Labarai

Da ƊUMI-ƊUMI: Tinubu ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da Naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan Nijeriya yayin da ya alƙawuranta sabonta dokar albashi duk bayan shekaru uku. Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris ya faɗi hakan a Fadar shugaban ƙasa da ke Abuja, a ranar Alhamis. Ministan ya ce, shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a yayin ganawa da shugabannin haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadago. Waɗanda su ka halarci zaman sun haɗa da shugaban ƙungiyar ƙwadago (NLC), Joe Ajaero da na ƙungiyar kasuwanci (TUC), Festus Usifo tare da wasu mambobin ƙungiyoyin. Kafin zaman, ƙungiyar ƙwadago ta…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta haramta ɗaukar ɗalibai ‘ƴan ƙasa da shekara 18 a jami’a

Gwamnatin Tarayya ta haramta ɗaukar ɗalibai ‘ƴan ƙasa da shekara 18 a jami’a

Gwamnatin tarayya ta ba da umarnin cewa ɗalibai da ba su kai shekaru 18 ba su cancanci shiga manyan makarantu a Najeriya ba. Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ne ya sanar da wannan umarni a Abuja. A jawabinsa na bude taron gurbin karatu na 2024 da hukumar JAMB ta shirya. Ya kuma umarci hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB da ta aiwatar da sabbin ƙa’idojin da suka fara daga shekarar 2024. Ya ce matakin ya yi daidai da shawarwarin hukumar kula da ilimi ta kasa (NCE) da wasu dokoki, daga yanzu ya kamata a bi umarnin. Ya ce: “Na…
Read More

Ƙudirin zangon shekara shida ga shugaban ƙasa da gwamnoni ya tsallake karatun farko a majalisa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Majalisar wakilai ta gudanar da karatun farko ga ƙudirin da ke neman kwaskwarima ga kundin 1999 wanda zai mayar da yin shekara shida a kowane zango na ofishin shugaban ƙasa da gwamnoni da shugabannin ƙananan hukumomi. Ofishin shugaban ƙasa da na gwamnoni ya tsallake karatun ne a yayin zaman majalisar na ranar Laraba wanda Ikenga Ugochinyere da ke wakiltar mazaɓar Ideato ta Kudu da ta Arewa ta jihar Imo ya gabatar tare da wasu ƴan majalisa 50. Haka nan, ƙudirin na neman goyon bayan sakin layuka na 7, 135, 137, 180 da kuma na 182 kamar…
Read More
‘Ƴan sanda sun hana SSANU da NASU yin zanga-zanga

‘Ƴan sanda sun hana SSANU da NASU yin zanga-zanga

Rundunar ‘yan sandan Najeriya, reshen babban birnin tarayya, Abuja, a ranar Alhamis, ta dakatar da kwamitin hadin gwiwa, (JAC), na ƙungiyar SSANU da NASU daga gudanar da zanga-zanga a Abuja. Wakilin jaridar Blueprint ya tattaro cewa jami’an ‘yan sanda dauke da makamai da aka tura da motoci sun tare kofar shiga fitaccen dandalin Unity Fountain da ke Maitama a Abuja. Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, CP Benneth Igwe, ya halarci dandalin taron, inda ya shaida wa shugabannin ƙungiyar cewa ba za su yi amfani da titunan Abuja wajen gudanar da zanga-zanga ba ba tare da bayyana dalilin da…
Read More
Kotu ta yi watsi da ƙarar da ke ƙalubalantar rubutun Larabci a takardar Naira

Kotu ta yi watsi da ƙarar da ke ƙalubalantar rubutun Larabci a takardar Naira

Babbar kotu dake zamanta a Legas tayi watsi da ƙarar da aka shigar gabanta, a kan rubutun Larabci dake jikin kuɗin Naira. Mai shari'a Yellin Bogoro yayi hakane yana mai dogara da sashe na 53 na dokar bankuna da sauran al'amuran kuɗi wanda ke cewa har sai an tabbatar an yi wani abu da wata manufa sannan kotu zata amshi wannan ƙorafin. Kotun ta ƙara da cewa, ƙarar wanda wani lauya mazauni Legas ya shigar Malcom Omirhabo, yana mai ƙalubalantar rubutun Larabcin dake jikin takardar Naira ya gaza nuna wata shaida da ke tabbatar da cewa babban bankin ƙasa yayi…
Read More
Za mu amshe duk wasu kujerun shugabanci, inji gwamnonin PDP

