Labarai

‘Yan Sandan Kano na karɓar umurni daga wasu ɓoyayyun mutane – Gwamnatin Jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Jihar Kano ta nuna damuwa kan yadda jami'an 'Yan Sanda ke bijire wa karɓar umurni ta hanyar da doka ta tsara inda take zargin wasu mutane da ba huruminsu bane ke juya hukumar. Kwamishinan Shari'a kuma Antoni Janar na Jihar, Haruna Isa Dederi ya faɗi hakan a wani taron manema labarai inda ya ce gwamna Abba Kabir Yusuf shi ne shugaban harkar tsaron Jihar kuma ke da ikon umurtar dukkan hukumomin tsaron Jihar. Dederi ya ce, wasu mutane da ba a san ko suwaye ba suna bada umurni ga hukumar 'Yan Sanda inda ya bada…
Read More
Shugaban ƙaramar Hukumar Bursari ya nemi goyon bayan ‘yan adawa a Yobe

Shugaban ƙaramar Hukumar Bursari ya nemi goyon bayan ‘yan adawa a Yobe

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sabon Zaɓaɓɓen Shugaban ƙaramar Hukumar Bursari a jihar Yobe, Hon. Lawan Bukar Guba, ya yi kira ga ‘yan takarar jam’iyyun adawa da suka gudanar da zaɓen da shi da su ba shi haɗin kai don ciyar da ƙaramar hukumar gaba. Ku tuna cewa Guba yana ɗaya daga cikin shugabannin ƙananan hukumomin jam’iyyar APC 17 da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar ta ayyana a matsayin waɗanda suka lashe zaben ƙananan hukumomin da aka gudanar a jihar Yobe ranar Asabar. A wani kira na haɗin kai, Guba ya gayyaci ‘yan takarar jam’iyyar adawa da…
Read More
Idris ya roƙi NLC ta karɓi albashin da ba zai gurgunta tattalin arziki ba

Idris ya roƙi NLC ta karɓi albashin da ba zai gurgunta tattalin arziki ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya yi kira ga ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC) da ta amince da mafi ƙarancin albashi na ƙasa wanda ba zai gurgunta tattalin arzikin ƙasa ba, kuma ya kai ga korar ma’aikata da dama.Idris ya yi wannan roƙon ne a lokacin da yake bude taron ƙungiyar limaman Kirista ta Charismatic Bishops of Nijeriya na 2024 a Abuja ranar Laraba. A cikin wata sanarwa da Mataimaki na Musamman ga Ministan kan Harkokin Yaɗa Labarai, Rabi’u Ibrahim ya fitar, an ruwaito cewa Idris ya jaddada buƙatar samar…
Read More
An bankaɗo badaƙalar ɗaukar aiki a wasu ma’aikatun gwamnatin Kano

An bankaɗo badaƙalar ɗaukar aiki a wasu ma’aikatun gwamnatin Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar ƙorafe-ƙorafen Jama’a da Yaƙi da Cin Hanci ta ƙasa da Rashawa reshen Jihar Kano ta kama wasu mutane biyu tare da gayyatar wasu sakatarorin dindindin guda uku domin amsa tambayoyi kan badaƙalar sayar da fom ɗin aiki a Ofishin Shugaban Ma’aikata. Shugaban hukumar, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa a Kano ranar Laraba cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike don gano tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a badaƙalar. Ya ce, tuni dubban masu neman aiki damfarar ta shafa.“Bincike na farko ya gano…
Read More

Rikicin Masarautar Kano – Kotu za ta yi hukunci kan ƙarar soke dokar tsarin Masarautun Jihar na 2024

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata babbar kotu a Jihar Kano ta ayyana ranar Alhamis, 20 ga watan Yuni, 2024 a matsayin lokacin da za ta yanke hukunci kan sabuwar dokar Masarautu da gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf ya ƙirƙira. Mai Shari'a Abdullahi Muhammad Liman ya bada sanarwa kan ƙarar wanda Sarkin Dawakin Masarautar, Aminu Baba Ɗan Agundi ya shigar kan sauya dokar zuwa yadda tsohuwar gwamnatin Jihar ta tsara. Hakan na zuwa ne biyo bayan da Sarkin Dawakin ya ce Gwamnatin Jihar ta ki girma 'yancinsa na ɗan ƙasa inda yake neman kotun da ta tabbatar da adalci kan rikicin…
Read More

