Labarai

Muna fatan sabon Gwamnan Katsina ya tabbatar da Hukumar Hisba a jihar – Rabiu Garba.

Muna fatan sabon Gwamnan Katsina ya tabbatar da Hukumar Hisba a jihar – Rabiu Garba.

Daga RABI'U SANUSI a Kano An yi kira ga zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar Katsina, Dr Dikko Raɗɗa, da ya taimaka wajen tabbatar da Hukumar Hisbah ta ƙasa reshen jihar dan aikin cigaban jihar da ma ƙasa baki ɗaya. Wannan kira ya fito ne daga bakin sabon Shugaban Hukumar Hisbah ta jihar Katsina, Alh. Muhammad Rabiu Garba (Aminchi), jim kaɗan bayan tabbatar da shi matsayin sabon Kwamandan Hukumar na jihar. Muhammad Rabiu Garba ya ce sahalewar Hukumar ta Hisbah a jihar zai taimaka wajen daƙile matsalolin yau da kullum da ke ƙara samun gindin za ma a wasu ɓangarorin jihar. Don haka…
Read More
‘Yan sanda sun cika hannu da waɗanda suka ɓarnata gidan Rara a Kano

‘Yan sanda sun cika hannu da waɗanda suka ɓarnata gidan Rara a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Rundunar 'Yan Sandan ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Usaini Mohammed Gumel, ta yi nasarar cafke wasu mutane kimanin su 21 da ake zargi da hannu wajen ɓarnatawa da sace kayan shahararren mawaƙin nan, Dauda Adamu Kahutu da akafi sa ni da Rarara da ɓata wani ɓangare na sakatariyar yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC da ke hotoro cikin birnin Kano. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Kakakin rundunar, SP Haruna Abdullahi Kiyawa, ya fitar ga manema labarai. Sanarwar ta ce, a ranar 20-03-2023 da misalin ƙarfe 2 na rana rundunar ta samu sanarwar…
Read More
Buni ya taya al’ummar musulmi murnar fara azumin Ramadan

Buni ya taya al’ummar musulmi murnar fara azumin Ramadan

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN, Damaturu Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya taya al'ummar musulmin jihar da na duniya baki ɗaya, murnar fara azumin watan Ramadan. A sanarwar manema labarai mai ɗauke da sa-hannun mai magana da yawun Gwamnan, Alhaji Mamman Mohammed, ya ce Buni ya yi wa al'ummar musulmi kyakkyawan fatan samun dacewa a wannan wata mai alfarma wanda babbar dama ce ga musulmi saboda ɗimbin albarkar da watan ya ƙunsa. "Ina taya mu murna baki ɗaya sakamakon ɗimbin alfanu da rahamar Allah Maɗaukakin Sarki dake cikin wannan wata mai girma, ina roƙon Allah ya ba mu lafiya da himma…
Read More
Safarar sassan jiki: Kotun Birtaniya ta samu Ekweremadu da aikata laifin da ake tuhumarsu.

Safarar sassan jiki: Kotun Birtaniya ta samu Ekweremadu da aikata laifin da ake tuhumarsu.

Daga WAKILINMU Kotun Birtaniya ta samu tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Ike Ekweremadu da matarsa, Beatrice, da aikata laifin safarar sassan jikin mutum. Haka nan, laifin ya shafi har da wata 'yarsu mai suna Sonia da kuma wani likita, Dr. Obinna Obeta, saboda taimakawa da suka yi wajen shirya kai matashin da lamarin ya shafa Birtaniya. An same su da laifin haɗin baki wajen ɗaukar matashin zuwa London don cire ƙodarsa. An rawaito cewar nan ba da daɗewa ba kotun da ke sauraren ƙarar za ta yanke hukunci kan shari'ar. Idan za a iya tunawa, a watan Yunin 2022…
Read More
Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Tinubu ya tafi hutu ƙetare

Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Tinubu ya tafi hutu ƙetare

Daga BASHIR ISAH Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasar Nijeriya mai jiran gado, Bola Tinubu, ya tafi hutu Paris a ƙasar Fransa inda daga nan zai tafi Saudiyya domin aikin Umarah. Bayanin haka ya fito ne ta bakin mai magana da yawun Tinubu, Tunde Rahman, cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Laraba. “Bayan kammala harkokin kamfe da zaɓe, zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Asíwájú Bola Tinubu, ya keta hazo domin hutawa da kuma tsara yadda shirin karɓar mulki zai kasance a ranar 29 ga Mayun 2023,” in ji Rahman. A cewarsa, Tinubu ya bar Babban Filin Jirgin Saman Murtala Mohammed da ke Ikeja zuwa…
Read More
‘Yan sanda a Kano sun cafke waɗanda ake zargi da ƙona gidan Rarara

