Labarai

Tinubu ya tsige manyan jami’an gwamnati guda biyu

Tinubu ya tsige manyan jami’an gwamnati guda biyu

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya tsige Mataimakin Shugaban  hukumar kare hakkin masu amfani da kayayyaki da aka fi sani da FCCPC a takaice, Mr. Babatunde Irukera. Kazalika, Tinubu ya tsige Babban Daraktan Hukumar Kula da Kamfanonin Gwamnati (BPE), Mr. Alexander Okoh. Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Chief Ajuri Ngelale ne ya bayyana tsigewar cikin sanarwar da ya fitar  jiya Litinin, inda ya ce matakin tigewar ya fara aiki ne nan take. Sanarwar ta kara da cewa, an umarci jami’an da lamarin ya shafa da su mika ragamar gudanar da ofisoshinsu ga jami’i mafi girma a bakin aiki a ma’aikatarsu…
Read More
Tinubu ya dakatar da Ministar Jinƙai, Betta Edu kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati

Tinubu ya dakatar da Ministar Jinƙai, Betta Edu kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarni kan a dakatar da Ministar Jinkai da Yaki da Talauci, Dokta Betta Edu daga mukaminta na minista. Kuma dakatarwar ta fara aiki ne nan take, kamar yadda Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Ajuri Ngelale ya sanar a ranar Litinin. Sanarwar ta ce Tinubu ya dakatar da Betta ne domin kare mutuncin gwamnatin kasa da kuma aiki da gaskiya. Ta kara da cewa, Tinubu ya bai wa Shugaban EFCC umarni kan gudanar da cikakken bincike a kan Betta bisa zargin da ake yi mata na karkatar da wasu makudan…
Read More
Za a daƙile layukan Glo daga barin kiran MTN saboda rashin biyan haraji – NCC

Za a daƙile layukan Glo daga barin kiran MTN saboda rashin biyan haraji – NCC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Kula da Kafafen Sadarwa ta Nijeriya (NCC), ta bayyana cewa akwai yiwuwar masu amfani da layin sadarwa na kamfanin Globacom su fuskanci kwarya-kwaryar dakikewa wajen kiran layukan sadarwa na kamfanin MTN. Hukumar ta bayyana haka ne a sanarwar da ta fitar ran Litinin wadda ta samu sa hannun Daraktan Sashen Hulda da Jama'a, Reuben Muoka. NCC ta ce za a fuskanci hakan ne biyo bayan rashin biyan harajin sadarwa daga bagaren Globacom. Hukumar ta kara da cewa ta ba da izinin a katse sadarwar kamfanin Globacom daga MTN Nigeria Communications Plc. A cewar Hukumar, “An sanar…
Read More
Hajjin 2024: Nijeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna

Hajjin 2024: Nijeriya da Saudiyya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna

Daga BASHIR ISAH An cimma yarjejeniyar aikin Hajjin bana tsakanin Gwamnatin Nijeriya da takwararta ta kasar Saudiyya. A ranar Lahadin da ta gabata bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar a Jedda, kasar Saudiyya, inda Ministan Harkokin Wajen Nijeriya, Ambasada Yusuf Maitama Tuggar ya wakilci Gwamnatin Nijeriya. Yayin wani taron ban gishiri, in ba ka manda da suka yi tare da Ministan Hajji da Umarah na Saudiyya, Dokta Taofiq bin Fawzan AlRabiah, Tuggar ya bayyana cewa ayyukan Hajjin 2024 za su gudana ne bisa sabbin dokokin da aka gindaya domin tabbatar da komai ya gudana a kan lokaci. Tattaunawar tasu…
Read More
Airtel Afirka ta yi sabon shugaba

Airtel Afirka ta yi sabon shugaba

 Daga AMINA YUSUF ALI Airtel Afirka ta ba da sanarwar ritayar  Babban Jami'in Zartaswarsa, Olusegun Ogunsanya, wanda zai akiye aiki a ranar 1 ga Yuli, 2024. Ogunsanya, ya fara aiki da kamfanin  Airtel a shekarar  2012, shi yake kula da harkokin sadarwa na Nijeriya da kamfanin hada-hadar kudi na tsahon shekaru tara kafin a yi masa nadin  Babban Jami'in Zartaswar rukunin kamfanonin a cikin shekarar 2021. Saboda saninsa da yadda Afirka take da gidewarsa waen rarraba kaya a cikinta, ya kasance a lokacin da yake shugabantar kamfanin ya samar da bunkasar kudin shiga masu tarin yawa tsahon shekaru, sannan ya…
Read More
Tsaro: Matasan Arewa sun jinjina wa Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher

