Labarai

Rundunar ‘Yan sanda ta dakatar da rijistar yanar gizo ga motoci

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sufeta Janar na 'Yan sanda, Kayode Egbetokun ya dakatar da rijistar yanar gizo ta e-CMR ga motoci a Nijeriya. An bada umarnin hakan ne kwana ɗaya bayan rundunar 'Yan sandan ta bada wa'adin 29 ga Yuli ga masu motoci su yi rijistar e-CMR kan Naira 5,375. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar da sanarwar bayan ƙorafe-ƙorafe daga ƴan ƙasa na cewa yin rijistar tilastawa ce ga waɗanda suka motoci. Shugaban ƙungiyar lauyoyi kan muradun al'umma da cigaban Shari'a, John Aikpokpo Martins ya ce umarnin yin rijistar abin a ƙi amincewa da…
Read More

Messi ya ji rauni yayin da Argentina ta lashe Copa America karo na 16

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ƙasar Argentina da ke Kudancin Nahiyar Amurka ta lashe gasar 'Copa America' karo na 16 bayan doke Colombia da ta yi da ci ɗaya da nema a birnin Miami. An dakatar da fara buga wasan na tsawon mintuna 80 bayan hayaniya ya kaure tsakanin magoya bayan ƙasashen biyu a wajen filin wasan. Kyaftin ɗin Argentina, Lionel Messi ya ji rauni yayinda yake ƙoƙarin karɓar ƙwallo a zango na biyu wanda hakan ya sa aka sauya shi da wani ɗan wasan inda ya bar fili yana zubar da ƙwalla. Lautaro Martinez shi ne ɗan wasan da ya…
Read More

Ministan labarai ya marabci ƴan jaridan da aka yi garkuwa da su bayan sako su

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ministan Labarai da Haɗin kan Ƙasa, Alhaji Mohammed Idris ya marabci ƴan jaridan da ke aiki a Kaduna da aka yi garkuwa da su a gidajensu ƙarshen makon da ya gabata. Sanarwar ta fito ne daga mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Rabi'u Ibrahim a yayin ganawa da manema labarai a Abuja, ranar Lahadi. A lokacin da ya ke magana yayin martabar AbdulGafar Alabelewe na jaridar 'The Nation' da kuma AbdulRaheem Aodu na jaridar 'Blueprint' daga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, Ministan ya jinjina wa hukumomin tsaro…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: PDP ta lashe duka kujerun shugabannin ƙananan hukumomin Adamawa

Da Ɗumi-Ɗumi: PDP ta lashe duka kujerun shugabannin ƙananan hukumomin Adamawa

Jam'iyyar APC ta sha kashi a hannun Jam'iyyar PDP a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Jihar Adamawa. Wannan ya fito ne bayan da hukumar zaɓe ta Jihar Adamawa ta bayyana sakamakon zaɓen. Ta bayyana cewa dukkanin kujerun Jam'iyyar PDP ce ta lashe tare da kansiloli. Sai dai Jam'iyyar NNPP tayi nasarar lashe kujerar kansila ɗaya. Hukumar ta tabbatar cikin jami'u 19, guda 12 ne kaɗai suka shiga zaɓe. Wannan zaɓen shine na farko da akayi bayan hukuncin kotun ƙoli a kan cin gashin kai na ƙananan hukumomi.
Read More
An kashe wanda ake zargi da yunƙurin kashe Trump

An kashe wanda ake zargi da yunƙurin kashe Trump

Jami'an hukumar FBI sun tabbatar da kashe wanda ake zargi da yunƙurin kashe tsohon Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump. Sunce sunyi nasarar kashe Thomas Mathew crook, ɗan shekara 20 daga Pennsylvania. A farkon sanarwa da suka bayar, sun ƙi yadda su bayyana sunan wanda ake zargin. Saboda a cewar su lokacin suna ta bincike kuma basu shirya faɗan wanda ya aikata wannan laifin ba. Sai dai yan sandan Pennsylvania sun tabbatar da cewa yanzu, suna da tabbacin cewa babu wani abu mai ban tsoro irin wannan da sake faruwa.
Read More
Jihar Zamfara ta yi zarra a Arewa a jarrabawar NECO 2024

