Labarai

Gwamna Dauda Lawal ya yi sabbin naɗe-naɗe a ɓangaren raya birane

Gwamna Dauda Lawal ya yi sabbin naɗe-naɗe a ɓangaren raya birane

Gwanan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya naɗa sabon Shugaban Hukumomi tare da ɗaukar ƙarin ma'aikata don Sabunta Aikin Raya Birane a jihar. Naɗin ɓangare ne na matakin Gwamnatin Zamfara ta ɗauka wajen gudanar da ayyukan gina jihar da tara mata kuɗin shiga. Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata, Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya ce Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Abubakar Nakwada ne ya sanar da naɗin a Gusau, babban birnin jihar. Ya ƙara da cewa, naɗin ya haɗa da na sakatarorin hukumar tattara bayanan yanayi ta jihar (ZAGIS) da ta raya birane (ZUREPB). “Gwamnan ya…
Read More
Atiku ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe

Atiku ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe

Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP a babban zaɓen 2023, Abubakar Atiku, ya garzaya Kotun Ƙoli don kotun ta yi watsi da hukuncin da Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa ta yanke a ranar 6 ga Satumba. A hukuncin da ta yanke, Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen ta ce Bola Ahmed Tinubu shi ne wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a babban zaɓen da ya gabata. Sai dai, Atiku ya ce kotun ta tafka kuskure a hukuncin da ta yanke ranar Talata ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a Haruna Simon Tsammani. Ƙarar da Atiku ya ɗaukaka ta hannun babban lauyansa, Chief Chris…
Read More
Sau uku babban layin wutar lantarki na ƙasa na ɗaukewa ƙasa da makonni biyu

Sau uku babban layin wutar lantarki na ƙasa na ɗaukewa ƙasa da makonni biyu

Babban layin wutar lantarki na ƙasa ya sake ɗaukewa wanda hakan ya yi sanadiyar jefa sassan ƙasa cikin duhu. Wannan shi ne karo uku a ƙasa da makonni biyu da babban layin lantarkin ya ɗauke, don kuwa irin haka ya faru sau biyu kimanin mako guda da ya gabata. A cewar masu kula da cibiyar lantarki ta ƙasa, a ranar Talata aka samu koma bayan ƙarfin wutar lantarkin da ake samarwa daga megawat 3,594.60 zuwa megawat 42.7. Sun ce ya zuwa lokacin da lamarin ya faru, cibiyar lantarki da ke Delta kaɗai ke da wuta mai ƙarfin megawat 41.00, yayin…
Read More
Majalisar Tarayya: Kotu ta tabbatar da nasarar ɗan takarar NNPP a Kano

Majalisar Tarayya: Kotu ta tabbatar da nasarar ɗan takarar NNPP a Kano

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Majalisar Tarayya da ta jiha, ta tabbatar da nasarar ɗan takarar Jam'iyyar NNPP, Mudassir Zawachiki, a matsayin wakilin al'ummar Kumbotso a Jihar Kano a Majalisar Wakilai ya Tarayya. Kwamitin alƙalan ƙarƙashin jagorancin Mai Shari'a L. B. Owolabi, ya yi watsi da ƙarar da Sagir Abdulkadir-Panshekara na Jam'iyyar APC ya shigar inda yake ƙalubalantar nasarar Zawachiki a zaɓen da ya gudana ran 18 ga Maris, 2023. Kotu ta ce mai ƙarar ba shi da hurumi kuma ya kasa gabatar da hujjoji kan cewa an yi arigizon ƙiri'u, tada zaune tsaye da amfani da takardun bogi yayin zaɓen.…
Read More
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro takwas a Imo

Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaro takwas a Imo

Bayanan da muka samu daga Jihar Imo na nuni da cewa 'yan bindiga sun kashe jami'an tsaro takwas a jihar a ranar Talata. Jaridar News Point Nigeria ta rawaito cewa, waɗanda lamarin ya shafa sun haɗa da sojoji da 'yan sanda da jami'an sibul difens. Majiyar tamu ta ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Umualumaku da ke yankin Ƙaramar Hukumar Ehime Mbano a jihar. Ta ce 'yan bindigar sun yi wa jami'an kwanton ɓauna ne a cikin motocinsu inda suka buɗe musu wuta kana daga bisani suka banka musu wuta. Majiyar ta ƙara da cewa babu ko mutum guda…
Read More
Shari’ar Gwamnan Kano: Kotu ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci

