cewa daruruwan ‘yan Nijeriya na gangami domin gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar. Da ya ke tsokaci kan lamarin, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Joe Ajaero, ya buƙaci shugaban ƙasar da ya gano jagororin zanga-zangar ya tattaunawa da su. Ajaero ya kuma yi kira ga Tinubu da ya saurari kukan jama’a, inda ya ƙara da cewa miliyoyin ‘yan…
Read More