20
Jul
Daga RABI'U SANUSI a Kano An jaddada yunƙurin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ƙoƙarin kawo canjin bai ɗaya a ɓangaren noma a faɗin Jihar Kano baki ɗaya. Wannan na zuwa ne daga bakin shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Hon Abubakar Mu'azu Moja a wata zantawa da manema labarai yayin da tawagar sa suke adana takin da aka basu tare da sauran Kansilolin sa baki ɗaya. Hon Abubakar Mojo ya ce, a yadda mai girma Gwamna Abba Kabir ya mayar da hankali wajen canza akalar jihar ta hanyoyi daban-daban domin ci gaban jama'ar sa. Hon Mojo ya kuma bayyana cewa…