Shari’ar Gwamnan Kano: Kotu ta ayyana ranar da za ta yanke hukunci

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Kano ta ayyana ranar Laraba ta wannan mako a matsayin ranar da za ta yanke hukunci kan shari'ar da ke gabanta inda Jam'iyyar APC ke ƙalubalantar nasarar da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jam'iyyar NNPP ya samu a zaɓen gwamnan jihar da ya gabata. A ranar Litinin da ta gabata Kotun ta sanar da ranar da za ta yanke hukuncin cikin sanarwar da ta aike wa ɓangarorin da shari'ar ta shafa. Sakataren lauyoyin NNPP, Barrister Bashir T/Wurzici, ya tabbatar wa Jaidar Daily Trust da hakan, yana mai cewa lallai an miƙa wa tawagar lauyoyi takardar…
Read More
Tinubu ya naɗa Nkwocha, Kakanda da wasu a muƙamai a Fadar Shugaban Ƙasa

Tinubu ya naɗa Nkwocha, Kakanda da wasu a muƙamai a Fadar Shugaban Ƙasa

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya naɗa tsohon Editan Jaridar Leadership, Kingsley Stanley Nkwocha, a matsayin Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Yaɗa Labarai a Fadar Shugaban Ƙasa. An naɗa Nkwocha tare da wasu ne inda za su yi aiki tare a ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa. Kazalika, Tinubu ya naɗs Tope Fasua a matsayin Mai Bada Shawara na Musamman Kan Harkokin Tattalin Arzikin Ƙasa a ofishin Mataimakin na Shugaban Ƙasa. Sauran waɗanda aka naɗa masu bada shawara a ɓangarori daban-daban sun haɗa da Sadiq S Jambo da Dr. Muhammad Bulama da Mahmud Muhammad da kuma Ahmed Ningi. Sanarwar…
Read More
Tinubu ya naɗa Baba-Ahmed mai bai wa mataimakinsa shawara

Tinubu ya naɗa Baba-Ahmed mai bai wa mataimakinsa shawara

Hakeem Baba-Ahmed, a matsayin mai bai wa shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin siyasa a ofishin Mataimakin Shugaban, Kashim Shettima. Baba-Ahmed da kansa ya sanar da naɗin nasa a shafinsa X a ranar Litinin. “Lokaci ne da ya kamata in bayyana wa duniya cewa na amsa kira in yi aiki a matsayin Mai Bada Shawara ns Musamman (kan harkokin siyasa) ga Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettim,” in ji shi Shi ɗin jigo ne a Ƙungiyar Dattawan Arewa (NEF), kuma ɗan uwa ga abokin takarar shugabancin ƙasa na Jam'iyyar Labour a babban zaɓen da ya gabata, wato Datti Baba-Ahmed. Ya…
Read More
Kotu ta tabbatar da nasarar zaɓen Gwamnan Zamfara

Kotu ta tabbatar da nasarar zaɓen Gwamnan Zamfara

Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Jihar Zamfara, ta tabbatar da nasarar da Gwamnan Jihar, Dauda Lawal ya samu a babban zaɓen da ya gabata. Mai magana da yawun Gwamnan, Sulaiman Bala Idris ne ya bayyana haka cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin. Bala Idris ya bayyana hukuncin da kotun ta yanke a matsayin tabbatar da zaɓin al'ummar jihar ta Zamfara. Dauda Lawal ya zama gwamnan Zamfara ne biyo bayan nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan jihar da ya gudana a watan Maris da ya gabata, inda ya ɗaɗa gwamana mai ci na wancan lokaci da ƙasa. “Ba da jimawa…
Read More
Tinubu ya naɗa ministocin matasa

Tinubu ya naɗa ministocin matasa

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da a naɗa Dr. Jamila Bio Ibrahim Ministar Matasa gabanin Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin. A cewar mai magana da yawun Shugaban Ƙasa a ranar Lahadi, Ajuri Ngelale, Tninubu ya kuma amince da naɗin Mista Ayodele Olawande a matsayin Ƙaramin Ministan Matasa kafin Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin nasa nan gaba. “Dr. Jamila likita ce wadda ta yi shugabancin Ƙungiyar Cigaban Mata Matasa (PYWF) ba da daɗewa ba. "Kazalika, ta riƙe muƙamin Hadimar Gwamnan Jihar Kwara kan Muradan Samar da Cigaba Mai Ɗorewa (SDGs). “Shi kuwa Mista Ayodele Olawande, masanin cigaban al'umma…
Read More