Jihar Zamfara ta yi zarra a Arewa a jarrabawar NECO 2024

Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja Jihar Zamfara ta shiga jerin jihohin Arewa da su ka yi abun a zo a gani a jarrabawar NECO lokacin da hukumar ta fitar da sakamakon jarrabawa na rukunin ɗalibai masu hazaƙa. Wannan ya fito ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwaman jihar, Sulaiman Bala Idris, ya yi. Ya bayyana cewa a faɗin kasar, Jihar Zamfara ita ce ta zo na biyu da ɗalibai 35, yayin da Jihar Anambra ta zo na farko. Ya bayyana cewa, a karo na farko Jihar Zamfara ta zo na biyu a wannan jarabawar wanda ɗalibai…
Read More

Rundunar ‘Yan Sanda ta kama jami’inta kan zargin yi wa yarinya fyaɗe

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Rundunar 'Yan sanda ta kama wani jami'inta mai muƙamin mataimakin sufuritanda kan zargin yin fyaɗe wa wata ƴar shekara 17 a Legas. Ana zargin ɗan sandan mai suna Owolabi da samun damar afkawa yarinyar a ofishinsa da ke reshen rundunar a Ojota. An kama shi ne bayan da hukumar yaƙi da cin zarafi ta jihar ta shigar da wata takarda ofishin kwamishinan 'Yan sandan jihar, Adegoke Fayoade wanda hakan ya sa kwamishinan ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin. Mai magana da yawun rundunar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da kama jami'in nasu inda ya ce…
Read More

Shugabannin duniya sun bayyana kaɗuwarsu bisa kai wa Trump harbi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugabannin ƙasashe da dama sun nuna damuwarsu kan ji wa tsohon shugaban ƙasa Amurka, Donald Trump ciwo a wani harin kisan kai da aka kai masa a lokacin yawon yaƙin neman zaɓe. Shugabanni da Firaministoci sun yi tsokaci kan tare da sukan tashin-tashinar siyasa gami da nuna goyon bayansu ga waɗanda ibtila'in ya afka musu a ranar Asabar wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum ɗaya da kuma raunata wasu biyu a taron. Shugabar hukumar Turai, Ursula Von der Leyen ta ce ta yi matuƙar girgiza da harin inda ta ce babu gurbin tashin-tashinar siyasa a demokraɗiyya.…
Read More
Hukumar FBI ta tabbatar da yunƙurin kashe Trump a yayin yaƙin neman zaɓe

Hukumar FBI ta tabbatar da yunƙurin kashe Trump a yayin yaƙin neman zaɓe

Hukumar FBI ta tabbatar da yunƙurin kashe tsohon Shugaban ƙasar Amurka, Donald Trump a yayin yaƙin neman zaɓe a Butler, Pennsylvania. Wanda yayi yunƙurin yanzu haka ya mutu da wani mutum guda ɗaya. Sai kuma wasu jami'an tsaro da sun jikkata sosai, suna asibiti suna amsar kulawa. FBI ta fitar da sanarwa cewa " mun tabbatar da yunƙurin kashe tsohon shugan ƙasa Donald Trump a Pennsylvania." Sai dai hukumar baga bayyana sunan wanda ke da alhakin kai wannan mummunan harin ba.
Read More
An saki wakilan Blueprint da The Nation da akai garkuwa da su

An saki wakilan Blueprint da The Nation da akai garkuwa da su

Alamu sun nuna cewa, wakilan Jaridar Blueprint da The Nation Abduraheem Aodu and Abdulgafar Alabelewe sun sami ƙuɓuta daga hannun wanda suka yi garkuwa dasu. Wannan ya fito ne daga bakin shugabar ƙungiyar yan jaridu na ƙasa reshen Jihar Kaduna, Asma'u Yawo Halilu. Ta bayyana wannan saƙon ne ta manhajar WhatsApp inda ta ce" ƙungiyar na miƙa sakon jinjina ga rundunar ƴan sanda reshen jihar kaduna da kuma sauran jama'a wanda suka taya mu addu'a wannan lokacin" Jaridar Blueprint ta gano cewa ƴan jaridun suna hanyar zuwa Abuja.
Read More