Labarai

Tinubu ya naɗa sabbin shugabannin wasu hukumomi

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da naɗa Baffa Ɗan Agundi a matsayin sabon Darakta Janar na cibiyar bunƙasa ƙwazon aiki ta ƙasa (NPC). Mai taimaka wa Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale ya ce, Ɗan Agundi shi ne tsohon shugaban masu rinjaye na Majalisar Dokokin jihar Kano kuma tsohon rijistira a babban kotun Shari'a na jihar. Tinubu ya kuma naɗa tsohon mataimakin gwamnan jihar Nassarawa, Silas Agara a matsayin Darakta Janar na cibiyar samar da ayyuka (NDE). Agara, ɗan kasuwa ne kuma jigo a harkar wasanni. Haka kuma, "a hukumar kula da albarkatun ruwa…
Read More

Ministar al’adu ta taya Wole Soyinka murnar cika shekaru 90

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Ministar al'adu, Barista Hannatu Musa Musawa ta shiga sahun al'umma da dama wajen taya ɗaya daga cikin jigo a fagen ilimi, Farfesa Wole Soyinka murnar cikarsa shekaru 90 a duniya. Wata sanarwa da mai bata shawara kan harkokin yaɗa labarai, Nneka Ikem Anibeze ta fitar, ta ce ministar ta taya Farfesan murnar cimma nasarar kai wa matakin nasara irin haka gami da jinjina masa bisa ga halin juriya da ya siffanta da shi. Musawa ta kuma yi farin cikin sauya sunan cibiyar al'adu ta ƙasa zuwa cibiyar al'adu ta Wole Soyinka wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu…
Read More

An cinna gobara a fadar Sarki Sanusi

Daga FAROUK ABBAS Wani rahoto daga jihar Kano ya ce gobara ta kama a fadar Sarki Sanusi da ke Gidan Rumfa wanda ake zargin waɗansu da ba'a san ko su waye ba ne suka cinna ta, inda a nan ne Sarkin ya ke. Lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na daren Juma'a, a Ƙofar Kudu wanda a nan ne Sarkin ya ke zaman kotu duk ranar Litinin. Wani mutum da ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce suna zargin an buɗe mukullin ƙofar ne da ƙarfi sai kuma aka shiga ciki aka cinna wuta kana sai aka sake…
Read More
Ma’aunin talauci na Nijeriya

Ma’aunin talauci na Nijeriya

Assalam alaikum. Ina yi wa jaridar Blueprint Manhaja fatan alheri. Wani sabon rahoto ya tabbatar da cewa aƙalla ’yan Nijeriya miliyan 133 ne ke fama da talauci. Wannan na ƙunshe ne a cikin sabuwar ƙididdigar Talauci ta Nijeriya da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta fitar kwanan nan a Abuja. Sabuwar alƙalumman talauci na wakiltar kusan kashi 63 cikin 100 na al'ummar ƙasar. An gudanar da binciken tsakanin Nuwamba 2021 da Fabrairu 2022. Ambaliyar ruwa ta baya-bayan nan a faɗin ƙasar, wacce ta lalata gidaje da rayuwa da kuma nitsewar filayen noma a jihohi da dama na tarayyar ƙasar, mai…
Read More
Biyan ‘yan kwangila akan lokaci yana bunƙasa tattalin arzikin jihar Kano – Engr. Khalil

Biyan ‘yan kwangila akan lokaci yana bunƙasa tattalin arzikin jihar Kano – Engr. Khalil

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano An yi amanna cewa biyan ƴan kwangila akan lokaci yana inganta tattalin arzikin jihar Kano. Manajan Daraktan Kamfanin Gerawa Global, Engr. Abubakar Ibrahim Khalil ne ya bayyana hakan a lokacin da gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya kaddamar da titin kilomita biyar da aka gina a Gwarzo, wanda gwamnatin baya ta yi watsi da shi. Engr Abubakar Khalil ya kara da cewa, bayar da kwangiloli ga kamfanoni na cikin gida na rage rashin aikin yi a tsakanin matasan Kano da sauran al'umma, Kazalika ya yabawa Gwamnan Jihar Kano bisa yadda ya ke baiwa…
Read More
‘Yan Boko Haram 69 sun miƙa wuya ga rundunar MNJTF

