Labarai

‘Yan bindiga sun sako Shugaban Karamar Hukumar Akwanga bayan biyan kuɗin fansa

‘Yan bindiga sun sako Shugaban Karamar Hukumar Akwanga bayan biyan kuɗin fansa

Daga BASHIR ISAH Shugaban Karamar Hukunar  Akwanga a Jihar Nasarawa, Safiyanu Isah Andaha, ya shaƙi iskar 'yanci bayan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi. An sako shi ne tare da  abokinsa, Adamu Custom da wasu mutum biyu wadanda aka yi garkuwa da su a lokaci guda ranar Litinin da daddare. MANHAJA ta kalato cewa, sai da aka biya fansar Naira miliyan 10 kafin aka sako wadanda lamarin ya shafa. Majiya da ta bukaci a dakaya sunanta ta bayyana cewa, an saki wadanda aka yi garkuwa da su din ne a bayan wani gidan mai da ke hanyar Bayan…
Read More
Gwamnati ta yi watsi da shirin karin kudin wutar lantarki

Gwamnati ta yi watsi da shirin karin kudin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta yi tsayin daka kan kin amicewa da karin farashin wutar lantarki kamar yadda kamfanin samar da lantarki na Nijeriya ya bukata. Ministan Makamashi, Adebayo Adelabu, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin. Ministan ya jaddada kudurin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da wadatacciyar wutar lantarki a kasa. Adelabu ya kara da cewa, “Rashin damarmaki na ci gaba da zama babban kalubalen da fannin lantarki ke fuskanta. “Muna yin nazari kan tsarin aiwatar da jadawalin kuɗin fito tare da tabbatar da ci…
Read More
Hannutu Musawa ta buƙaci a tallafa wa jarumi Zack Orji kan jinyarsa

Hannutu Musawa ta buƙaci a tallafa wa jarumi Zack Orji kan jinyarsa

Daga BASHIR ISAH Ministar Kirkire-kire da Al’adu, Barista Hannatu Musawa, ta yi kira ga masu hali a Nijeriya da su dubi Allah su taimaka wa jarumin masa’antar Nollywood, Zack Orji, bisa jinyar da yake yi a halin yanzu. A ranar Litinin da ta gabata aka yi wa jarumin aiki na lalurar da yake fama da ita mai nasaba da kwakwalwa. Wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba mai dauke da sa hannun hadimarta, Nneka Ikem Anibeze, ta ce Hannatu ta yi wannan roko ne bayan da ta ziyarci jarumin a asibitin da yake jinya da ke yankin Wuse a…
Read More
Zargin N17bn: Tinubu ya bada umarnin dakatar da binciken da ake yi wa Halima Shehu

Zargin N17bn: Tinubu ya bada umarnin dakatar da binciken da ake yi wa Halima Shehu

Daga BASHIR ISAH Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bada umarni kan gaggauta dakatar da binciken da ake yi wa Shugabar shirin NSIPA, Halima Shehu. Kazalika, Tinubu ya amince da nadin Dokta Akindele Egbuwalo don maye gurbin Halima a matsayin mukaddashi. Idan za a iya tunawa, ‘yan watanni da suka gabata ne gwamnatin Tinubu ta nada Halima shugabancin NSIPA. Tun farko, rahotanni sun nuna hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta tsare Halima a Talatar da ta gabata. An tsare ta ne jim kadan bayan da Shugaba Tinubu ya dakatar da ita daga mukaminta bisa zargin tura kudaden NSIPA Naira…
Read More
Hizbah za ta fara kamen mabarata a titunan Katsina

Hizbah za ta fara kamen mabarata a titunan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Hukumar Hizbah a Jihar Katsina ta bayyana cewar bada jimawa ba za ta fara kamen masu bara a duk fadin jihar. Shugaban hukumar Mallam Aminu Usman ( Abu Ammar) ne ya bayyana haka. A cewar shi gwamnatin jihar na yin dukkan mai yiwuwa don kawar da mabarata daga titinun jihar. "Bara ba ta daga cikin addini ta na kuma bata sunan addini da al'umarmu." Inji shi. Ya kuma bayyana cewar dokar da kafa hukumar Hizbah a jihar ta ba su damar shiga lungu da sako don cafko masu bara. "Idan mun kama su za mu…
Read More
An yi jana’izar mutane takwas da ‘yan bindiga suka hallaka a Katsina

