Labarai

Shugabancin APC: Kyari ya maye gurbin Adamu

Shugabancin APC: Kyari ya maye gurbin Adamu

Daga BASHIR ISAH Mataimakin Shuagaban Jam'iyyar APC na ƙasa da daga shiyyar Arewa, Abubakar Kyari, ya maye gurbin Sanata Abdullahi Adamu a matsayin sabon shugaban jam'iyyar na ƙasa biyo bayan murabus da Adamu ɗin ya yi. Wannan sauyin da jam'iyyar ta APC ta samu ya yi daidai da tanadin kundin dokokin jam'iyyar, wanda ya nuna cewa idan shugaban jam'iyyar na ƙasa ya yi murabus mataimakinsa ya maye gurbinsa a matsayin riƙon ƙwarya. An ga Kyari ya jagoranci mambobin Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam'iyyar wajen yin taro a sakatariyar jam'iyyar da ke Abuja cikin tsattsauran tsaro a ranar Litinin.…
Read More
Gwamnatin Neja za ta rufe hanyar Minna-Bida ranar Talata

Gwamnatin Neja za ta rufe hanyar Minna-Bida ranar Talata

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Jihar Neja ƙarƙashin jagorancin Gwamna Umaru Bago ta ba da sanarwar za ta rufe babbar hanyar Minna-Bida na sa'o'i shida domin bai wa ma'aikata damar gyara wani sashen hanyar da ya lalalace. Ta ce hakan zai faru ne daga ƙarfe 12 na rana zuwa 6 na yamma na ranar Talata, 18 ga Yuli, 2023. Gwamnatin ta ba da sanarwar ne ta bakin mai bai wa Gwamna shawara kan kafagen sadarwa na zamani, Abdullberqy U Ebbo. Sanar ta ce, "A sani, Gwamnatin Jihar Neja za ta rufe hanyar Minna-Bida ranar Talata, 18 ga Yuli, 2023 na sa'o'i…
Read More
Tinubu ya bai wa Gbajabiamila, Akume sabbin muƙamai

Tinubu ya bai wa Gbajabiamila, Akume sabbin muƙamai

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa wani kwamiti na musamman wanda zai maye gurbin hukumomin gudanarwa da aka sauke a makon jiya a ɗaukacin ma'aikatun Gwamnatin Tarayya kafin a naɗa wasu sabbi. Majiyarmu ta rawaito cewa, Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, wato Hon. Femi Gbajabiamila, shi ne wanda Tinubu yaɗa shugabancin kwamitin. Ta ce aikin kwamitin shi ne zaɓowa da kuma tantance waɗanda za a naɗa hukumomin gudanarwa a ma'aikatun da lamarin ya shafa daidai da tsarin gwamnati. Haka nan, wata majiyar daga Fadar Shugaba Ƙasa ta bayyana cewa, Shugaba Tinubu ya ƙalubalanci kwamitin da ya…
Read More
Gwamnan Kano ya bada tallafin karatu ga nakasassu zuwa ƙasashen ƙetare

Gwamnan Kano ya bada tallafin karatu ga nakasassu zuwa ƙasashen ƙetare

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da tallafin karatu a ƙasashen ƙetare ga nakasassu a jihar. Gwamnati ta ce nakasassu za su ci gajiyar shirin gwamnatin jihar na bayar da tallafin karatu a ƙasashen ƙetare muddin sun mallaki abubuwan da ake buƙata. Kwamishinan ilimi na jihar Alhaji Umar Haruna Doguwa ya bayyana hakan a ranar Alhamis. A cewar Kwamishinan, "Yana daga cikin manufofin gwamnati mai ci na tabbatar da adalci da samun daidaiton samun ilimi ga kowane ɗan jihar, daidai da yarjejeniyar ƙasa da ƙasa." "Tabbas za mu bada tallafin karatu ga waɗanda ke da…
Read More
HortiNigeria ta gudanar da bita ga manoman Kano

HortiNigeria ta gudanar da bita ga manoman Kano

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja A ranar Talatar da ta gaba ta ne ƙungiyar HortiNigeria ta gabatar da taron bita na farko ga manoma a Jihar Kano. HortiNigeria, wata ƙungiya ce da take tallafa wa manoman lambu da dabarun yadda za su inganta nomansu. Ƙungiyar, wacce take samun tallafi daga Ƙasar Netherlands, ta qaddamar da aikin ne ta karkashin cibiyar samar da takin zamani ta kasa (IFDC) tare da wasu abokan hurdar su. A nasa Mohammed Salasi Idris daraktan shirye shirye na Horti Nigeria ya baiyanawa manema labarai cewa wannan shiri ne da gwamnatin netherland ta ɗauki nauyin na…
Read More
‘Yan ta’adda daga Nijar, Mali, Libya suna ƙaƙaba wa manoman Nijeriya haraji – Ɗan Majalisa

