Labarai

Yarjejeniyar Samoa: Jihar Kano ba za ta lamunci baɗala ba, inji Sheikh Tijjani Auwalu 

Yarjejeniyar Samoa: Jihar Kano ba za ta lamunci baɗala ba, inji Sheikh Tijjani Auwalu 

Daga MAHAMMAU MUJJITABA a Kano Kwamishinan Kula da Al'amuran Addinai na Jihar Kano, Sheikh Tijjani Auwalu ya bayyana cewa a daidai wannan lokacin da muka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1446, Jihar Kano ba za ta lamunce da baɗala ba da sunan auren jinsi kamar yadda ake ta cece-kuce kan yarjejeniyar Samoa da ake zargin a cikinta akwai wasu sharuɗɗa da suka saɓa wa addinin Musulunci da kuma kyawawan al'adu. Sheikh Tijjani Auwal ya yi wannan bayani ne a lokacin da yake hira da 'yan jaridu a Kano Alhamis ɗin makon jiya. "Mu a nan ma'aikatar kula da addini muna…
Read More

Nan ba kulob ba ne, sai an ba ki dama kafin ki yi magana – Akpabio ya gargaɗi Natasha

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban majalisar dattijai, Godswill Akpabio ya faɗa wa Sanatar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan cewa zauren majalisar ba kulob ba ne, don haka sai an gabatar da ita kafin ta yi magana a zaman majalisar. Hakan ya faru ne a lokacin da majalisar ke tafka muhawara game da ƙudirin ƙirƙirar dokar majalisar sufurin motoci da dangoginsu wanda Sanatan Kwara ta Kudu, Oyelola Ashiru na jam'iyyar APC ya ɗauki nauyinsa. Ƙudirin mai suna 'National Road Transportation Council (Establishment) bill, 2024' ya ƙunshi kula da harkokin sufurin da aikin yin sufurin da abubuwan da suka shafe su a…
Read More
Ina roƙon ’yan Nijeriya da su ƙaurace wa shiga zanga-zanga — Zulum

Ina roƙon ’yan Nijeriya da su ƙaurace wa shiga zanga-zanga — Zulum

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya yi kira ga al’ummar jihar da ma ’yan Nijeriya baki ɗaya da su ƙauracewa shiga zanga-zangar da ake shirin yi a faɗin ƙasar nan a wata mai zuwa. Zulum ya yi wannan roƙo ne a ranar Laraba yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Fadar Gwamnatin Borno da ke Maiduguri. Gwamnan ya ci gaba da cewa, a madadin wannan mataki da ’yan ƙasa ke shirin ɗauka, zai fi dacewa su shiga tattaunawa mai ma’ana domin zanga-zangar na iya haifar da tarzoma da tashin hankali a…
Read More

Gwamnati ta fitar da hotuna da sunayen waɗanda su ka tsere daga gidan yarin Suleja

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar gyaran hali ta ƙasa (NCoS), ta fitar da hotuna da sunaye da sauran bayanan waɗansu mutane da su ka tsere daga kurkukun Suleja, reshen Abuja, sakamakon ruftawar ginin da su ke ciki bayan wani mamakon ruwan sama da aka yi a ranar Laraba, 24 ga watan Afrilu, 2024. Wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar, Abubakar Umar ya fitar a ranar Alhamis, ta ce matakin yana da muhimmanci wajen sake kamo su tare da mayar da su komar hukumar. Ya ce, sun miƙa bayanan waɗanda suka tseren ga sauran hukumomin tsaro da kuma…
Read More
Gwamnatin Tarayya za ta ƙirƙiri kotunan tafi-da-gidanka don yaƙar cin zarafi

Gwamnatin Tarayya za ta ƙirƙiri kotunan tafi-da-gidanka don yaƙar cin zarafi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Gwamnatin Tarayya za ta kafa kotunan tafi-da-gidanka don magance matsalolin da suka shafi fyaɗe da sauran cin zarafi cikin gida. Ministar Harkokin Mata, Uju Kennedy-Ohanenye ce ta sanar da hakan a yayin wani taron kwana guda na masu ruwa da tsaki na kasa kan magance cin zarafi, da aka gudanar ranar Talata a Abuja. Hukumar ICPC tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Magance Matsalar Cin Zarafi ne suka shirya taron. Kennedy-Ohanenye ta bayyana damuwarta kan yadda ake samun yawaitar cin zarafi musamman a manyan makarantun ƙasar nan, ta kuma jaddada cewa ana aiwatar da sabbin matakai na…
Read More
Hauhawar farashi: Majalisar Wakilai ta yi barazanar kama shugabannin simintin Dangote