Tsaro: Matasan Arewa sun jinjina wa Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher

Daga BASHIR ISAH Matasan Arewa sun jinjina wa Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa, dangane da kokarin da yake yi wajen kare rayukan ‘yan kasa da kuma dukiyar gwamnati. Matasan sun yi wannan yabo ne ta bakin kungiyarsu ta Northern Youths Association of Nigeria (NYAN) cikin wata sanarwar manema labarai da kungiyar ta fitar ranar Asabar a Bauchi. Matasan sun ce, “Mun yaba da kokari da jajircewarsa wajen maido da zaman lafiya a Nijeriya. Hakika ya dora rundunar sojin Nijeriya kan turbar da ta dace. Shugaban kungiyar,  Ambasada Godiya T. Adams Bogoro, ya bayyana cewa, bayan nazari da lura,…
Read More
Yadda rikita-rikitar digiri ɗan jabu ta ruɗa Nijeriya

Yadda rikita-rikitar digiri ɗan jabu ta ruɗa Nijeriya

*Badaqalar ta shafi jami’o’i 78 *An cafke jami’ai bisa zargin hannunsu *Hukumar NYSC ta farga Daga MAHDI M. MUHAMMAD A farkon makon nan ne Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta dakatar da amincewa da takardar shaidar digiri daga wasu jami’o’in kasashen waje da ma masu cibiya a cikin gida. Umarnin na qunshe ne a cikin wata sanarwa ne da aka fitar a ranar Talata, 2 ga Janairu, 2023, mai dauke da sa hannun Augustina Obilor-Duru a madadin Daraktan Yada Labarai Da Hulda Da Jama’a Na Ma’aikatar Ilimi Ta Tarayya. Gwamnati ta koka da cewa "wasu 'yan Nijeriya suna amfani da hanyoyin da…
Read More
Zargin karkatar da N585m:  Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan Betta Edu

Zargin karkatar da N585m:  Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan Betta Edu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ba da umarnin a binciki Ministan Jinkai da Yaki da Talauci, Dokta Betta Edu, dangane da karkatar da Naira miliyan 585 da aka ware don ba da tallafin rage radadin rayuwa zuwa wani kebabben asusu. Bayanin haka na kunshe ne cikin sanarwar da Ministan Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya fitar a ranar Lahadi. A cewar Idris, “Gwamnatin Tarayya, karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na aiki ne da gaskiya ga jama’a tare da tabbatar da an zuba kudaden gwamnati a inda ya dace don magance matsalolin bukatun ‘yan Nijeriya. “Duba…
Read More
Gwamna Lawal ya ƙaddamar da rabon kayan aiki ga manoma a Zamfara

Gwamna Lawal ya ƙaddamar da rabon kayan aiki ga manoma a Zamfara

*Za a gina makarantu tsangaya a mazabun sanata Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kaddamar da raba kayayyakin aiki ga manoma a shiyyar Zamfara ta Yamma. Shirin wanda ke mazaunin bangare na tayar da komadar da annobar Korona ta haddasa wa Nijeriya da kuma yaukaka tattalin arziki karkashin Shirin FADAMA III, an kaddamar da shi ne a yankin Karamar Hukumar Gummi da ke jihar. Mai magana da yawun Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana a cikin sanarwar da ya fitar cewa, Gwamna Lawal ya kaddamar da shirin rabon kayayyakin ne hadi da gina Makarantar Tsangaya irin ta…
Read More
‘Yan bindiga sun halaka ‘yan kasuwa takwas a Katsina

‘Yan bindiga sun halaka ‘yan kasuwa takwas a Katsina

Daga Umar Garba a Katsina ‘Yan bindiga masu tarin yawa dauke da muggan makamai sun tare ayarin motocin 'yan kasuwa inda suka kashe wasu mutane takwas a lokacin da suka kai wani hari kan ayarin da ke dawowa daga kasuwar garin Yantumaki da ke karamar hukumar Danmusa a jihar Katsina. A duk mako 'yan kasuwar kan yi ayari don tafiya cin kasuwa inda suke samun rakiyar jami'an tsaro, sai dai a wannan karon 'yan ta'addar sun yi wa jami'an tsaron kwanton bauna inda suka jikkata wasu daga ciki suka halaka wasu 'yan kasuwar.  Shugaban kungiyar direbobi a yankin, Kabiru Dangaye,…
Read More