An yi jana’izar mutane takwas da ‘yan bindiga suka hallaka a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wata dabar 'yan ta'adda dauke da muggan makamai sun bude wa 'yan kasuwa takwas wuta, kusa da kauyen babangida bayan da suka dawo cin kasuwar Jibiya dake karamar hukumar Jibiya a jihar Katsina. Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar ya tabbatar da faruwar lamarin. 'yan ta'addar sun kuma jikkata wasu karin mutane hudu a yayin da wasu biyu suka vata tun bayan harin da aka kai jiya Lahadi da dare. Wadanda aka kashe din mazauna kauyen 'Yan gayya ne a karamar hukumar ta Jibiya dake makota da Zurmi ta jihar Zamfara. Rahotanni sun bayyana cewar…
Read More
‘Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma a Nasarawa

‘Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma a Nasarawa

Daga BASHIR ISAH Rahotanni daga yankin Karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa sun ce, 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban hukumar, Mr. Safiyanu Isa Andaha. Hadimin Gwamnan jihar kan lamurran kananan hukumomi da masarsutu, Haruna Kassimu ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an sace Safiyanu Isa ne a kauyen Ningo da ke hanyar Akwanga - Andaha a yankin. Ya kara da cewa, an sace shugaban karamar hukumar ne tare da wani mai suna Alhaji Adamu Tanko Custom da misalin karfe 8:30 na daren Litinin da ta gabata. Kazalika, Kassimu ya ce jami'an tsaro sun dukufa bincike…
Read More
Tinubu ya rattaɓa hannu kan kasafin 2024

Tinubu ya rattaɓa hannu kan kasafin 2024

Daga BASHIR ISAH    Shugaban Kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu kan kasafin 2024 na Naira tirilyan 28.7 wanda hakan ya sanya  kasafin zama doka. A ranar Litinin da ta gabata Tinubu ya sanya wa kasafin hannu da misalin karfe 2:00 na rana a ofishinsa, inda aka shirya kwarya-kwaryar biki wanda ya samu halartar manyan jami’an gwamnatinsa. Mahalarta bikin sun hada da Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio; Shugaban Majalisar Wakilai, Hon Tajudeen Abbas; Ministan Kudi, Mr Wale Edun. Sauran sun hada da Ministan Kasafi da tsare-tsaren Tattalin Arziki, Alhaji Atiku Bagudu; Mai bai wa Shugaban Shawara Kan Sha’anin Tsaro (NSA),…
Read More
KASSOSA ta karrama Mustapha Bala Dawaki bisa gudunmuwa da yake bayarwa

KASSOSA ta karrama Mustapha Bala Dawaki bisa gudunmuwa da yake bayarwa

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Honarabul Mustapha Bala Dawaki ya bayyana karramawar da kungiyar tsaffin dalibai na Makarantun Kimiyya ta Kasa (KASSOSA) ta yi masa a yayin taronta na shekara da aka gudanar a jami'ar Bayero  rantsar da sabbin shugabaninta da cewa abin godewa ne ga Allah kuma sun yi duba ne da irin abubuwa da akai musu na alkhairi wajen kawo cigaba a makarantunsu na kimiyya. Tsohon dan majalisar mai wakiltar Dawakin Kudu da Warawa ya ce irin abubuwa na gine-gine da hanyoyi sa wutar lantarki da ruwa da bunkasa harkar iliminsu ita tasa suka ga cancantar karramashi a…
Read More
ACF za ta ci gaba da ƙoƙarin inganta zaman lafiya – Ƙungiyar Matasan Arewa

ACF za ta ci gaba da ƙoƙarin inganta zaman lafiya – Ƙungiyar Matasan Arewa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kungiyar Matasan Arewa ta bayyana amincewa da shugabancin Kungiyar Tuntuva ta Arewa (ACF), tare da jaddada cewa kungiyar ta shirya tsaf domin samar da zaman lafiya, hadin kai da samar da wadata a fadin Arewacin Nijeriya baki daya bisa ingantaccen tsari. Gamayyar kungiyoyin matasan Arewa, kwamitin hadin gwiwa na kungiyoyin matasan Arewa (JACOM), sun yi amanna da kungiyar tuntuba ta Arewa (ACF) domin ganin an samu sauyi tare da sauya akalar shugabancin kungiyar ta fannin zamantakewa da al’adun Arewacin Nijeriya. Kungiyar Matasan Arewa, a wata sanarwa da Murtala Abubakar, shugaban JACOM da Israel Musa, Sakatarenta suka…
Read More