Labarai

Sojoji sun kashe Ali Dogo da mayaƙansa a Kaduna

Sojoji sun kashe Ali Dogo da mayaƙansa a Kaduna

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rundunar Sojojin Saman Nijeriya (NAF) ta samu nasarar kashe ƙasurgumin ɗan ta'addan nan da ya addabi Jihar Kaduna, Ali Dogo, tare da wasu mutanensa 30. Rahotanni sun nuna cewa, sojojin dakarun ‘Operation WHIRL Punch’ ne suka fattaki Dogo, wanda aka fi sani da Yellow da mayaƙansa a ƙarshen makon da ya gabata. Sojojin sun yi wa Yellow da mayaƙan nasa dirar mikiya ne a daidai lokacin da suke tsaka da tattaunawa a gidan Alhaji Gwarzo, inda jirgin yaƙin ya sakar wa ginin wuta ya hallaka su baki ɗaya. Hakazalika, sojojin sun sake kai samame kan ’yan…
Read More
Da ɗuminsa: Za a tuna da Buhari a matsayin Shugaban Ƙasa mafi inganci, inji Sarkin Lafia

Da ɗuminsa: Za a tuna da Buhari a matsayin Shugaban Ƙasa mafi inganci, inji Sarkin Lafia

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja An bayyana cewa, za a tuba da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a matsayin Shugaban Ƙasa mafi inganci a tarihin Nijeriya. Wannan furuci ta fito ne daga bakin Mai Martaba Sarkin Lafia, Alhaji Sidi Mohammad, wanda kuma shine Shugaban Kwamitin Bada Lambobin Girma na 2022 da aka gudanar a yau. Sarkin ya bayyana hakan a lokacin da ya ke gabatar da jawabin godiya a yayin bikin bayar da lambobin girmamawar, wanda aka gudanar yau a Ɗakin Taro na Ƙasa da ƙasa da ke Abuja. A ta bakinsa, "bisa la'akari da irin fafutuka da gudunmawar da…
Read More
An tono gawarwakin mata a ofishin wani likita

An tono gawarwakin mata a ofishin wani likita

Daga WAKILINMU Jami’an bincike sun gano gawarwakin wasu mata biyu da aka binne a ofishin Babban Daraktan Asibitin Kaiama da ke Jihar Kwara, Dkta Abbas Adeyemi. Daga cikin gawarwakin da aka tono har da ta wata matar mai suna Nofisat Halidu a wani kabari mara zurfi a asibitin a gaban mijinta, kamar yadda ’yan sanda suka tabbatar. Adeyemi, wanda a halin yanzu ya ke tsare, ana zargin shi da laifuka daban-daban na kisan kai. A watan jiya ne rundunar ’yan sandan Jihar Edo ta kama Adeyemi kan kisan wani direban tasi mai suna Emmanuel Yobo Agbovinuere. Dakta Adeyemi wanda ya…
Read More

Bayan sama da wata bakwai: ASUU za ta janye yajin aiki nan ba da daɗewa ba – Osodeke

Daga BASHIR ISAH Ɗaliban jami'o'in gwamnati a faɗin Nijeriya na ci gaba da nuna farin cikinsu bayan da yajin aikin da malamansu suka yi ƙarƙashin ƙungiyarsu ta ASUU ya zo ƙarshe. Kimanin watanni takwas aka shafe ASUU na yajin aiki inda sai a kwanan nan lamarin ya zo ƙarshe bisa umarnin kotu ga ƙungiyar. Bayan tirka-tikar da aka yi tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya, ƙungiyar ta ba da sanarwa a ranar Talata cewa za ta janye yajin aikin nata nan ba da daɗewa ba. A ranar Litinin malaman jami'o'in suka bayyana cewa, suna da yaƙin shiga tsakani da Majalisar Wakilai…
Read More
Ya yi wa ɗiyar abokinsa ’yar shekara 13 fyaɗe