‘Yan Boko Haram 69 sun miƙa wuya ga rundunar MNJTF

Daga SANI AHMAD GIWA a AbujaMayaƙan ƙungiyar Boko Haram 69 da ‘yan uwansu sun miƙa wuya ga Rundunar Haɗin Gwiwa ta Ƙasa da Ƙasa (MNJTF) a Kamaru da Nijar da ke yankin Tafkin Chadi.Babban jami’in yaɗa labarai na rundunar soji da ke N’djamena-Chad, Laftanar-Kanar Abdullahi Abubakar a wata sanarwa ya ce, ’yan tayar da ƙayar bayan sun miƙa wuya ne a tsakanin ranakun 1 zuwa 6 ga watan Yulin 2024, yayin da rundunar Operation Lake Sanity 2 ke ci gaba da samun nasara a kansu.Laftanar-Kanar Abubakar ya bayyana cewa, farmakin da sojojin Kamaru da Nijeriya ke kaiwa a Tafkin Chadi,…
Read More
Babu auren jinsi a ‘Yarjejeniar Samoa’ — Ƙungiyar Lauyoyi

Babu auren jinsi a ‘Yarjejeniar Samoa’ — Ƙungiyar Lauyoyi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta ce 'Yarjejeniyar Samoa' da gwamnatin ƙasar ta sa hannu a kai ba ta da wata alaƙa da auren jinsi da ake cece-kuce a kai.Shugaban NBA, Yakubu Maikyau, ya ce ƙungiyar na da hannu wajen sanya hannu kan yarjejeniyar Samoa kuma babu wani ɓangare na yarjejeniyar da ke da alaƙa da ’yan luwaɗi da maɗigo, ko auren jinsi (LGBTƘ).Shugaban na NBA ya ce ƙungiyar ta lura da ce-ce-ku-cen da ake a Nijeriya kan rattaɓa hannu da ƙasar ta yi kan yarjejeniyar Samoa wanda ake zargin an sharɗanta mata amincewa da…
Read More
A Nijeriya an samu kisan kai guda 1,702 a 2023

A Nijeriya an samu kisan kai guda 1,702 a 2023

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya ta bayyana cewa, an samu kashe-kashen kai har guda 1,702, garkuwa da mutane 2,149 da kuma laifuka 320 na fashi da makami a faɗin ƙasar a shekarar 2023.A wani rahoto da ƙungiyar ƙididdigar tattara bayanai ta fitar a ranar Juma’a 5 ga Yuli, 2024, ya nuna cewa yankin Arewa ta Tsakiya ne ya fi kowacce yawan al’amuran kisan kai, wanda ya kai 436 a shekara.A cikin shekarar da ta gabata, yankin Arewa maso Yamma ya samu laifukan kisan kai 417, yankin Arewa maso Gabas yana da 345, sannan Kudu maso Yamma ya…
Read More
Rikicin Masarautar Kano: APC ta sha alwashin koya wa NNPP darasi a 2027

Rikicin Masarautar Kano: APC ta sha alwashin koya wa NNPP darasi a 2027

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Jam’iyyar APC ta tabbatar da cewa jam’iyyar NNPP za ta faɗi warwas a zaɓen 2027 saboda matsayar da ta ɗauka kan rikicin masarautar Kano.A wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin a Abuja, shugaban jam’iyyar APC na jihar, Alhaji Abdullahi Abbas, ya bayar da hujjar cewa lamarin zai yi mummunar tasiri ga damar zaɓen NNPP, wanda hakan zai bai wa Shugaba Bola Tinubu nasara.Ya yi iƙirarin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ba shi da wani shiri na zama shugaban Nijeriya.A cewar Abbas, jam’iyyar APC a yanzu ta samu haɗin…
Read More
An kuɓutar da limamin coci bayan sati biyu da sace shi a Zamfara

An kuɓutar da limamin coci bayan sati biyu da sace shi a Zamfara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An sako Fafa Mikah Suleiman, Babban Limamin Cocin Katolika na St. Raymond da ke Damba, Gusau a Jihar Zamfara, bayan da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi tsawon makonni biyu.An tabbatar da sakin sa ne a ranar Lahadi, 7 ga Yuli, 2024, a cikin wata sanarwa da Pascal Salifu, Daraktan Sadarwa na Diocese na Katolika a Sokoto ya fitar.“Mun yi matuƙar farin cikin sanar da sakin Fr Mikah Suleiman, wanda aka yi garkuwa da shi ranar 22 ga watan Yuni, 2024,” inji sanarwar.“Mu na miƙa godiyar mu ga Allah da ya kiyaye shi da…
Read More