Zamfara ta fara biyan sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatanta

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da ake cigaba da shirye-shiryen bikin babbar sallah, gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya ƙaddamar da fara biyan naira dubu 30 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikata a Jihar. Jawabin ya fito ne daga bakin mai magana da yawunsa, Sulaiman Bala Idris cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a inda ya ce sun yi haka ne sakamakon cika alƙawarin da suka yi tsakaninsu da wakilan ƙungiyar ƙwadago na Jihar a watan da ya gabata. Sanarwar ta ce, tuni dai ma'aikata suka fara karɓar albashi kan sabon tsarin daga ranar 12…
Read More

Gwamnatin Tarayya ta sanar da ranakun hutun sallah

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Tarayya ta ware ranakun Litinin da Talata a matsayin lokacin hutun bikin Babbar-sallah a faɗin ƙasar. Babbar sakatariyar ma'aikatar harkokin cikin gida, Dakta Aishetu Gogo Ndayako ta faɗi hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar juma'a. Dakta Aishetu ta ce, ministan ma'aikatar, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya inda ya ce yana mai taya al'ummar musulmi murnar zagayowar wannan lokaci mai albarka. Ya kuma yi kira ga al'ummar musulmi da su cigaba da kasancewa masu son zaman lafiya, da kyautatawa juna, da sadaukarwa tare da yin addu'o'in samun zaman…
Read More

Sufeta Janar ya dakatar da ƙarin girma na musamman a hukumar ‘Yan Sanda

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Sufeta Janar na hukumar 'Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya sanar da dakatar da tsarin ƙarin girma na musamman da ake yi wa jami'ansu inda ya ce hakan na haifar da rauni da kawo cikas ga ƙoƙarinsu wajen gudanar da ayyukansu. Kayode ya bayyana hakan ne a yayin bikin girmama manyan jami'ai 15 da hukumar ta ƙara wa girma a Abuja. Kayode, ya bayyana alhininsa kan yadda wasu ma'aikatan ke kamun ƙafa wajen neman waɗannan muƙaman, dan haka ya ce duk wanda aka kama da yunkurin haka, to za'a hukunta shi. Ya kuma ƙara da cewa,…
Read More
Yadda sojoji suka halaka ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Yadda sojoji suka halaka ƙasurgumin ɗan bindiga, Buharin Yadi a Kaduna

Daga MADHI M. MUHAMMAD Rundunar Sojojin Nijeriya sun bayyana cewa, sun kashe wani ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan arewa maso yammacin ƙasar mai suna Kachalla Buhari Alhaji Halidu da aka fi sani da Buharin Yadi da wasu yaransa fiye da 30.Cikin wata sanarwa kwamishinan harkokin tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar ya ce lamarin ya faru ne sakamakon wani gagarumin farmaki da dakarun rundunar 'Sector 6 Operation Whirl Punch' suka kai a kan iyakar Kaduna da KatsinaYa ƙara da cewa, Manjo Janar MLD Saraso ya jagoranci farmaki kan Yadi da mayaƙansa bayan samun rahotannin sirri da…
Read More
Dangote ya fallasa masu yunƙurin dakatar da matatarsa

Dangote ya fallasa masu yunƙurin dakatar da matatarsa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Mamallakin rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote, ya bayyana cewa ƙungiyoyin masu aikata laifuka na cikin gida da waje, waɗanda ya bayyana a matsayin “mafiya”, suna yunƙurin yin zagon ƙasa a aikin matatar man da ya kai Dala Biliyan 19 a Legas.A yayin da ya ke jawabi a taron shekara-shekara na Afreximbank, Aliko Dangote ya ce, ƙungiyar mafia masu safarar mai sun fi ƙarfin masu safara miyagun ƙwayoyi, waɗanda su ne ke neman riƙe masa masana'anta.“To, na san cewa akwai fitina. Amma ban san cewa mafiyan man fetur sun fi ƙarfin mafiyan ƙwayoyi ba. Na tabbatar da…
Read More