Labarai

Ƙananan hukumomi: Kotun ƙoli ta sa ranar sauraron ƙarar Gwamnatin Tarayya

Ƙananan hukumomi: Kotun ƙoli ta sa ranar sauraron ƙarar Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kotun ƙoli ta ajiye hukunci a gaban gwamnatin tarayya kan gwamnonin jihohi 36 da ke neman cikakken cin gashin kansu ga ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan.Mai shari’a Garba Lawal a ranar Alhamis ya bayyana cewa za a sanar da ɓangarorin da ke cikin lamarin da zarar an yanke hukunci. Ya sanar da jingine hukuncin ne bayan da kwamitin mutum bakwai na Kotun ƙoli ya amince da matakin da babban lauyan gwamnatin tarayya AGF, Prince Lateef Fagbemi, SAN, ya shigar a madadin gwamnatin tarayya, da na gwamnonin jihohi 36.A zaman da aka yi ranar…
Read More
Kotu ta sallami manyan masu ruwa da tsaki na Binance

Kotu ta sallami manyan masu ruwa da tsaki na Binance

Daga Karofi Usman Babban kotun Ƙasa da ke zamanta a Abuja ta sallami Tigran Gambaryan, dan shekara 39 ɗan asalin ƙasar Amurka da kuma Nadeem Anjarwalla waɗanda ake zargi da rashin biyan haraji. Dukkansu masu ruwa da tsaki a kafar da ake hada hadar kirifto wato Binance wanda gwamnatin Najeriya ke ƙara ta hannun hukumar FIRS a kan rashin biyan haraji. Duk da cewa Binance ba tada wakili na doka a Najeriya, bai hana an karanta tuhume tuhemen ga Gambaryan ba.Mai wakiltar shi yace wanda yake wakilata ba a bashi tuhumar ba hannu da hannu, don haka bai kamata a…
Read More

Rikicin masarauta: Lauyoyin Gwamnatin Kano sun fice daga kotu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Bayanan da ke fitowa daga cikin Babbar Kotun Tarayya a Kano da ke sauraron ƙarar da ake yi kan rikicin Masarautar Kano sun nuna cewa, lauyoyin Gwamnatin Jihar Kano da Majalisar Dokokin Jihar sun fice daga zauren kotun. Blueprint Manhaja ta gano cewa, wannan ya biyo bayan gabatar da takardar ɗaukaka ƙara da suka gabatar wa alƙalin kotun, Liman Muhammad ne kan hukuncin da ya yanke a jiya Alhamis, inda ya ƙi amincewa. Lauyoyin sun ɗaukaka ƙara ne bisa hukuncin da kotun ta yanke na huruminta kan sauraron ƙarar. To amma, Alƙali Liman ya ƙi yarda…
Read More

Ba mu amince da wasan kwaikwayon Gwamnatin Zamfara ba – Wasu ‘yan kishin Jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wasu masu fafutukar zaman lafiya da cigaban al'umma a Zamfara sun yi kira ga gwamnan Jihar, Dauda Lawal da ya daina siyasantar da mulkin 'yan Jihar tare da mayar da hankali wajen ayyukan da ya alƙawuranta wa mutane. Jaridar 'Daily Post' ta ruwaito cewa, ƙungiyar ta buƙaci gwamnan da ya bayyana wa al'ummar Jihar jadawalin nasarorinsa cikin shekara guda da yake kan karagar mulki. A cikin satinnan ne shuwagabanni a matakai daban-daban kama daga kan shugaban ƙasa zuwa gwamnoni suka bayyana ire-iren nasarorin da suka samu a yayin da suke bikin cikar shekara ɗaya a kan…
Read More

Har yanzu Aminu Ado Bayero na da ikon faɗa-a-ji – Kotu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wata babbar kotu a Jihar Kano, ta ce har yanzu sarki Aminu Ado Bayero na riƙe da kambun sarautar dake nuna cewa yana da ikon faɗa-a-ji duk da cewa gwamnatin Jihar ta fitar da sanarwar rusa tsarin masarautun da tsohuwar gwamnati ta yi a baya. Mai Shari'a Liman Mohammed ya bayyana haka jim-kaɗan bayan wata sanarwa da ta fito daga wata kotun Jiha sakamakon ƙarar da gwamnatin Jihar take kai tana mai cewa Sarki Ado da wasu sarakuna huɗu basu da hurumin amsa sunayen sarakuna tunda gwamnatin Jihar ta soke tsarin masarautunsu da aka yi a…
Read More