‘Yan sanda a Kano sun cafke waɗanda ake zargi da ƙona gidan Rarara

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Rundunar 'yan sanda ta jihar Kano ta tabbatar da kama wasu ɓata-gari da ake zargi da cinna wuta a gidan shaharrren mawaƙi, Dauda Kahutu Rarara. Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar a Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya tabbatar da hakan cikin wata sanarwa da ya fitar. Kiyawa ya ce sun cafke mutanen ne bisa zargin ƙone wani ɓangare na gidan mawaƙin Jamiyyar APC, biyo bayan samun Nasarar Abba Kabir Yusif na Jamiyyar NNPP a zaɓen Gwamnan Jihar Kano. Ya ce za su gurfanar da dukkan waɗanda aka samu da hannu cikin lamarin da…
Read More
JAMB ta dawo da rajistar DE, ta kuma kafa sabbin ƙa’idoji

JAMB ta dawo da rajistar DE, ta kuma kafa sabbin ƙa’idoji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire ta JAMB, ta gindaya wasu sabbin ƙa’idoji don daƙile jabun takardun shaidar 'A Level' yayin da ta kuma dawo da rajistar DE 2023. Sakataren hukumar, Farfesa Ishaq Oloyede, wanda ya bayyana haka a wani taron manema labarai a ranar Litinin a Abuja, ya ce za a rufe rajistar DE ranar 28 ga watan Afrilu. Yayin da yake kokawa kan yadda ake amfani da takardar shaidar matakin 'A' na jabun takardu wajen yin rajistar, Mista Oloyede ya ce hukumar ta ɓullo da sabbin tsare-tsare don tantance irin…
Read More
Tukur Mamu ya ƙi amsa tuhuma

Tukur Mamu ya ƙi amsa tuhuma

Daga SANI AHMAD GIWA Tsohon mai shiga tsakani wajen tattaunawa da 'yan ta'adda, Tukur Mamu, ya ƙi amsa tuhumar laifuka 10 da Gwamnatin Tarayya ke zarginsa da aikatawa. A ranar Laraba ofishin Babban Lauyan Nijeriya ya gurfanar da Mamu a gaban Mai Shari'a Inyang Ekwo na Babban Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin taimaka wa 'yan ta'adda. Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayar da rahoton cewa, Mai Shari’a Nkeonye Maha na wata kotun tarayya a ranar 13 ga watan Satumba, 2022, ta bai wa hukumar tsaro ta farin kaya, SSS, izinin tsare tsohon ɗan mai sasanci tsakanin 'yan ta'addan…
Read More
Gwamnati ta gurfanar da Tukur Mamu

Gwamnati ta gurfanar da Tukur Mamu

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da tsohon mai shiga tsakani wajen tattaunawa da 'yan ta'adda, Tukur Mamu, kan zargin laifuka 10 da suka haɗa da taimaka wa 'yan ta'adda da sauransu. A ranar Laraba Ofishin Babban Lauyan Ƙasa (AGF) ya gurfanar da Mamu a madadin Gwamnatin Tarayya a gaban Mai Shari'a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya a Abuja. Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya rawaito cewar, a ranar 13 ga Satumban 2022 wata kotu ƙarƙarshin jagorancin Alƙali Nkeonye Maha, ta bai wa hukumar tsaro ta DSS damar tsare Mamu na kwana 60 domin ba ta damar kammala…
Read More
Ganduje ya ɗage dokar taƙaita zirga-zirga a Kano

Ganduje ya ɗage dokar taƙaita zirga-zirga a Kano

Daga RABI'U SANUSI a Kano Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Dokta Abdullahi Umar Ganduje, ta sanar da ɗage dokar hana fitowa da ta sa daga ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin da ta gabata. Kwamishina Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Muhammad Garba ne ya sanar da haka a daren Lahadi nan data gabata zuwa safiyar Litinin. Sanarwar ta ce duba da kwanciyar hankali da aka samu a faɗin jihar hakan ya bai wa gwamnati damar ɗage dokar ta awanni 24 da ta kafa don kare dukiya da rayukan al'ummar jihar Kwamishinan ya buƙaci 'yan kasuwar jihar da sauran masu gudanar…
Read More