07
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A cikin makon nan ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Shugabar Hukumar Shirin Bada Tallafi da Dogaro da Kai, wato ‘National Social Investment Programme Agency’ (NSIPA), inda a gefe guda kuma tun a makon jiya Hukumar EFCC mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati ta mika goron gayyatarta ga tsohuwar Ministar Jinkai da Agaji a lokacin tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari, wato Sadiya Farouq kan zargin ta da hannu a badakalar Naira biliyan 37.1. A bangaren Halima Shehu ta hukuma NSIPA, wacce ke karkashin Ma’aikatar Jinkan, bayanai sun ce hukumar…