Za mu amshe duk wasu kujerun shugabanci, inji gwamnonin PDP

Ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP, ta sha alwashin ƙwato dukkan muƙaman shugabancin da wasu jam’iyyun siyasa suka mamaye. Shugaban ƙungiyar Gwamnonin PDP, Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi ne ya yi wannan alƙawarin a wajen buɗe taron da aka yi ranar Laraba a gidan gwamnatin Jihar Enugu. Gwamna Bala Muhammad ya cigaba da cewa "A yau mun zo ne domin haɗa kawunan mu, sannan mu tattauna batutuwan da suka shafi jam’iyya da al’amura daban daban da suka shafe mu" Lokaci ya yi da jam’iyyar za ta ƙwato muƙamai na shugabanci a dukkan jihohin da a halin yanzu wasu jam’iyyu ke mamaye…
Read More
Tinubu ya naɗa Esther Walson-Jack a matsayin sabuwar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Tinubu ya naɗa Esther Walson-Jack a matsayin sabuwar Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da naɗin Mrs. Didi Esther Walson-Jack, OON, a matsayin Shugabar ma'aikatan Tarayyar Najeriya, inda zata karɓi ragamar aiki daga ranar 14 ga watan Agusta, 2024An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai baiwa Shugaban ƙasa shawara a kan harkar yaɗa labarai, Ajuri Ngelale a fitar a ranar Laraba.Sanarwar ta ce sabuwar shugabar zata karɓi ragamar aikinr daga hannun shugabar ma'aikata mai ci a yanzu, Dr Folashade Yemi-Esan, CFR, wacce zata yi ritaya a ranar 13 ga watan Agusta, 2024.Yayin da yake miƙa godiyarsa ga Shugabar ma'aikata mai barin gado a kan jajircewarta, shugaba…
Read More

Tinubu ya nemi majalisa ta amince da ƙarin tiriliyan N6.2 a kasafin 2024

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci majalisar dattijai ta yi kwaskwarima kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2024 ta hanyar ƙara tiriliyan N6.2 kan na shekarar da ta gabata. Jawabin hakan na ƙunshe a cikin wata takarda da Tinubu ya aika wa shugaban majalisar, Goodwill Akpabio wacce aka bayyana ta a zaman majalisar na ranar Laraba. Tinubu ya buƙaci hakan ne la'akari da samun goyon bayan sakin layi na 58 wanda reshe ne na sakin layi na biyu na kudin dokar ƙasa kwaskwarimar 1999 inda ya nemi majalisar ta amince da ƙudirin. Ƙundirin gyaran dokar ta 2024,…
Read More

Majalisar Dattijai ta sauke Ndume a matsayin Mai Tsawatarwa, APC ta nemi ya bar ta

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Majalisar Dattijai ta sanar da cire Sanata Mohammed Ali Ndume da ke wakiltar Borno ta Kudu a matsayin mai tsawatarwa inda ta maye gurbinsa da Tahir Mungono da ke wakiltar Borno ta Arewa. An samu hukuncin hakan ne a wani jawabi da kakakin majalisar, Goodwill Akpabio ya yi ta wata ɗaukar murya wanda jiga-jigan mambobin APC da ke majalisar suka amince da hakan. Majalisar ta yi hukuncin ne la'akari da sukan gwamnatin shugaba Tinubu da Ndume ya ke yi a ƴan kwanakin nan wanda hakan ya sa APC ƙarƙashin shugabancin Abdullahi Umar Ganduje, ta aika da…
Read More
‘Yan bindiga sun saki mahaifiyar Rarara bayan shafe kwanaki a tsare

‘Yan bindiga sun saki mahaifiyar Rarara bayan shafe kwanaki a tsare

Daga UMAR GARBA a Katsina Masu garkuwa da mutane sun saki mahaifiyar fitaccen mawaƙin siyasa, Dauda Adamu Kahutu Rarara. Blueprint Manhaja ta rawaito cewa 'yan bindiga dake satar mutane don neman kuɗin fansa sun yi garkuwa da Hajiya Hauwa Adamu a gidanta a ranar 28 ga watan Yuni, 2024, a ƙauyen Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, lamarin da ya haifar da damuwa da cece kuce a tsakanin masoya fitaccen mawaƙin musamman a arewacin ƙasar nan. Tun da farko dai masu garkuwa da mutanen sun buƙaci a biya su maƙudan kuɗin fansa Naira miliyan 900, kawo yanzu…
Read More