27
Jul
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Sufeton ‘Yan Sadan Nijeriya, IGP, ya ce sun shirya tsaf domin tunkarar zanga-zangar da wasu ‘yan ƙasar ke shiryawa a wata mai zuwa, yana mai cewa “za mu kare masu zanga-zanga matuƙar dai ta lumana ce”. Sai dai da yake magana bayan ganawa da manyan jami’an rundunar na faɗin Najeriya, Kayode Egbetokun ya yi kira ga matasa da haƙura da zanga-zangar “saboda gwamnati na bakin ƙoƙarinta”. “Idan zanga-zangar ta lumana ce za ku ganmu muna kare masu zanga-zangar. Ba mu adawa da zanga-zangar lumana, za mu taimaka wa masu zanga-zangar lumana saboda ‘yancinsu…
