03
Jul
Daga EDITA Wata babbar kotun jiha da ke zamanta a Osun ta yanke wa wasu masu garkuwa biyar hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan samunsu da laifin sace wani mutum mai suna Alhaji Ibrahim Adamu, tare da kashe shi. An gurfanar da mutanen biyar a gaban alƙali bisa tuhume-tuhume da suka ƙunshi haɗa baki don yin garkuwa da mutumin da kuma laifin kisan kai, zargin da suka musanta a lokacin da aka fara gurfanar da su ranar 28 ga watan Oktoban 2021. Jaridar 'BBC Hausa', ta ruwaito cewa a lokacin zaman sauraron shari'ar, lauyan gwamnati, Faremi Moses, ya gabatar da…