Ya yi wa ɗiyar abokinsa ’yar shekara 13 fyaɗe

Daga WAKILINMU Hukumar Tsaro ta NSCDC ta sanar da kama wani ɗan shekara 20 kan zargin yi wa yarinya mai shekara 13 fyaɗe a Jihar Nasarawa. Kakakin NSCDC reshen jihar, DSC Jerry Victor ya ce, mutumin da ya yi wa yarinyar fyaɗe ya sanya ta samu juna biyu a Lafiya, babban birnin jihar. Haka kuma, NSCDC ta ce, ta kama wasu mutum biyu daban da zargin lalata da wata ’yar shekara 13. Da ya ke gabatar da su a gaban manema labarai, DSC Jerry Victor, ya ce, an kama mutanen ne a wurare daban-daban na jihar. “Waɗanda ake zargi sun…
Read More
Gwamnatin ƙasar Sin ta sauke nauyin dake wuyanta ta hanyar ingiza samun wadata ba tare da barin kowa a baya ba

Gwamnatin ƙasar Sin ta sauke nauyin dake wuyanta ta hanyar ingiza samun wadata ba tare da barin kowa a baya ba

Daga AMINA XU Abin dake shaida wadata da karfin wata kasa shi ne ƙarfinta na kawar da talauci, kuma shaidar ƙarfin wata gwamnati shi ne matakan da ta ɗauka don rage gibin dake tsakanin mawadata da matalauta. Tabbatar da samun wadata ba tare da barin kowa a baya ba, daya ne daga cikin wasu muhimman abubuwa dake cikin tsarin mulki na gurguzu mai halayyar musamman ta ƙasar Sin. Mawadata su taimakawa matalauta wajen fita daga talauci, wata hanya ce mai kyau ta tabbatar da wannan buri. Ni ne na yi sa’a sosai, saboda iyali na ɗaya ne daga cikin iyalan…
Read More
Allah Ya yi wa ɗan Majalisar Katsina, Ibrahim Kurami rasuwa a Saudiyya

Allah Ya yi wa ɗan Majalisar Katsina, Ibrahim Kurami rasuwa a Saudiyya

Daga WAKILINMU Ɗan Majailsar Dokokin Jihar Katsina mai wakiltar mazaɓar Bakori, Hon. Ibrahim Kurami, ya riga mu gidan gaskiya a birnin Madina, Saudi Arebiya. Abokin siyasarsa, Alhaji Nasiru Danguga, ya ce Kurami ya rasu ne da misalin ƙarfe biyu na dare agogon Nijeriya bayan fama da taƙaitaccen rashin lafiya. Bayanai sun ce marigayin ya tafi birnin Madina ne don yin Ummara, tare da cewa a Madina hukumomin ƙasar za su yi masa jana'iza. Marigayin ya rasu ya bar mata biyu, 'ya'ya 11 da kuma jikoki uku. Kurami ya zama ɗan Majlisar Katsina ne bayan nasarar da ya samu a zaɓen…
Read More
Sojojin Nijeriya 68 za su gurfana gaban shari’a saboda take doka

Sojojin Nijeriya 68 za su gurfana gaban shari’a saboda take doka

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Sojin Nijeriya ta bayyana shirin hukunta dakarunta guda 68 saboda samun su da aikata laifuffuka daban-daban, lokacin da runduna ta 8 dake Sakkwato ke gudanar da sintirin kakkaɓe 'yan ta’adda a jihohin Sakkwato da Zamfara da Kebbi da kuma Katsina. Kwamandan Runduna ta 8, Manjo Janar Uwem Bassey dake kuma jagorancin rundunar da ake kira ’Hadarin Daji’ ya bayyana haka lokacin da yake qaddamar da kotun da za ta gudanar da shari’ar. Janar Bassey wanda ya yi suna wajen kutsa kai sansanonin ‘yan ta’adda yana kai musu hari, ya buƙaci alƙalan da za…
Read More
‘Yan sanda sun ceto mata tara da za a yi safararsu zuwa Libiya a Jihar Katsina

‘Yan sanda sun ceto mata tara da za a yi safararsu zuwa Libiya a Jihar Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina 'Yan sanda sun ce sun yi nasarar ceto wasu mata tara da suka fito daga wasu jihohin Nijeriya daban-daban da ake shirin safararsu zuwa ƙasar Libiya, a ranar Laraba. Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, wanda ya bayyana haka, ya ce sakamakon bayanan sirri da suka samu ne jami'ansu suka yi wa wata maɓoya ta masu safarar dirar-mikiya a yankin ƙaramar hukumar Daura inda suka ceto matan. Jaridar Punch ta ruwaito cewa, kakakin ya yi bayani kan matan inda ya ce, ''waɗanda aka ceto su ne Timilaye Ojo mai shekara 26 daga…
Read More