Ba za mu yi zaman sulhu da ‘yan bindiga ba – Gwamnan Zamfara

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada cewa gwamnatinsa ba zata yi tattaunawar sulhu da ƴan bindigar da suka addabi zaman lafiya a Jihar ba. Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a wani tattakin neman zaman lafiya da wasu matasa suka shirya a Jihar inda ya ce suna cigaba da ƙoƙarin bin hanyoyin da suka dace wajen ganin an samu zaman lafiya a dukkan sassan Jihar. Gwamnan ya kuma yaba wa matasan da suka shirya tattakin yayin da ake gudanar da bikin demokradiyya inda yayi kira da su bada gudunmawa wajen tabbatar da an samu…
Read More

Adadin masu kwalara a Najeriya na cigaba da ƙaruwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Wani rahoto na musamman da jaridar BBC ta fitar, yace hukumar hana yaɗuwar cutuka ta ƙasa, NCDC tana sanar da al'umma cewa adadin masu kamuwa da cutar kwalara na ƙaruwa a faɗin Najeriya ganin yadda damuna ke ƙara ƙamari. Rahoton yace daga watan Janairu zuwa Yunin shekarar 2024, an samu jimillar mutum 1,141 da ake zargi da kamuwa da cutar, da 65 da aka tabbatar sun kamu da ita, da kuma 30 da suka mutu a ƙananan hukumomi 96 na Jihohi 30 sakamakon ɓullar cutar. A kwanannan ne aka samu ɓullar cutar a Jihar Legas lamarin…
Read More
An zargi Ministan Kimiyya da jabun takardun NYSC

An zargi Ministan Kimiyya da jabun takardun NYSC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ana zargin ministan Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Geoffrey Nnaji da laifin yin takardar bautar ƙasa (NYSC) ta jabu.Rahoton da Peoples Gazette ta fitar wanda ya bankaɗo wani aikin damfara da ministan ya yi ya kuma sanya hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS cikin wani rufa-rufa mai ban mamaki.Ku tuna cewa an tabbatar da Geoffrey Nnaji a matsayin minista daga jihar Enugu a ranar 7 ga watan Agusta, 2023, tare da wasu mambobin majalisar ministoci 44, bayan naɗin da majalisar dattawa ta gabatar a ranar 7 ga Yuli, 2023.Daga nan aka naɗa shi…
Read More

Gaisuwar ‘Dobale’ na yi a ranar demokraɗiyya: Shugaba Tinubu

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya magantu kan tuntuɓe da ya yi yayin hawa motar zagaye a ranar bikin cikar demokradiyya shekaru 25 ganin yadda ɗaukar ta karaɗe shafukan sada zumunta da sauran gidajen jaridu. A lokacin da yake magana wajen cin abincin bikin demokraɗiyya a daren Laraba a fadar shugaban ƙasa, Tinubu cikin raha yace, mutane sun gagara fahimtar rawar waƙar 'Buga' ce ko kuma gaisuwar al'ada ta 'Idobale' ce ya yi a lokacin aukuwar lamarin. Shugaba Tinubu, ya ƙara da cewa, hakan na nuna farin cikinsa ga ranar demokradiyya da kuma girmama al'adar ƙabilarsa ta…
Read More

Johnathan ya jinjina wa gwamnan Edo kan 70,000 mafi ƙarancin albashi a Jiharsa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Ebele Jonathan ya yaba ma gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki kan amincewa da biyan naira dubu saba'in a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan Jiharsa. Ya faɗi haka ne a ranar Laraba yayin hira da manema labarai a lokacin ƙaddamar da buɗe sabon sakatariyar ma'aikata a Benin, babban birnin Jihar. Johnathan ya ce, wannan wani mataki ne da zai inganta walwala da jin daɗin al'ummar Jihar da kuma gwamnatinsa. Goodluck ya ƙara da cewa kasancewarsa jajirce kuma mai hangen nesa ne suka sa ya yi wannan babban abun a yaba duk…
Read More