‘Yan ta’adda daga Nijar, Mali, Libya suna ƙaƙaba wa manoman Nijeriya haraji – Ɗan Majalisa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazaɓar Tangaza/Gudu a Jihar Sakkwato, Sani Yakubu ya koka da cewa mayaqa masu iƙirarin jihadi daga Nijar, Mali da Libya da kuma ‘yan bindiga da ke kai hare-hare a Ƙaramar Hukumar Tangaza ta jihar sun sanya haraji kan manoma a yankin. Yakubu, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake gabatar da ƙudiri a zauren majalisar a ran around Talata, ya ce mazavar Tangaza/Gudu ta yi wa dazuzzuka biyu ƙawanya; Dajin Tsauna wanda ya ratsa har zuwa Gwadabawa, Illela da Jamhuriyar Nijar da dajin Kuyan Bana wanda kuma ya…
Read More
Wani sashe na kotu ya rufto wa Alƙalin-alƙalan Jihar Ekiti

Wani sashe na kotu ya rufto wa Alƙalin-alƙalan Jihar Ekiti

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Alƙalin-alƙalan Jihar Ekiti, Mai shari’a Oyewole Adeyeye, ya tsallake rijiya da baya a ranar Larabar da ta gabata, lokacin da wani sashe na babbar kotun jihar ya rufta masa a lokacin da yake ofishinsa. A yanzu dai mai shari’a Adeyeye yana samun kulawar likitoci a wani asibiti da ba a bayyana ba a jihar. Jaridar Manhaja ta tattaro cewa lamarin ya faru ne a lokacin da yake bakin aiki ranar Laraba. Alƙalin dai yana ofishinsa ne a lokacin rugujewar. Wataqila lamarin ba zai rasa nasaba da giɓin tsarin da mamakon ruwan sama ya tsananta…
Read More
Discos na shirin ƙarin farashin wutar lantarki

Discos na shirin ƙarin farashin wutar lantarki

Daga BASHIR ISAH Alamu masu ƙarfi na nuni da cewar akwai yiwuwar 'yan Nijeriya su fuskanci ƙarin kuɗin wutar lantarki nan ba da daɗewa ba. Hakan zai faru ne biyo bayan buƙatar da gamayyar kamfanonin rarraba wutar lantarki (DisCos) mai ƙunshe da kamfanoni 11 ta nuna kan ƙarin farashin lantarkin. Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ce ta bayyana haka a ranar Juma'a, 14 ga Yulin 2023. A cewar NERC, Gwamnatin Tarayya ta ce buƙatar sake duba farashin ta taso ne kan buƙatar haɗa sauye-sauye a ma’aunin tattalin arziki da sauran abubuwan da suka shafi ingancin sabis, ayyuka…
Read More
Tinubu ya ƙaddamar da shirin biyan Naira 8,000 ga magidanta miliyan 12

Tinubu ya ƙaddamar da shirin biyan Naira 8,000 ga magidanta miliyan 12

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fitar da wani shiri na biyan Naira 8,000 na tsawon watanni shida ga iyalai miliyan 12 domin magance wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi. An bayyana hakan ne a cikin wata takarda da Kakakin Majalisar Wakilan Nijeriya, Tajudeen Abbas ya karanta a Zauren Majalisar a ranar Talata, 11 ga Yuli, 2023. Tinubu ya ce wannan tallafi ne domin baiwa talakawa da marasa galihu ‘yan Nijeriya damar shawo kan tsadar biyan buƙatu. Wasiƙar ta kasance ne don amincewa da ƙarin kuɗi…
Read More
Sojoji sun fatattaki ’yan bindiga a Filato

Sojoji sun fatattaki ’yan bindiga a Filato

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar Sojojin Nijeriya ta bayyana cewa, dakarunta da aka aika garin Mangu ta Jihar Filato don magance rikicin da ke faruwa sun kashe wasu ’yan bindiga da dama. Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar sojin ƙasa, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya wallafa a shafin rundunar na intanet ta ce, lamarin ya faru ne a Ƙaramar Hukumar Mangu mai fama da rikicin ƙabilanci ranar Laraba. Hakan na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan hukumomin jihar sun sanya dokar hana fita ta awa ashirin da hudu a Mangu bayan ɓarkewar rikici da ya yi sanadin mutuwar mutane…
Read More