Hauhawar farashi: Majalisar Wakilai ta yi barazanar kama shugabannin simintin Dangote

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Kwamitin haɗin gwiwa na Majalisar Wakilai kan ƙarin farashin siminti, a ranar Talata, ya yi barazanar damƙe mahukuntan kamfanin simintin Dangote idan suka gaza bayyana a zamanta na gaba. Idan za a iya tunawa, a ranar 7 ga watan Mayun 2024 ne majalisar ta bada wa’adin kwanaki 14 ga masu kamfanin siminti da su gurfana a gaban kwamitinta na haɗin gwiwa tare da gabatar da ra’ayoyinsu kan ƙarin farashin siminti a Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba. Shugaban kwamitin majalisar mai kula da ma’adanai, Jonathan Gbefwi ne ya yi wannan sammacin a wajen wani taron…
Read More
Tinubu ya sauke surukin Buhari da wasu shugabannin hukumar buga kuɗi

Tinubu ya sauke surukin Buhari da wasu shugabannin hukumar buga kuɗi

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya gaggauta tsige Shugaban Hukumar Buga Kuɗaɗe da Muhimman Tarardun Sirri ta Nijeriya, NSPM, Alhaji Ahmed Halilu, tare da wasu manyan jami’ai huɗu. Ahmed Halilu, ɗan uwa ga A’isha Buhari, uwargidan Buhari, wanda Buhari ya naɗa shi a cikin watan Satumba, 2022, yana daga cikin waɗanda Tinubu ya kora. Sauran waɗanda korar ta shafa sun haɗa da Babban Darakta Ado Ɗanjuma, Babban Darakta na Legas, Chris Orewa, Babban Darakta Tunji Kazeem da Sakataren Kamfani, Ɓictoria Iraboh. Ita dai Victoria Iraboh matar Janar Lucky Irabor (mai ritaya) ce, wanda ya riƙe muƙamin Babban…
Read More
NAHCON ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2025 – Arabi 

NAHCON ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2025 – Arabi 

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Malam Jalal Arabi, Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa NAHCON ya bayyana cewa hukumar ta fara shirye-shiryen aikin hajjin 2025. Mataimakiyar Daraktar Hulɗa da Jama’a ta NAHCON, Fatima Sanda-Usara, a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata, ta ce Arabi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake bankwana da rukunin ƙarshe na maniyyatan Nijeriya a ƙasar Saudiyya. Shugaban NAHCON ya bayyana fatan hukumar za ta samu gagarumar nasara wajen gudanar da aikin hajjin 2025 bisa ga darasin da aka koya a bana. Arabi ya kuma miƙa godiyarsa ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa nasarar kammala aikin…
Read More
Gwamnatin Kano ta ƙwace filayen Legal da tsohon Gwamna Ganduje ya rabar

Gwamnatin Kano ta ƙwace filayen Legal da tsohon Gwamna Ganduje ya rabar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Kano Gwamnatin Jihar Kano ta ƙwace filayen da gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje ta raba tsakanin Kwalejin Kano da kwalejin Koyar da Shari’a ta Aminu Kano. Kwamishinan filaye da tsare-tsare na ƙasa, Abduljabbar Umar ne ya sanar da ƙwace filin ga manema labarai a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa Gwamna Abba Yusuf yana da ikon sashe na 28 na dokar amfani da filaye mai lamba 15 na Tarayyar Nijeriya, 2004, don ɗaukar wannan mataki. Ya ce gwamnatin jihar ta karɓe madadin wurin, wanda kuma aka bayar da ita ga cibiyar da ke Badume a…
Read More
An zane Ɗan Bilki Kwamanda ciki-da-bai bisa zargin cin zarafin gwamnan Kaduna

An zane Ɗan Bilki Kwamanda ciki-da-bai bisa zargin cin zarafin gwamnan Kaduna

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja Fitaccen ɗan siyasa daga Jihar Kano na Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya mai suna Dan Bilki ya sha tsabga a jikinsa cikin wani bidiyo wanda ya mamaye yanar gizo a ranar Alhamis ɗin nan, inda wasu waɗanda ba a gama sanin ko su waye ba suka zane shi tsaf bisa zargin sa da cin zarafin Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Uba Sani. Tun da farko an ji mutane su na umartar Ɗan Bilki, wanda ke cikin ankwa, da ya gabatar da kansa, inda kuma ya yi hakan, sannan suka tuhume shi da dalilinsa na sukar…
Read More